Connect with us

NAZARI

Rikici Na Neman Kassara APC A Zaben 2023

Published

on

Rikici cikin jam’iyyar APC mai mulkn Najeriya, a  tsakanin manyan ‘yan jam’iyyar da ake kallon babbar barazana ga jam’iyyar da ke fatan ci gaba da mulki a shekara ta 2023. Hasashen kwabewar lamura a cikin jam’iyyar APC, tun lokacin da irin su Inginiya Buba Galadima masu neman sauyin, suka fara ficewa daga jam’iyyar APC. A bayyane take cewa rikicin da ke ruruwa a APC mai mulkin Najeriya ya taso ne a kokawar da wasu ‘yan jam’iyyar suke yi na tabbatar da ikonsu gabanin kakar zaben 2023.

Masana harkokin siyasa suna kallon  APC ba jam’iyya ba ce, illa dai kawai wata gamayyar ‘yan siyasa masu mabambantan ra’ayoyi da suka hadu domin kawar da jam’iyyar PDP daga mulki a 2015. Rikicin baya bayan nan shi ne game da hukuncin wata kotun Abuja wadda ta tabbatar da sauke Mr Adams Oshimhole daga shugabancin jam’iyyar APC.

Mai Shari’a Danlami Senchi na kotun Abuja Shine ya yanke hukuncin, bayan karar da wani dan jam’iyyar APC, Oluwale Afolabi, ya shigar cewa tuni aka dakatar da Mr Oshiomhole daga jam’iyyar APC a jiharsa ta Edo.

Hukunci ya tayar wa Mr Oshiomhole hankali inda ya garzaya fadar shugaban kasa domin nema agaji, amma dai alamu sun nuna wasu gwamnonin APC da kuma wasu manyan ‘yan jam’iyyar suke son ganin an cire Oshiomhole daga kan mukaminsa. Akwai kanshin gaskiya ganin cewa sakatariyar gwamnonin APC ta bakin kakakinta Abdurrahman Barkindo ta fitar da sanarwar da ke goyon bayan hukuncin kotun.

Sai dai a wani mataki da ake gani na samun goyon bayan gwamnan jihar Kano Dokta Abdullahi Ganduje, inda wata kotun tarayya da ke jihar ta Kano ta yi fatali da hukuncin kotun Abuja ta yi, inda ta jaddada cewa Mr Oshiomhole shine halastaccen shugaban APC.

Tinubu da kansa ya ce “ana kassara APC saboda zaben 2023” Amma masu yunkurin kawar da Mr Oshiomhole sun riga sun ja daga. Wani bangare da ke kiran kansa reshen APC da ke kudu maso kudancin Najeriya, wanda fitattun ‘yan siaysar yankin irin su tsohon  gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki da tsohon gwamnan Ribas kuma ministan sufuri Rotimi Amaechi ke cikin sa, ya nada Mr Victor Giadom a matsayin shugaban riko na jam’iyyar.

An dade ana kai ruwa rana tsakanin Mr Obaseki, wanda shi ne mutumin da ya maye gurbin Mr Oshiomhole a matsayin gwamnan Edo da tsohon maigidansa, lamarin da wasu ke gani shi ne silar sabon rikicin da yayi gaba kujerar Mr Oshiomhole.

Sa-toka-sa-katsi da ya-ki-ci-ya-ki-cinyewa ya sa daya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar, Bola Ahmed Tinubu, ya fusata inda a wata wasika da ya rubuta ya yi zargin cewa zazzabin cutar samun mulki a 2023 ne ya kama mutanen da ke yunkurin cire Mr Oshiomhole daga shugabancin APC.

Idan ba a yi hankali ba, rikicin APC zai iya yi mata illa sosai idan ba a shawo kansa ba, amma da wuya a shawo kansa ganin cewa kowa da inda ya sa gaba a jam’iyyar.

Amma jam’iyyar APC, wasu gungu-gungu mutanene da ke da akidu mabanbanta  wadanda a baya ma ba sa zama da juna inuwa guda, amma saboda kokarin kawar da jam’iyyar PDP saboda su karbi mulki a shekarar 2015.

Rikicin APC ya soma ne tun lokacin tsayar da ‘yan takara a zaben 2019 inda wasu ‘yan jam’iyyar suka yi zargin cewa shugabanta Mr Oshiomhole ya yi rashin adalci ga wasu masu neman yi wa jam’iyyar takara na mukaman gwamnoni da ‘yan majalisu.

Ci gaba da shugabancin jam’iyyar na Oshiomhole zai iya durkusar da ita, saboda halayyarsa ta kin jin-bari, ya kuma ki karbar shawara, inda ya ki a rika juya shi kamar yadda wasu ‘yan jam’iyyar suke so. Haka ta sa suke son cire shi daga mulki.

Bangare da ke adawa da Mr Oshimohle ya bukaci a gudanar da taron kwamitin zartarwar jam’iyyar wanda ake gani ana son yin sa ne domin yin amfani da shi wurin cire shugaban jam’iyyar. Ko da yake taron da wasu gwamnonin jam’iyyar suka yi da Shugaba Buhari ranar Litinin, ya dakatar da gudanar da taron kwamitin zartarwar.

Rikicin siyasar da yake ci gaba da ci a APC zai koma na sari-ka-noke ne kawai kuma nan gaba zai sake bullowa. Taron koli na jam’iyyar ta APC da aka gudanar ranar a fadar, bayan da Shugaban Najeriya ya amince da shugabancin bictor Giadom kuma ya umarce shi ya kira taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar ta APC. A lokacin taron, shubaban kasa muhammadu Buhari ya amince da da kafa kwamatin riko da ke karkashin Gwamnan jihar Yobe Mala Buni na tsawon watanni Shidda.

Rikicin jam’iyyar APC, ya fara kamari lokacin da shugabanta ya jagoranci yi wa wasu manyan jam’iyyar, wato mataimakin shugaban jam’iyar a yankin arewa maso yamma Senata Lawal Shu’aibu da kuma mataimakinsa Abdulkadir Inuwa afuwa bayan dakatar da su da aka yi tsawon wata shida, zai iya zama wata hanya ta dinke barakar jam’iyyar.

Gwamnonin jam’iyyar APC sun nemi tsohon shugaban jam’iyyar na kasa, Adams Oshiomole da ya yi murabus. A wata sanarwa da  kungiyar gwamnonin na APC, Salihu Lukman ya sa hannu, ta nemi Oshiomole da ya kira babban taron jam’iyya na kasa da gaggawa ko kuma ya fice daga jam’iyyar. Duk da cewa Shugabannin jam’iyyar na kananan hukumomi 18 a jihar Edo suka kada kuri’ar yanke kauna kan Adams Oshiomole. Rikicin ya samo asali ne tun daga watan Yuni lokacin da ‘yan majalisa tara cikin 24 na majalisar jihar suka zabi kakakin majalisar da sauran shugabanninta.

Rikicin APC ya dauko hanyar rugujewa tun yanzu a rashin sahihin shugaba. Amma shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da ya tsinkayi wata babbar matsalar rikicin cikin gida na neman kassara jam’iyyar, ya rusha shugabancin tare da kafa kwamatin riko na Jam’iyyar. Ga dukkan alamu dai jam’iyyar da ba a taba yin irinta ba a tarihin Najeriya, wato jam’iyyar da ta kada da jam’iyya mai mulki,

Kowa a jam’iyyar sun yadda cewa Tinubu da Buhari sune iyayen a jam’iyyar APC, amma rigimar tana neman tafi karfin su, ganin halin da jam’iyyar ta afka ciki. Yanzu haka, jam’iyyar APC dai tana kan keken makaho ne, sai abinda yayi mata birki.

Abin burgewa a rikicin siyasar  jam’iyyar APC, reshen jihar Edo da ta dakatar da shugaban jam’iyyar na Kasa, Adams Oshiomhole daga jam’iyyar, wadda a tarihin siyasar Najeriya abu ne mai wahala shugabancin Mazaba ko jiha, sun aikata haka.

Haka yaba Kotuna har uku suka jaddada dakatar da  Adams Oshiomhole, wanda ya dare kujerar na kwance a Asibiti ba lafiya, sannan wani can kuma ya kaddamar da kansa, shugaba jam’iyyar.

Rikice-rikicen da APC ke fama da su a jihohin Najeriya, abin da ya faru a jihar Zamfara, ya faru a jihar Edo, duk haka na faruwa saboda ba a ga maciji a tsakanin gwamnan jihar Edo, Obasaike da shugaban jam’iyyar na Kasa Adam Oshiomhole.

Rikicin cikin gida a wasu jihohi na APC ya yi tasiri a zaben 2019. Rikicin APC a jihar Zamfara tsakanin Sanata Marafa da ke wakiltar Zamfara ta tsakiya da bangaren APC  mai mulkin mulki jihar,da rikicin Adamawa sun yi tasiri  a jam’iyyar APC, tsakanin Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha da kuma bangaren tsohon Sakataren gwamnati Babachir Dabid Lawal.

A jihar Filato akwai rikici tsakanin magoya bayan Ministan wasanni da ci gaban matasa Barista Solomon Dalung da kuma bangaren gwamnan jihar Simon Lalong. Rigingimun jam’iyyar da ta ke fama da su a jihohi na iya yi wa jam’iyyar illa sosai a zaben 2023.

Rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar APC a jihar Kaduna,

yayin da aka dakatar da dan majalisar dattijai da ke wakiltar Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani, saboda babu dadi tsakanin sa da gwamnan jihar, Malam Nasiru El Rufai, tare da ficewar wasu jiga-jigan jam’iyyar. Rikicin APC a jihar Bauchi tsakanin tsohon ministan lafiya, Dr Muhammad Pate da takwaransa na ‘yan sanda, Alhaji Yabubu Lame, da kuma tsohon Gwamna da ya sha kaye.

Ire-iran wadannan rikice-rikice da suka addabi jam’iyyar APC a jihohin Najeriya, da kasa da kuma Kananan hukumomin, watakila da mazabun Kansiloli, za su iya jefa     jam’ iyyar APC cikin wani hali, wadda daga karshe ta yi mummunar asara a zaben 2023. A kwanan ‘yan majalisar dokokin jihar kaduna suka baiwa hammata iska a zauren majalisar, da kuma rikice-rikice a majalasun Jihohin Najeriya.

Idan muka dubi yadda rikicin shugabanci da yadda ‘yan Jam’ iyyar APC, suke fuskantar wahala tare da dukan kawo wuka daga shugabaninsu, da yin watsi da su da masu madafun iko suke ko-in-kula da ‘ya’yan jam’ iyyar suke fuskanta, haka zai iya kawo nakasu ga jam’iyyar APC a zaben 2023.

Akwai kararraki da korafe korafi a gaban kotuna wadda jam’iyyar take fuskanta, idan ba a yi hankali ba, zai iya jawowa jam’iyyar cikas a zabe mai zuwa.

Yadda a cikin Jam’iyyar APC, akwai ‘yan Bora da ‘yan Mowa, watau wadanda ke da uwa a gidin Murhu sune kullum ake fifitawa, zahiri hakan ba zai haifarwa da jam’ iyyar Alkhairi. Duk lokacin da aka fita fagen yaki, watau lokacin kokawar kafa mulki, da an yi nasara, sai kaga shugabanni masu mulki sun fita lalubo wadanda ko fagdn yakin basu sani ba, amma sai a dorasu akan mayakan kuma addensu ko dai su gudu ko kuma su tsaya a  yi ta azabtar da su.

Akwai bukatar jam’iyyar APC ta sake shiri yadda ‘yan jam’ iyyar za su ji ana yi dasu, saboda zaben 2023.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: