Wasu fussatattun magoya bayan jam’iyyar adawa a jihar Nasarawa sun fara gudanar da zanga-zanga a Lafia babban birnin jihar. Zanga-zangar na zuwa ne bayan hukuncin da kotun koli ta yanke inda ta tabbatar da Abdullahi Sule na Jam’iyyar APC a matsayin halastacen gwamnan Jihar Nasarawa.
Magoya bayan sun rufe titin da ya tashi daga Lafia zuwa Jos, yayin da suke kone-konen tayoyi da kuma nuna rashin jin dadinsu kan hukuncin kotun, kamar yadda jaridar Vanguard ta rawaito.
- Kotun Ƙolin Nijeriya Ta Tabbatar Da Zaɓen Sule A Matsayin Gwamnan Nasarawa
- Hukuncin Zaben Nasarawa: PDP Za Ta Daukaka Kara Zuwa Kotun Koli
To sai dai kuma jami’an tsaro sun yi saurin daukar matakin dakile zanga-zangar, amma duk da haka ma su bababen hawa sun kauracewa titin, haka zalika ma masu shaguna sun rufe shagunansu.
Tun da farko dai Kotun sauraron kararrakin zabe ta sauke Gwamna Sule daga matsayin Gwamnan Jihar Nasarawa, inda Kotun ta ce akwai lam’a a zaben nasa, daga bisani kuma kotun daukaka kara ta ruguje hukuncin kotun farko, inda ta tabbatar masa da matsayinsa na gwamnan Nasarawa.