Daga Hussaini Yero,
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara karkashin jagorancin Kwamishina ‘Yan Sanda, CP Abutu Yaro, tare da hadin gwiwar da kwamitin sulhu na jihar sun tabbatar da sakin mutane 10 daga hannun masu garkuwa da mutane a kauyen Kaya da yake Karamar Hukumar Maradun.
Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sanda na Jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu, ya bayyana haka a takardar da ya sanya ma hannu ya raba wa manema labarai a Gusau, Babban Birnin jihar.
A cewarsa, wadanda aka sacen a Karamar hukumar Maradun, sun hada da mata bakwai da maza uku, kuma an sace su zuwa dajin Sububu, amma cikin taimakon Allah da kwamitin sulhu na Gwamna Bello Muhammad Matawalle Maradun ya sanya aka ceto su.
Ya ce, kuma tuni kwamitin sulhun ya mika su ga iyalansu dake Kaya a cikin Karamar hukunar ta Maradun.