Wannan masallaci an fara samar da shi ne a matsayin masallacin Juma’a a shekara ta 1836, a wata Unguwa da ta yi shuhura kan karantar da addinin musulunci da ake kira Unguwar Jumatun kafin jihadin Shehu Usman Dan Fodiyo.
Fitaccen masanin tarihin nan kuma Sarkin Ayyukan Zazzau, Malam (Barista) Muhammad Abbas Fagachi ya yi wa wakilinmu tsakure kan tarihin wannan masallaci inda ya ce tun a shekarar da aka ambata, aka fara ginin wannan masallaci a Unguwar Juma da aka ambata a zamanin Sarkin Zazzau Malam Musa.
“Bayan jihadin Shehu Dan Fodiyo sai Malam Musa Sarkin Zazzau na wancan lokaci ya nemi izini wajen Shehu na ya dawo da masallacin Juma’a na Zazzau da ke Unguwar Juma, kamar yadda aka ambata a baya, sai Shehu Dan Fodiyo ya amince masa. Allah cikin ikonsa, Sarkin Zazzau Malam Musa bai sami damar cika burinsa na gina massalacin a Kofar Fadar Zazzau ba, sai Allah ya karbi rayuwarsa. Wanda ya zama Sarkin Zazzau bayan Malam Musa shi Malam Abdulkarimu, ya na hawa karagar Zazzau sai ya fara yunkurin aiwatar da kudurin marigayi sarkin da ya gada wato Malam Musa.”
Dangane da inda masallacin yake a yau kuwa, Malam Abbas Fagachi Sarkin Ayyukan Zazzau ya shaida wa wakilinmu cewar wasu gine -gine da sarakunan Zazzau suka yi domin aje kayayyakin tarihi da suka shafi masarautar Zazzau ne aka kwashe tare da dora harsashin ginin masallacin.
“A lokacin da mai martaba Sarkin Zazzau Abdulkarimi ya yanke shawarar fara gina masallacin da Shehu Dan Fodiyo ya amince masa, kwatsam sai aka habarta masa wani fitaccen magini da ke wata Unguwa a birnin Zariya, maginin sunansa Muhammadu Durugu, nan take sarki ya sa aka kira shi, ba tare da bata lokaci ba ya fara ginin masallacin a Kofar Fadar Zazzau inda masallacin yake a yau.
“A kwai zantuka masu harshen damo da suka bayyana yadda wannan bawan Allah magini ya aiwatar da bukatar Sarkin Zazzau Malam Abdulkarimi, wato kamar yadda yawan wadanda suke jefa masa laka a lokaci guda ba tare da laka ko kuma tubali daya ya dawo kasa ba.”
Wannan magini a wadancan shekaru, a cewar Sarkin Ayyukann Zazzau Malam Abbas Fagachi, ya na zaune ne a wannan Unguwa da a yau ake kira da Unguwar Babban Gwani. Kuma bayan kammala gina masallacin saboda gamsuwa da Sarkun Zazzau Malam Abdulkarimi ya yi na yadda wannan magini ya aiwatar da bukatar Sarki, sai aka nada shi Sarkin Maginan Zazzau, inda har zuwa yau zuriyyar Muhammadu Durugu ne ke sarautar Sarkin Magina a Zazzau.
Sarkin Ayyukan na Zazzau ya kuma shaida wa wakilinmu cewa, ko bayan Sarkin Zazzau Malam Abdulkarimi tun daga kan Sarkin Zazzau Malam Jafar Dan Isiyaku har zuwa Sarki Shehu Idris, a zamanin kowanne Sarki sai da aka yi wa wasu sassan masallacin gyare-gyare, musamman a zamanin Sarkin Muhammadu Aminu ne aka yi wa masallacin gyaran da aka sa siminti, haka nan a zamanin Sarkin Shehu Idris an yi gyare -gyare masu yawan gaske.
A lokacin da mai martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmed Nuhu Bamalli ya hau karagar Zazzau, a cewar Sarkin Ayyukan Zazzau, ya furta yiwuwar yin gyare -gyare a wannan masallaci, domin abin da ya gani na nau’in kasar da ke masallacin. A lokacin da ya fara gyare-gyare a cikin Fadar Zazzau, ya kudiri aniyar gyara duk ginin masallaci da aka yi da kasa. Amma Allah cikin ikonsa, sai wannan matsala ta rushewar rufin masallacin ya auku, inda mutum takwas suka rasu wasu kuma da dama suka sami munanan raunuka.
Bayan faruwar wannan matsala da kwana daya mai martaba Sarkin Zazzau, ya bayar da umurnin rufe masallacin, har sai an gyara za a ci gaba da salloli a ciki.
Wani abu kuma da ganau a lokacin da matsala ruftawar ginin ta auku ya bayyana wa wakilinmu shi ne, al’amarin ya faru sarkin ya je bude masallacin Juma’a a karamar hukumar Soba, “yana dawowa sai ya ga al’umma a fadarsa, ya tambaya aka ce ga abin da ya faru, nan ta ke ya cire alkyabbarsa, har gudu ya yi zuwa cikin masallacin, da shi aka rika zakulo wadanda kasa ta rufe su, aka ciro wasu gawa, wasu kuma sun sami mummunan raunuka.
“Kuma mai martaba Sarkin Zazzau ya aika da sakon kudi ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu, domin gudanar da jana’izarsu, kuma ya nemi a kawo gawarwakin Fadar Zazzau, domin yi ma su Sallah, tun kafin fara sallah ruwan sama kamar da bakin kwarya aka yi har kammala sallar gawarwakin ana ruwa ba tare an sa wa mai martaba Sarki lema ba.
“A game da batutuwan da ake yi cewa wasu matsaloli ne suka sa masallacin ya fada wa wadanda ke sallah, duk jita-jita ne, illa kasar da aka rufe masallacin fiye da shekara dari biyu ita ce ta mutu, Allah kuma ya aiwatar da ikonsa a wannan rana da rufin ya fada wa al’umma da suke sallar la’asar.” In ji ganau din.