Rikicikin ya turnuke jam’iyyar SDP a yayin da aka samu shugabanni bangare biyu a Jihar Kogi, rikicin ya kunno kai ne bayan da wani bangare ya kaddamar da kwamitin gudanarwa a Lakwaja.
Taron da aka gudanar a sakateriyar jam’iyyar na jihar, an zabi tsohon shugaban sashi na APC, Hon. Ahmed Attah a matsayin sabon shubagaba, tare da Alhaji Idris Sofada a matsayin sabon sakatare na jam’iyyar a jihar.
Wakilai 3,890 ne daga kananan hukumomi 21 na jihar suka zabi shugabanni 21 na jam’iyyar. Sannan kuma jami’an hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) sun kasance a wannan wuri lokacin zaben.
A jawabinsa na farko, Attag ya yi alkawarin zai yi gaskiya da adalci tare da daga martabar jam’iyyar SDP don samun nasara a zabe a gaba.
- Kotu Ta Dakatar Da INEC Karɓar Buƙatar Yin Kiranye Ga Senata Natasha
- INEC Ta Karɓi Takardun Yi Wa Sanata Natasha Akpoti Kiranye
Ya yaba wa jami’an INEC da kwamitin shirya zaben da kuma jami’an tsaro wurin tabbatar da nasarar wannan taron. Ya ce wannan ya nuna yadda SDP za ta yi nasara a zaben gwamna a 2028.
Sai dai kuma wani bangare da Moses Peter Oricha yake jagoranta ya yi watsi da zaben, inda ya bayyana shi a matsayin wanda bai inganta ba.
Oricha, wanda shugabancinsa zai kare a watan Afrilun 2026, ya zargi masu shirya zaben da karya doka da kuma kin bin hukuncin kotu kan wannan lamari.
“An sanar da ni cewa wasu mutane da suke kiran kansu ‘ya’yan SDP ne sun shirya babban taron jam’iyyar a jihar. Wannan abun dariya ne kuma babban laifi ne. Wadannan mutane ana daukar nauyinsu ne domin su kawo rudani a cikin jam’iyyarmu,” in ji Oricha.
Ya bukaci mutane da hukumomin tsaro da INEC su yi watsi da taron, sannan kuma ya dauke shi a matsayin wani kokari na tarwatsa jam’iyyar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp