Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da rasuwar ɗaya daga cikin manyan jami’anta, ACP Aminu Umar Dayi, da wani jami’inta guda wanda ‘yan bindiga suka kashe a yau talata a Katsina.
Wannan yana kunshe cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar wanda kakakinta, SP Gambo Isah, ya sanyawa hannu aka rabawa manema labarai a Katsina.
- Sallah: ‘Yan Bindiga Sun Kai Wa Tawagar Shugaba Buhari Hari A Hanyarsa Ta Zuwa Katsina
- ‘Yan Sanda Sun Kama Wata Mata Da Ta Sace Yarinya A Anambra
Sanarwar ta ce a yau talata da misalin karfe 11:30 na safe, rundunar ‘yan sanda ta samu rahoton gaggawa da ke cewa, an hango ɓarayin daji sama da 300 a kan mashina suna ta harɓe-harben bindiga kirar AK 47 da GPMG inda suka kai farmaki tawagar ACP Aminu Umar a dajin Zakka a lokacin da suke aikin samar da tsaro a wannan daji da ke cikin ƙaramar hukumar Safana.
Sai dai bisa ƙadarrar Allah ACP Aminu Umar tare da wani jami’in ɗan sanda sun rasa rayukansu a lokacin musayar wuta da ‘yan ta’ada.
Sanarwar kwamishinan ‘yan sanda na jihar Katsina, Idrisu Dauda, a madadin rundunar ‘yan sanda cikin alhini ya isar da sakon ta’aziyarsu ga iyalan mamacin da sauran al’uma.
Daga nan ya ƙara bada tabbacin rundunar ‘yan sandan na ci gaba da yakar ‘yan bindiga har sai sun kawo karshen ayyukan ta’addancin a jihar Katsina baƙi-ɗaya.