Shugaba Muhammadu Buhari, ya yi roko ga al’ummomin da suke kewaye da Jami’ar gwamnatin tarayya ta Kimiyya da Fasaha da ke Owerri (FUTO), da su bayar da cikakken hadin kai tare da shugabannin Jami’ar, yana mai cewa rikicin filaye da ya ki ci ya ki cinyewa a tsakanin Jami’ar da al’ummun da suke kewaye da ita sam ba zai haifar da da mai ido ba ga bunkasar Jami’ar.
Buhari ya yi wannan jawabin ne a bukin saukan karatu na 32 da Jami’ar ta yi, ya nemi al’ummun da su dauki kasantuwar Jami’ar a tsakanin su a matsayin wata albarka a kusancin na su da hukumomin Jami’ar domin su taimaka wa fadada da ci gaban ta.
Shugaban kasan wanda karamin Minista a ma’aiakatar Ilimi, Emeka Nwajuba, ya wakilce shi cewa ya yi, ba wai gazawa ce a bangaren gwamnatin tarayya a kan matakin da ta dauka na kin karbe filayen da karfin tsiya, saboda ta hanyar kalal ne gwamnatin ta mallaki filayen, amma a maimakon hakan sai ta zabi hanyar sasantawa da lalama a matsayin hanyar warware rikicin.
Shugaban kasan ya ce, gwamnatin tarayya a karkashin hukumar kula da zaizayar kasa ta amince da farfado da duk wuraren da zaizayar kasar ta lalata a gefen kogin Otamiri da sassan gadar jami’ar, ya kara da cewa gidauniyar kula da ilimin manyan makarantu (TETFUND), ta bayar da aikin ginawa da kuma bincike a sassan.
Ya kuma bukaci hukumomin Jami’ar da su tabbatar da suna kulawa da yanda ayyukan suke tafiya, ya karfafa cewa, gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da zaman lafiya da kuma ci gaban karatu ta hanyar kungiyoyi da sauran masu ruwa da tsaki ta yanda za a sami ingantaccen Ilimi.
Gwamnan Jihar ta Imo, Emeka Ihedioha, ya yaba wa Shugaban kasa Buhari, a kan irin goyon bayan da yake baiwa Jami’ar, sannan ya kwatanta Jami’ar a matsayin babbar cibiyar ilimin da suke tinkaho da ita.