Gwamnatin tarayya ta sake nanata kudirinta na cewa daliban Nijeriya da ke kasar Sudan su kasance a masaukansu yayin da gwamnatin ke ci gaba da shirye-shiryen kwasosu daga kasar da ke fama da rikici.
Wata sanarwa da ofishin jakadancin Nijeriya da ke birnin Khartoum, mai dauke da sa hannun H.Y Garko a ranar Lahadi ta fitar, ta shawarci daliban da su yi watsi da sanarwar da kungiyar dalibai ta kasa (NANS) ta kasar Sudan ta sanar, inda ta yi kira ga daliban da su hadu a Jami’ar Kasa da Kasa ta Afirka, a ofishin NANSS da kuma Jami’ar El-Razi, don kwashe su sannan kuma su riko dala 100 ko 200.
“Kamar yadda ofishin jakadanci ya sanar da dalibai tun da farko, sabida haka ana rokon ku da ku kwantar da hankalinku kuma ku kasance a masaukanku yayin da ofishin jakadancin ke cigaba da shirye-shirye don fara jigila,” inji Garko.
Ta kara da cewa “Ofishin Jakadancin yana so ya tabbatar wa daliban Nijeriya cewa lafiyarsu itace abu mafi girma akan ofishin” in ji ta.
Kimanin ‘yan Nijeriya 4000 ne suka makale a sakamakon fadan da ake yi tsakanin dakarun da ke biyayya ga babban hafsan sojin Sudan, Abdel Fattah al-Burhan, da mataimakinsa, Mohamed Hamdan Daglo, wanda ke jagorantar runduna ta Rapid Support Forces (RSF).
Yazuwa yanzun, an kashe daruruwan mutane sakamakon barkewar rikicin a tsakanin dakarun hafsoshin sojojin biyu a Khartoum, babban birnin Sudan.