Gwamnatin Jihar Filato ta jagoranci wani gagarumin taro a birnin Jos domin yafe wa juna da kuma sasanta al’ummar jihar da rikicin kabilanci da Addini ya raba kawunansu.
Wannan biki ya gudana ne a karkashin jagorancin gwamnan jihar, Simon Bako Lalong wanda ya samu halartar Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar II da Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero da shugaban mabiya darikar Katolika na Nijeriya, Arch Bishop John Onayekan da ya samu wakilcin Arch Bishop Ignatius Kaigama.
- Sin Ta Bukaci Amurka Da Ta Kai Zuciya Nesa Game Da Batun Kumbon Farar Hula Da Ta Harbo
- Zan Tabbatar Da An Ci Gajiyar Man Fetur A Yankin Bauchi Da Gombe Muddin Aka Zabe Ni – Atiku
Yayin gudanar da jawabinsa, gwamna Lalong wanda ya bayyana farin cikinsa da yadda jama’a suka amsa kiran da ya musu, ya ce sun yi nasarar kafa ginshikin zaman lafiya da adalci da mutunta juna da kuma karbar baki.
Lalong, ya ce da taimakon sarakunan gargajiya da limaman Addinai da shugabannin al’umma, gwamnatinsa ta yi aiki tukuru wajen sake fasalin jihar da kuma hada kan jama’a.
Gwamnan, ya ce kokarin da suka yi, ya taimaka wajen kawar da tsoro da rashin amincewa juna da kuma kyamar da ake samu a tsakanin jama’ar jihar da suka fito daga kabilu daban-daban
Lalong ya bukaci jama’ar Jihar Filato da su rungumi shirin yafe wa juna da kuma hadin kai, yayin da shi ma ya nemi gafarar jama’ar da suke zaton ya saba musu.
Yayin jawabinsa, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Saad Abubakar, ya jinjina wa gwamnatin Jihar Filato saboda jajircewar da ta yi wajen ganin ta tabbatar da dorewar zaman lafiya, musamman ganin yadda zaman lafiya da walwala ke dawowa a tsakanin al’umma.
Sarkin Musulmin ya ce babu dalilin da zai sa bayan an kwashe shekaru aru-aru ana zaman lafiya a Jihar, a ce kuma yanzu wasu ‘yan tsiraru za su hana zaman lafiya, yayin da ya gargadi jama’a da su daina barin bata gari suna tunzira su domin tashin hankali ba.
A nashi jawabin, Arch Bishop Ignatius Kaigama, shugaban mabiya darikar Katolika ya bayyana farin cikinsa cewar kokarin da suka yi a Filato na tabbatar da zaman lafiya ya kankama, sakamakon rawar da gwamnatin jihar ta taka.
Shugaban sarakunan Jihar Filato, Gbong Gwom Jos, Jacob Gyang Buba, ya bayyana taron a matsayin mai dimbin tarihi, saboda yadda ya tabbatar da aniyar Gwamna Lalong na janyo hankalin jama’ar jihar domin watsi da matsalolin da aka samu a baya dan rungumar zaman lafiya.
Cikin wadanda suka halarci bikin har da tsofaffin gwamnonin Jihar, Janar Lawrence Onoja mai ritaya da Sir Fidelis Tapgun.