Rikicin Binuwai:  Wai ’Yan ISIS A Nijeriya?

El-Zaharadeen Umar, Katsina 08062212010

Shekara da shekaru mutanen Nijeriya suna da shakku game da wasu batutuwa ko bayanai da hukumomi tsaro ko gwamnati kan bada idan wata matsala ta faru, koda kuwa bayanai suna da kamshin gaskiya kasancewar yadda hukumomin suka koma macuta  a maimakon maceta.

Sannan sun kasa game cewa duniya yanzu ci gaba take, amma abin mamaki hukumomin tsaron Nijeriya suna kallon ‘yan Nijeriya a matsayin da suka ajiye su na duhun kai da bakin jahilci saboda haka duk maganar da suka ga dama sai su fada ba tare da duba abin da zai je dawo ba.

Jami’an tsaron Nijeriya mutane kamar sauran jama’a suna da basira da ilimi kamar saura, suna da tunani da wayo da dibara kamar sauran jama’a amma me yasa suke mantawa da haka sai kawai su kalli ‘yan Nijeriya su fada masu abin da suka ga dama, kuma su tsaya kai da fata cewa wannan batu haka yake.

Wasa da hankalin ‘yan Nijeriya da hukumomin tsaro ke yi kullin yana kara rage kima da mutuncin aikin tsaro da masu tafiyar da sha’anin tsaro tare da zubarwa kasa mutunci a idon duniya

Kazalika wannan ba dibara ca, ba kuma hikima ma ce, ba mafita ba ce, kuma yana taimakawa wajan samun rashin jituwa tsakanin  jami’an tsaro da ‘yan kasa mai makon su rika taimaka masu da bayanai, sai su kyaleku da wayo ko dibararku ta rainin hankali.

A sha’anin tsoro akwai abubuwa da daman gaske da ake boyewa ‘yan kasa saboda wasu dalilai, to amma a Nijeriya abubuwan da ‘yan kasa suka sani na yau da kullin da su ake amfani wajan raina masu hankali da sunan tsoro.

Wannan shimfida ce akan maganar da zan yi da ta shafi rikicin Bunue wanda kullin yake daukar sabon salo a siyasance ko a hukumance, da kuma yadda ake amfani da wannan damar wajan jingina lamari ga wasu bangarori da dama.

Rikicin tsakanin makiyaya da Fulani wani daddadan al’amari ne da yake da tarihin gaske a Nijeriya, hukumomi sun san da haka kamar yadda wasu gwamnatocin suka so dakatar da abun amma suka yi shiru da batun saboda wani dalilin da har yanzu bai bayyana ba.

Akwai tabbacin cewa wasu na amfani da duk wata dama ta rikici domin su cika karansu ba babbaka, ta hanyar yin amfani da rikici su samu kudadai na fitar hankali da sunan kwantar da tarzoma.

Haka suna hukumomin tsoro suna da cikakken rahoton duk wata matsala ko rikici da yake da tarihi a wannan kasa sai dai har yanzu an kasa gane dalilin da yasa aka ki daukar mataki da ya dace domin kaucewa daukar rayukan jama’ar da ba su da laifin komi.

Babu shakka Idan hukumomin tsoro sun ga dama suna da muhimmiyar rawar da za su taka akawo karshen abun cikin ruwa sanyi, wani abu da ke daure kai, shi ne kullin abun ci gaba yake kamar wutar da ji.

A lokacin mulkin shugaba Muhammadu Buhari an samu asarar rayuka da daman gaske ta hanyar kara zafafar rikice-rikice a wurare daban-daban musamman arewacin Nijeriya amma har yanzu gwamnati ta sanyawa idanunta tuka tana kallon abin yana tafiya har inda ya zo haka.

Bayanai daga masana sun bayyana cewa hatta rigimar Boko Haram da yaki ci yaki cinyewa wasu daga cikin jami’an tsaro suna da hannu dumu-dumu aciki, ma’ana dai suna amfana, shi yasa ba sa son wannan fada ya kare da wuri.

Haka kuma masana suna ganin wannna ba karamin kuskure bane a sa ido kullin rayuka na salwalta ba tare da daukar mataki na karshe akan duk wanda aka kama yana tada kayar baya ba.

Al’umma suna sane da irin rikice-rikicen da suka faru musamman a shekarar 2017 a jahohin Barno da Taraba da Ribas da kuma wanda yanzu ake magana akai wato na jihar Binuwai, kafafen yada labarai na cikin gida da na waje sun bada labarin yadda wannan matsala ta ci rayukan jama’a.

To amma abin mamaki shi ne, me yasa na Binuwai ya fi daukar hankali tare da daukar sabon salo daga rikicin jahar, ya koma na kasa baki daya, yanzu ido ya koma akan matsalar rikicin jahar Binuwai, kowa yana fadin albarkacin bakinsa wasu kuma na ganin ana wasa da wuta ne domin cimma wata boyayyar manufa ta siyasa.

Jami’an tsaro musamman na DSS sun kwarai wajen bada bayanan sirri da za su taimakawa gwamnati wajan maganin wata matsala idan ta ta so, saboda su ne babbar madogara ga gwamnatin tarayya domin samun bayyanan sirri a yi maganin matsalar da ka iya ta so wa.

Masana sun yi tunanin cewa DSS za su taimakawa da gwamnati da bayanan sirri da ka iya kawo karshen duk wata barazaran tsaro musamman abin da ya shafi fadace-fadace, amma sai gashi suna jin wasu maganganu da ke kawo shakku game da matakan da gwamnati ta ce ta dauka akan matsalar tsaro.

Rahotan da hukumar DSS suka bayar na cewa mutanen da suka kai hari suka yi kisan kare dangi a jihar Bunue wai ‘ya ISIS ne, wannan magana abin kunya ce ga Nijeriya da mutanen Nijeriya.

Ita dai wannan kungiyar ta ISIS ta yi kaurin suna wajen kai hare-haren ta’adanci akan wasu ba’arin mutane da ba ji ba su gani ba, sannan sukan bayyana dalilin kai ire-iren wannan hari na wuce gona da iri.

Wannan rahoto ya firgita masana ainu, ganin cewa ina ma’aikatan DSS suke har wadannan mutane suka samu wata kafa ta shigowa wannan kasa da ake da ma’aikatan tsaro kala daban-daban, wannan ya zama abin kunya inji wani masanin harkokin tsaro.

Kazalika gwamnatin tarayya a ta bakin mai taimakawa shugaban kasa a harkar yada labarai Malam Garba Shehu ya bayyanawa manema labarai cewa wadannan mutanen da ake zargin ‘yan ISIS ne suna magana da yaren farasanci wai kuma suna baiwa jami’in tsaro hadin kai domin samun wasu bayanan sirri da za a mangance wannan matsala.

Sai dai kuma ya ki ya yi karin haske akan cewa ko za a gabatar da su a gaban kuliya ko ko, abin zai kasance yadda aka saba, ana can ana binciken magana ta shirirce  acikin ofis din wani babba, sai daga baya a ji wani bayani na daban, ko kuma abin nan Malam bahuashe ke cewa sai wani jikon kare da ya zubar da tsamiyar kura?

Alamu na nuna cewa an yi amfani da Garba Shehu ne kawai ya fadawa ‘yan Nijeriya maganar da zata kara tuzura su da kara fusata su akan abin da babu shi, amma saboda su ne gwamnati sai abin da suke so za su fadawa jama’a gashi ya yi wasa da hankalin jama’a kamar  yadda jami’an tsaro suka saba.

Da aka tambayeshi wannan ya nuna cewa akwai sakaci game da harkar tsaro a Nijeriya? Sai ya ce duk wanda ya fadi haka wai bai san girman Nijeriya ba, yana da nufin abin ya fi karfin jami’an tsaro saboda haka kowa ya yi ta kansa.

Tun akwanakin bayan hukumar tsaro ta DSS ta so shigowa da ‘yan ISIS  a Nijeriya inda ta ce ta samu bayanan sirri game da wani jigon kungiyar da ya zo Nijeriya daga kasar Dubai, amma ta ce ta yi nasarar damke shi, sai dai har yanzu shiru kamar an aiki bawa garinsu.

Maganar zuwan ‘yan ISIS a Nijeriya kuma a rikicin jihar Binuwai akwai lauje cikin nada, wannan ya nuna cewa hatta kisan kare dangi da aka yi a wasu jahohi da suka hada Barno da Jos da Yobe da Taraba duk ‘yan ISIS ne? idan kuwa ba su bane to su wanene su kuma? Ya kamata su DSS su fito su yi wa kasa bayani indai ba akwai wata a kasa ba.

Tunda yanzu akwai ‘yan ISIS a Nijeriya sauran kungiyoyin ta’addanci ma akwai su ke nan a Nijeriya musamman wadanda suka yi kaurin suna wajan kai hare-haren wuce gona da iri akan jama’ar da ba su  ba su gani ba.

Sannan duk duniya ta san wannan kungiya ta ISIS da ire-iren ayyukan ta’addancinta suna da manufa a bayyanai suna fada idan  za su kai hari, suna fadin dalilin da yasa suka kai hari, amma me yasa a Nijeriya duk babu wadannan bayanai sai dai kawai a ji a bakin da aka ce wai baya karya?

Ya kamata hukumar DSS ta yi karatun ta nutsu wajan sake tunani na yadda za ta taimakawa gwamnatin Nijeriya ta kawo karshen wannan babbar matsala ta fadace-fadece da suka da alaka da addini da kuma kabilanci amma ba wai a rika kawo abubuwan da babu su ba saboda wata manufa da ba a santa ba.

Exit mobile version