Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya gargadi ‘ya’yan jam’iyyar PDP da su daina maganar tsayawa takarar shugaban kasa a 2027, su mayar da hankali kan rikicin shugabanci da jam’iyyar ke fama da shi a halin yanzu.
Da yake jawabi a taron ‘ya’yan jam’iyyar PDP a Abuja, Saraki ya ce PDP ta yi nisa don haka bai kamata a yi sadaukarwa don biyan bukatun kowane mutum ba.
- An Kafa Kawancen Hadin Gwiwar Taron Masanan “Global South”
- Mizanin Hajoji Da Hidimomi Da Masana’antun Kasar Sin Ke Samarwa Ya Karu Da Kaso 5.3 Bisa Dari A Watan Oktoba
Gargadin Saraki na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta cece-kuce a cikin babbar jam’iyyar adawa, wanda ya samo asali ne tun lokacin da jam’iyyar ta fadi zaben shugaban kasa a shekarar 2023.
Jiga-jigan jam’iyyar irin su Nyesom Wike, Gwamna Seyi Makinde, da wasu tsoffin gwamnoni sun juya wa dan takarar shugaban kasa na PDP baya a 2023.
Tun bayan zaben shugaban kasa da ya gabata, jam’iyyar PDP ta ci gaba da fuskantar rikicin shugabanci.
Sai dai Saraki ya ce, “An gina jam’iyyar ne bisa dabaru, falsafa da kuma manufofi. Mu kauce wa gina dabarun wani na kashin kai. Ba za mu iya samun cimma buri ba idan muka sauka daga tsarin jam’iyya. Ba za mu iya samun jam’iyya ba idan ba mu da wani dubaru, domin a nan ne farko.
“Mu daina maganar wane ne zai tsaya takarar kansila, ko gwamna, ko shugaban kasa a 2027. Mu maida hankali kan abin da PDP ke wakilta. Mene ne batutuwa da manufofin da ya kamata mu magance? Wannan shi ne abin da ‘yan Nijeriya ke son sani.
“Sakon da muke aika wa ‘yan Nijeriya shi ne, cewa wannan jam’iyya ce da gaske. Mu shugabanni ne. A bar PDP ta yi jagoranci a haka,” in ji Saraki.