Shugaban hukumar kwallon kafar Spain, Luis Rubiales, ya yi murabus daga mukaminsa, sakamakon sukar da aka yi masa na sumbatar Jenni Hermoso a lebe a wasan karshe na gasar cin kofin duniya ta mata.
Tuni dai aka dakatar da Rubiales,ya aika da takardar murabus dinsa zuwa ga shugaban riko na hukumar.
- Share Fagen Gasar Kofin Duniya; Messi Ya Zura Kwallo A Ragar Ecuador
- Lamine Yamal Ya Zama Dan Wasa Mafi Karancin Shekaru Da Ya Bugawa Sifen Kwallo
A wata budaddiyar wasika,Rubiales ya bayyana matakinsa na sauka daga karshe a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin.
Nayi murabus ne saboda ba zan iya ci gaba da aiki na ba in ji Rubiales a cikin wata hira da gidan talabijin.
An bani shawarar cewa ina bukatar in mai da hankali ga mutuncina kuma in ci gaba da rayuwata inji Rubiales.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp