Connect with us

JAKAR MAGORI

Rundunar ‘Yan Sanda Ta Cafke Kasurguman ‘Yan Bindigar Da A Ke Nema

Published

on

Jami’an ‘yan sandan rundunar IRS (Intelligence Response Team) sun samu nasarar Cafke tawagar wasu da ake zargin ma su garkuwa da mutane ne da suka kashe mutane uku bayan karbar miliyan Naira miliyan 7.5 a matsayin kudin fansa daga hannun ‘yan uwansu. Kakakin rundunar ‘yan sanda na kasa, Frank Mba, shi ne ya sanar da hakan a Abuja yayin bajakolin masu laifi su 26 da suka hada da ma su garkuwa da mutane, ‘yan fashi da makami da ma su safara mugayen makamai.

Rundunar ‘yan sanda ta yi bajakolin ma su laifin ne a yau, a hedikwatarta ta kasa da ke birnin tarayya, Abuja. A cewar Mba, tawagar ma su garkuwa da mutanen ne suka sace Dakta Audu Benedict, dansa, da kuma abokinsa a kan hanyarsu ta zuwa Abuja daga Jihar Benuwe. Dangi da ‘yan uwan Dakta Audu sun hada Naira miliyan 7 tare da ba wa masu garkuwa da mutane a matsayin kudin fansarsa tare da sauran mutanen da aka kamasu tare. “Kafin a kai mu su Naira miliyan 7 da suka nema, ma su garkuwa da mutanen sun tilasta Dakta Audu rubuta mu su takardar fitar da kudi har N500,000 saboda su na bukatar wasu kudi cikin gaggawa,” a cewar Mba. Mba ya kara da cewa amma duk da haka sai da ma su garkuwa da mutanen suka kashe Dakta Audu tare da dansa da abokinsa da aka kama su tare.

“Daga cikin masu garkuwar da muka kama akwai wadanda su ka addabi jama’ar yankin Arewa ta Tsakiya. “Iyalin Dakta Audu sun biya kudin fansa Naira miliyan 7. Kafin a kai wa masu garkuwa da mutane kudin, sun tilasta Dakta Audu rubuta takardar fitar da kudi N500,000 daga asusunsa na banki.

“Amma duk da sun karbi jimillar kudin da yawansu ya kai Naira miliyan 7.5, hakan bai hana su kashe Dakta Audu tare da dansa da abokinsa ba,” a cewar kakakin rundunar ‘yan sanda. Kazalika, ya kara da cewa tawagar masu garkuwa da mutanen sun sace wata mata mai suna Beronica Aboyi, wacce ke da alaka ta jini da daya daga cikin masu laifin. Biyu daga cikin masu laifin; Gwar Henry da Bello sun amsa laifinsu. Rundunar ‘yan sanda ta ce ta kama bindigu samfurin AK47 guda 6, wasu manyan bindigu guda 3, da sauran wasu mugayen makamai.

A wani rahoton kuma, Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Masari ya bai wa rundunar soji umarnin gamawa da ‘yan bindiga da ke kashe ‘yan jihar. Ya Kara da cewa kada a bar dan bindiga ko daya da rai. Masari ya yi wannan kiran ne yayin da ya kai ziyara ga ‘yan gudun hijira a kananan hukumomin Faskari, Kadisau da Dandume na jihar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: