Shugaban kasa Bola Tinubu, ya shiga tsakani a rikicin siyasa da ya kunno kai a jihar Ribas.
Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ne, ya sanar da shiga tsakanin da Tinubu ya yi a ranar Talata a ganawar da ya yi da manema labarai na fadar shugaban kasa jim kadan bayan kammala taron majalisar kasa da ta gudana a fadar ta shugaban kasa da ke Abuja.
- Hukumar ‘Yansanda Ta Tabbatar Egbetokun A Matsayin Sufeto-Janar Na ‘Yansanda
- An Kashe Basaraken Taraba, An Sace Matarsa, Dansa Da Wasu 8
Ruwa dai ya yi tsami ne a tsakanin gwamanan na jihar Ribas Siminalayi Fabura wanda ya gaji Nyesom Wike, wanda a yanzu ke rike da mukamin ministan babban birnin tarayyar Abuja, saboda yunkurin da ‘yan majalisar dokokin jihar ta Ribas suka yi na tsige Fabura a matsayin gwamanan jihar.
Mohammed, wanda a yanzu ke shugabantar kungiyar gwamnonin PDP ta kasa ya ce, daukacin gwamnonin na PDP sun amince za su bai wa shugaba Tinubu hadin ka akan maganar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp