Mutuwar shahararren mawaki Ilerioluwa Aloba, wanda aka fi sani da Mohbad it ace maganar da aka shafe kusan makonni biyu ana tattauna ta a shafukan sada zumunta a fadin kasar nan baki daya.
Mawakin mai shekaru 27 ya rasu ne a ranar 12 ga watan Satumba cikin wani yanayi mai cike da rudani da ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin abokan sana’ar sa a jihar Legas.
- A Shirye Sin Take Ta Inganta Hadin Gwiwa Da UNESCO Domin Samar Da Ci Gaba Da Zaman Lafiya A Duniya
- Sulhu Da ‘Yan Bindiga A Asirce: Sa-in-sa Ta Kaure Tsakanin Gwamnatin Tarayya Da Ta Zamfara
Sai dai wani abu mai kama da zargi da rudani shi ne kwana daya bayan rasuwarsa aka yi jana’izarsa, wani abu da shi ma ya janyo ka-ce-na-ce saboda abune wanda ba’a saba gani ba kasancewar sa ba musilmi ba ne kuma akanyi bukuku musamman idan wani ya mutu a cikin kabilar da aka haife shi.
Amma kuma a ranar Alhamis ‘yan sanda suka tono gawar Mohbad domin gudanar da bincike bayan da aka yi ta samun korafe-korafe har daga mawaka abokansa.
Itama gwamnatin jihar Legas karkashin mulkin Babajide Sanwo-Olu, ta bayar da umurni a hukunta duk wanda ya taka wata rawa da ta kai ga mutuwar mawakin.
Ya yinda rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta ce ta kammala bincike kan gawar mawaki Ilerioluwa Aloba, wanda aka fi sani da Mohbad kuma a cewar rundunar, ta kammala binciken cikin nasara.
Dubban mutane ne suka yi zanga-zanga a sassan kasar nan musamman ma dai a jihar Legas da makwabtan jihohi domin nuna fushinsu kan yadda mawakin na Afrobeat ya mutu cikin wani yanayi mai cike da alamar tambaya.
A birnin Legas, an yi wani taro na zaman jimami a ranar Alhamis din satin da ya gabata inda aka ga matasa suna tattaki suna kiran da a bi wa mawakin kadinsa.
Rahotanni sun ce fitattun mawaka irinsu Dabido, Zlatan da Falz sun halarci taron zaman jimamin duk da cewa hukumomi sun gudanar da bincike kan gawar Mohbad.
Mohbad ya rasu ne bayan da aka garzaya da shi wani asibiti bisa wani rashin lafiya da ba a sani ba sai dai bayanai sun yi nuni da cewa, an yi wa mawakin wata allura a lokacin da aka kai shi asibitin inda daga nan kuma sai rai ya yi halinsa.
Mohbad, wanda a da mawaki ne karkashin kamfanin Malians na fitccen mawaki Naira Marley, ya fito idon duniya da wakokinsa irinsu ‘Ponmo, Peace, Ask About Me’ da sauransu.
A bara ne ya kuma fice daga kamfanin bisa wasu dalilai da har yanzu ba a fayyace ba sai dai daman hakan baya rasa nasaba da irin rikice-rikice da ake yawan samu a tsakanin masu irin wannan sana’ar Itama kungiyar nan ta kare muradun yarabawa da OPC ta bukaci gwamnati da jami’an tsaro akan suyi iya yinsu domin ganin an yiwa marigayi Mohbad adalci.
Kungiyar tace da ace marigayi Mohbad ya bayyana halin firgici da tashin hankalin da yake ciki ga kungiyar da tuni ba a kai ga haka ba kuma za su dauki matakin kare shi daga masu yi masa barazana ga rayuwa.
Kungiyar OPC dai ta bukaci rundunar ‘yan sanda ta kasa da jami’an hukumar tsaro ta farin kaya DSS da suyi kokarin gano wadanda suka kashe mawakin domin a hukunta su.
Wani tsohon faifan bidiyo na Bella Shmurda yana cewa Mohbad yana fama da matsalar tabin hankali kwanan nan ya sake kunno kai a yanar gizo mintuna bayan mutuwar mawakin.
Bayanai kan musabbabin mutuwarsa da kuma inda ya rasu yana ci gaba da zayyana har lokacin da ake hada wannan rahoto.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp