Hukumar kula da kwallon kafa ta duniya, FIFA, ta fitar sunayen wadanda za a zaba a matsayin fitattaun ’yan kwallo na duniya daga cikinsu, wadanda suka hada da Cristiano Ronaldo daga Real Madrid dan kasar Portugal da Lionel Messi daga Barcelona na Argentina da kuma Neymar daga Paris St-Germain dan kasar Brazil.
A shekarar da ta gabata dai Ronaldo ne ya lashe kyautar gwarzon dan wasan bayan da ya doke Messi da Neymar da kuma Antoine Griezmann na Atletico Madrid.
Ronaldo ya taba lashe kyautar sau hudu, inda a bara ya lashe gasar cin kofin laliga da kuma kofin zakarun Turai da Real Madrid, sannan kuma shi ne yafi kowanne dan wasa zura kwallo a raga a gasar ta zakarun Turai da su ka lashe.
Messi, wanda ya fi kowa lashe kyautar, inda ya lashe ta sau biyar, da Neymar na kasar Brazil su ne abokan karawar Ronaldo bayan da su ka lashe kofin Copa del Rey na kasar ta Spaniya, sai dai yanzu Neymar ya bar kungiyar inda a yanzu ya ke taka leda a sabon kulob dinsa na PSG.
Hukumar dai ta kuma fitar da sunayen masu koyarwa guda uku wadanda su ma a cikinsu ne za a zabi wanda ya fi fice, Akwai Zinedine Zidane na Real Madrid dan kasar Faransa da Antonio Conte na Chelsea dan kasar Italiya sai kuma takwaransa na Jubentus shi ma dan kasar Italiya, wato Madililiano Alegri.
Kocin Chealsea Antonio Conte na iya lashe kofin gwarzon koci bayan da ya ja ragamar kungiyar har su ka kai da samun nasarar lashe kofin Premier a kakarsa ta farko a Stamford Bridge.
Yayin da shi ma Zidane zai iya lashe kyautar bayan da ya ja ragamar Real Madrid ta lashe gasar Laliga da kofin zakarun Turai.
Shi ma Alegri ya jagoranci jubentus ta lashe gasar Serie A, sannan kuma ya kai kungiyar wasan karshe na cin kofin zakarun Turai sai dai sun sha kasha da ci 4-1 a hannun Real Madrid.
An sake gabatar da mai rike da kofin fitacciyar ‘yar kwallon kafar mata Carli Lloyd a matsayin wacce za ta lashe kofin na bana.
Lieke Martens wadda ta ci kwallo uku a wasan neman shiga gasar Euro 2017 a Netherland, da kuma ‘yar kwallon Benezuela Deyna Castellanos su ne abokan karawar Lloyd.
A ranar 23 ga watan Oktoba ne za a gabar da wadanda su ka yi nasara a dakin taro na Palladium da ke Landan.