Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce yanzu haka ‘yan Nijeriya na cin shinkafar gida bayan rufe iyakokin kasar na tsawon shekaru.
Buhari ya yaba wa manoman kasar nan kan yadda suke noman shinkafa da sauran kayan abinci.
- Babu Wata Shawara Da DSS Ta Aike Wa Buhari Kan Takarar Musulmi Da Musulmi – Fadar Shugaban Kasa
- Gwamnan Gombe Ya Yi Alhinin Rasuwar Sheikh Maigano Da Ya Rasu A Saudiyya
Shugaba Buhari ya yi wannan jawabi ne a jiya Juma’a a Katsina, wajen wani taro da ya gudanar da zababbun shugabannin Kananan Hukumomin jihar.
Shugaban ya bayyana jin dadinsa da yadda manufofin gwamnatinsa na noma su kai aiki yadda ya kamata.
Buhari ya ce yana da kyakkyawar fahimtar al’ummar Nijeriya, haka tasa suka rungumi tsare-tsarensa na noma.
“Na ce dole ne mu noma abin da muke ci kuma mu ci abin da muka noma. Wannan kasa ce da ta taba dogaro da shinkafar waje a baya.
“Mun rufe iyakarmu don hana shigo da shinkafar waje. Hakan ta sa na ce me yasa ba za mu cin shinkafar mu ta gida Nijeriya ba, kuma ga shi nan bisa tsarin da muka yi, yanzu haka ‘yan Nijeriya suna cin shinkafar gida.” In ji Buhari
Buhari ya kara da cewa aiwatar da tsarin asusun bai daya ya taimaka wa gwamnati wajen dakile ayyukan jami’an gwamnati marasa kishin kasa.