Gwamnatin Tarayya ba ta fara kwaso ‘yan Nijeriya da suka makale a Sudan da ke fama da rikici ba a ranar Talata kamar yadda ta yi alkawari.
Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama, a ranar Lahadi, ya ce za a fara kwashe mutanen daga ranar Talata.
Daruruwan mutane ne aka kashe tun bayan rikicin da ya barke kwanaki 10 da suka gabata a babban birnin kasar Sudan tsakanin dakarun janar-janar guda biyu.
Sama da kashi 80 cikin 100 na ‘yan Nijeriya a Sudan dalibai ne, a cewar Onyeama.
A zantawarsa da ya yi da wakilinmu Daily Trust a daren jiya, Shugaban Kungiyar Daliban Nijeriya na Kasa a Sudan, Abubakar Babangida, ya ce ba a fara kwashe ‘yan Nijeriya da suka makale a kasar mai fama da rikici ba.
Yayin da ya ke korafin cewa an samu katsewar kafofin sadarwa a Khartoum babban birnin kasar Sudan, Babangida ya ce bai da tabbacin lokacin da za a kwashe daliban Nijeriya da suke can.
Sai dai ya ce gwamnatin Nijeriya na kokarin ceto daliban.
A halin da ake ciki kuma, a ranar Talata gwamnatin Nijeriya ta fitar da lambobin na atisayen kwashe ‘yan Nijeriya da suke Sudan.
Wata sanarwar hadin gwiwa da Geoffrey Onyeama da Sadiya Faruk, Ministocin Harkokin Kasashen Waje sa Ayyukan Jin Kai, da Kula da Bala’o’i da Ci Gaban Al’umma suka fitar, sun bukaci iyaye da su rika bai wa unguwanninsu shawara domin su kwantar da hankalinsu saboda ana kokarin kwashe dukkan ‘yan Nijeriya da suka makale a Sudan.
Sanarwar mai dauke da sa hannun manyan sakatarori na ma’aikatun biyu, ta kuma shawarci daliban Nijeriya da su ci gaba da tattaunawa da ofishin jakadancin Nijeriya da ke Sudan domin samun karin umarni.
“Za a iya samun jami’an ofishin jakadancin Nijeriya a Sudan ta lambobi kamar haka:
+2348035866773, +249961956284, +2348063636862, +249961956274, da kuma +2349066663493,” a cewar sanawar.
Rikicin dai na kasar Sudan ya barke ne a ranar Asabar din makon da ya gabata a babban birnin kasar Sudan tsakanin dakarun janar-janar guda biyu inda aka kashe daruruwan mutane.
Dubban ‘yan Nijeriya ne a kasar Sudan inda kimanin 5,500 daga cikinsu suka nuna bukatarsu ta a kwashe su zuwa Nijeriya.
Onyeama ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a wani shirin gidan talabijin na Channels, Sunday Politics.
“Muna fatan nan da kwana biyu ko biyu, za mu iya farawa. Da zarar an sami amincewa daga gare mu gwamnatin Sudan za ta fara fitar da mutanenmu.
“Na yi magana jakadanmu a Masar, saboda Misira ita ce kasa mafi kusa da Sudan inda a nan ne za mu samu saukin zuwa taimakawa don aiwatar da wannan aiki,” in ji ministan.
Ya yi watsi da masu ikirari na cewa gwamnatin tarayya ba ta nuna damuwa sosai game da halin da ‘yan Nijeriya ke ciki a kasar mai fama da rikici. “Babu wanda ya yi hasashen rikicin Sudan zai kara ta’azzara,” in ji shi, yana mai tabbatar da cewa tsaron rayukan ‘yan Nijeriya ne mafi girman fifikon gwamnati. Ya bayyana cewa kimanin ‘yan Nijeriya 5,500 ne suka shirya kwaso su daga Sudan, ya kara da cewa kashi 80 cikin 100 na su dalibai ne.
Ya kara da cewa hukumomin gwamnati na kokarin ganin an kai dauki ga wadanda suka makale.
“Ina ta tuntubar ofishin jakadancinmu da ke can dare da rana, sun ba mu kiyasin kudin, sun ba mu cikakkun bayanai, a halin yanzu dai jimmillar mutum 5,500 da aka shirya don kwaso su.
Ya kara da cewa, “Dukkan hukumomin gwamnati suna aiki tare, ciki har da hukumar NEMA, kuma ana tuntubar daliban domin jin bukatunsu kafin a kwashe su da kuma yadda za a kai musu dauki.
Daliban sun koma Habasha
A halin da ake ciki kuma, daliban Nijeriya da ke cikin kasar Sudan an sanar da shirin kwashe su zuwa Habasha.
Kungiyar Dalibai ta Kasa Reshen Sudan ta sanar da hakan ne a jiya a cikin wata sanarwa da kwamitin yada labaranta ya fitar. Kungiyar ta umarci Mambobinta da za su hadu a wurare uku a Gadarif, babban birnin jihar Al Kadarif a Sudan, kafin a kwashe su zuwa makwabciyar kasar Habasha.
Kungiyar ta ce lokacin tashi zai kasance karfe 1 na rana kuma kudin sufuri ya kai Dala 100.
“Don haka ana sanar da dukkan daliban Nijeriya da su taru a kowane daga cikin wadannan wurare guda uku don ci gaba tsallakawa da zuwa Gadarif, sannan zuwa Habasha, ga wuraren kamar haka; 1. Jami’ar Ifrikiyyah 2. NANSS Office ko 3. Jami’ar El-Razi. “Duk wanda ba shi da kudi ya kamata ya tuntubi ko dai makarantarsu ko kuma shugaban jiha.
Ku zo tare da fasfo dinku, na asali/kwafin hoto ko katin shaida na makaranta. “Wadanda ba su da fasfo dinsu a hannu, su kuma su tuntubi shugaban jiharsu ko kuma shugaban makaranta,” kamar yadda sanarwar ta kara a wani bangare.
A jiya ne ofishin jakadancin Tarayyar Nijeriya da ke birnin Khartoum ya bukaci daliban Nijeriya da ke Sudan da su ci gaba da zama a gida yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen kwashe su daga kasar Sudan inda ake fama da matsalar yaki.
Wata sanarwa da ofishin jakadancin, mai dauke da sa hannun H. Y. Garko D’Aff ya bayyana a ranar Lahadin da ta gabata, ta shawarci daliban da su yi watsi da sanarwar da hukumar NANS ta kasar Sudan ta watsa, inda ta yi kira ga daliban da su hadu a Jami’ar International Unibersity, NANS office da El- Jami’ar Razi, don su karbi Dala 100 ko 200 don kafi kwashe su.
‘Yan Nijeriya na kukan neman ceto
A halin da ake ciki, daliban Nijeriya da ke makale a Sudan sun ce sun shiga cikin fargaba da tashin hankali a babban birnin kasar Khartoum. A wani faifan bidiyo a shafukan sada zumunta sun ce suna cikin mawuyacin hali don haka suna son gwamnatin Nijeriya ta kwashe su.
Daya daga cikin daliban, Fauziyya Idris Safiyo, wadda ta tashi daga birnin Khartoum zuwa garin Gallabat da ke kan iyakar Sudan da Habasha, ta ce lamarin na kara ta’ azzara.
Kwanaki biyu da suka wuce, ni da ‘yar uwata mara lafiya muka tafi Khartoum zuwa Gadarif.
A kan hanya muna iya ganin ‘yan Sudan su ma suna ta gudu. Mun isa ga jami’an Hukumar Shige da Fice na Sudan don samun biza zuwa kasar Habasha amma an ki a bamu saboda ba mu da bizar shiga.
“Mun ma nuna musu wata takarda daga ofishin jakadancin Nijeriya da ke Sudan, amma duk da haka basu ba mu biza ba. “Yau rana ta uku ke nan muna makale a kan iyakar Habasha.
“Don haka, mun nemi takardar bizar kuma an caje mu Dala 80 kowannenmu amma babu wanda zai iya sanin lokacin da bizar za ta shigo hannunmu saboda ranar hutu ce,” in ji ta.
Ta kuma koka da yadda har yanzu ‘yan Nijeriya da dama wadanda galibinsu mata ne da ke can a birnin Khartoum.
Suna fama da yunwa, babu abinci, babu ruwa sha ga duhu babu wutar lantarki.
Ana jiyo karar Fashewar abubuwa da karar manyan bindigogi ta ko’ina
“Wasu sun fake a masallatai, komai ya tsaya cak babu sauran motsi a Khartoum kuma ga mu nan kan iyaka.
“Mun samu labarin cewa Jami’an Shige da Fice na Habasha ba za su bamu biza ba, a cewar su, suna bayar da biza ne kadai ga ‘yan Sudan, abin da suke fada shi ne ba sa gane fasfo din Nijeriya,” in ji ta. Safi yo ta kuma bayyana cewa, jakadan Nijeriya shi ya hada su da Sarkin Hausawa na Gadarif wanda ya ba su mafaka.
Ta ce sun gamsu da wurin zama na Samariyawa. “Ya dauke mu a matsayin ’ya’yansa kuma yana taimaka mana wajen tabbatar da mun samu biza. Har ma ya gaya mana cewa yana da karfin daukar dukkan daliban Nijeriya da suka makale a kasar.
Har ma ya hana mahukuntan Sudan shiga masaukinsa, yana mai cewa ya tanada ne ga daliban Nijeriya na Sudan.
“Amma abin dubawa a nan shi ne wadannan daliban ba za su iya barin Khartoum ba yayin da wasu kasashe suka kwashe dalibansu?. Tanzaniya ta aike da wata motar bas wadda ta kwashe dalibanta, sannan kuma hukumomin makarantar sun bai wa daliban Malawi motar bas domin kwashe su.
Daliban Siriya da na Somaliya su ma sun tashi daga jiya. Daliban Nijeriya ne kawai aka bari a cikin rudani.”
A cikin kimanin daliban Nijeriya 4,000 da ke Sudan, bakwai ne kawai suka iya tashi daga babban birnin Khartoum zuwa kan iyakar kasar da Habasha, in ji ta. Ta lura cewa suna cikin kwanciyar hankali a garin Gadarif da ke kan iyaka, ta kara da cewa “Muna jiran biza ne kawai don komawa gida.”
“Mun yi amfani da kudinmu wajen tashi daga Khartoum amma yawancin dalibai ba su da hanyar tashi. Don haka ya kamata gwamnati ta nemo hanyoyin da za ta kwashe abokan aikinmu, a kalla a kawo su Gadarif don gudanar da bizarsu, daga baya kuma su fice daga kasar.
“Muna ta jiyo karar harbe-harbe da tashin bama-bamai daga kowane bangare. Mayakan Jet kuma suna ta harbi da harsasai. Babu abinci, babu ruwa da magunguna. Ba ma iya tafiya ko’ina ba. Kudi ya kare, kuma akwai yawaitar masu aikata laifuka a ko’ina,” in ji ta.
A cewarta, “’Yan Nijeriya ne kawai aka bar su a yashe, tare da mata da yawa a cikinmu. Wasu kasashe makwabta kamar Habasha ba sa barin ‘yan Nijeriya shiga kasashensu ba tare da biza ba,” in ji ta.
Shima da yake magana game da mawuyacin halin da suke ciki, Shugaban Daliban Nijeriya na jami’ar Sudan International, Muhammad Nura Bello, ya ce akwai bakar da da aka samu kuma ‘yan Sudan suma suna daga cikin masu faman tada zaune tsaye.
“Yawancin daliban sun firgita sosai saboda wasu kayan abincinsu ya kare kuma za ka ga hatta ‘yan kasar ma za ka ga suna gudu,” in ji shi. ba ma samun bacci idan dare ya yi.
Fadar shugaban kasa, a ranar Lahadi, ta ce gwamnatin tarayya na kokarin tabbatar da tsaron lafiyar ‘yan Nijeriya a Sudan.
Garba Shehu, babban mataimaki na musamman ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Kan Harkokin Yada Labarai ne ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a shafin sa na Twitter @GarShehu.
Mai magana da yawun shugaban kasar ya ce jami’an Nijeriya na yin kokari sosai tare da ofishin jakadancin da ke Khartoum, da gwamnatocin Sudan da Habasha.
A gaggauta daukar mataki
Tsohon Jakadan Nijeriya a Afirka ta Kudu da Benezuela, Martins Cobham, ya koka kan halin da ake ciki a Sudan, ya yi kira ga Gwamnatin Nijeriya da ta gaggauta daukar matakin kwaso ‘yan Nijeriya da suka makale daga kasar mai fama da rikici.
Cobham ya ce akwai ‘yan Nijeriya da dama a Sudan, inda ya kara da cewa wasu daga cikinsu sun shafe shekaru suna zaune a can kuma watakila ba sa son komawa Nijeriya. Ya shawarci gwamnatin tarayya da ta dauki bayanan wadanda suke son a kwashe su fara aikin na ceto su nan take.
Ya ce gwamnati na iya tuntubar wasu kasashe domin neman taimako idan ta ga hakan yana da wahala domin a gudanar da aikin yadda ya kamata.
Rikicin ya yi barna a harkar sufurin jiragen sama na kasuwanci yayin da kamfanonin jiragen sama ke kauracewa sararin samaniyar kasar. Rikicin Kasar Sudan dai ya yi tasiri ga harkar sufurin jiragen sama inda kamfanonin jiragen sama ke kidayar asarar da suka yi yayin da suke kaucewa sararin samaniyar Sudan.
Daily Trust ta ruwaito cewa, kamfanonin jiragen sama da ke tashi daga Nijeriya zuwa Saudiyya ne suka fi fuskantar matsalar, wanda hakan ya haifar da tsaikon dawowar alhazai daga aikin (Umrah) a Saudiyya.
An fara samun wannan tasiri ne a lokacin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, wanda ya shafe mako guda a Kasar Saudiyya domin gabatar da Umrah, ya kwashe sama da sa’o’i bakwai daga Saudiyya zuwa Abuja, yana tafiyar kimanin sa’o’i hudu da rabi.
Wakilinmu ya ruwaito cewa Jeddah na da kusan awa hudu da rabi daga Nnamdi
Azikwe International Airport, Abuja da awa biyar ta filin jirgin sama na Murtala Muhammed (MMIA), Legas.
Daily Trust ta ruwaito cewa duk wani kamfanin jirgin da zai yi jigilar Nijeriya zuwa kasar Saudiyya sai ya kara kone man fetur na kimanin sa’o’i uku wanda aka ce hakan ya janyo karin kudin aiki.
Misali, wani faffadan jirgin da kamfanonin jiragen sama ake amfani da shi a kan hanya, kamar B747, yana cinye kusan lita 11,400 na man fetur a sa’a guda. Tare da karin sa’o’i uku zuwa lokacin tashin jirgin, wanda ke nufin karin lita 34,200.
Idan aka ninka shi da Naira 700 wanda ya kai kimanin lita daya na man jiragen sama, hakan na nufin karin Naira miliyan 23.9 da kamfanonin jiragen suka yi kan mai.
Wani mai sharhi kan harkokin sufurin jiragen sama, Mista Olumide Ohunayo, a wata zantawa da ya yi da wakilinmu, ya ce rikicin kasar Sudan, wanda ya ce ba zato ba tsammani, ya yi illa ga harkokin sufurin jiragen sama na kasuwanci.