Connect with us

RAHOTANNI

Sa Ohaa: Shahararre Kuma Jajirtaccen Ma’aikacin Gwamnati

Published

on

“Ga dukkan Shugaba na kwarai za ka tarad da dabi’un kirki.” Wannan dan gajeren bayani wanda Brian Cooper ya yi, babu komi a cikinsa face gaskiya, wanda kuma sun fayyace wanene Sa Christian Chinyeaka Ohaa, Babban Sakataren sashen gudanarwa na Birnin Tarayya, Abuja
Ba karamin aiki ba ne ke gaban Babban Sakatare a ma’aikatu na zamani, amma idan ya zama an samo mutum mai kwarewa da ilimi sai ka ga aikin ya zama mai sauki. Babban Sakatare shi ne mai daidaita al’amura a gwamnati.
Dole ne abubuwa su zama masu yawa da fadi ga Babban Sakataren a Babban Birnin Tarayya, wanda a nan duk wata hada-hada take. Sannan kuma a irin wannan, ana bukatae mutumin da ba shi da nuna kabilanci kuma mai taka-tsantsan irin Ohaa. Tun bayan da ya zama Babban Sakataren Birnin Tarayya shekaru uku da suka gabata, abubuwa sun canza sosai.
Wani babban aiki da Ohaa ya yi a Babban Birnin tarayya shi ne hada kan ma’aikata. Burinsa shi ne a yi aiki ba tare da la’akari da wa zai a yaba ba. Da irin wannan dabi’a Oha ya ke gudanar da ayyuka a Abuja.
Ya samar da yanayin kirkiro sabbin abubuwa na zamani. A aikinsa, ba ya damuwa da kai dan wanne kabila ne ko daga ina ka ke. Shi dai damuwarsa a yi aiki.
Haka kuma Ohaa a aikinsa yana matukar muhimmanta dokokin aikin gwamnati, yana taka-tsantsan wurin jefa kanshi cikin harkar siyasa domin yin aikinsa ba tare da wata matsala ba. Saboda haka ne ma yake aikinsa ba tare da ya wulakanta wani don bangarincin addini, jinsi ko kabila ba.
Wani karin dabi’a da Oha ke da ita shi ne yadda ya yi tsayin daka wurin ganin ya samar da ingantaccen tsarin gudanar da kudi da hulda da jama’a. A tafiyar da ayyukan gwamnati ya nuna cewa shi din na daban ne.
A duk lokacin da aka samu ma’aikacin gwamnatin da ya muhimmanta aikin fiye da son ransa, za a ga ci gaba sosai. Yana da alakar aiki mai kyau tsakaninsa da Ministan Abuja, Mallam Muhammed Bello. Biyayyarsa ga na-gaba da shi a fagen aiki wani abin ban sha’awa ne. Wannan ne ma ya sa ya samu karbuwa da aminta a wurin Ministan. A wasu ma’aikatan ana ganin yadda ake samun sabani karara tsakanin ma’aikata, amma a Babban Birnin Tarayya, inda Sa Ohaa ke Babban Sakatare, aiki ake yi tsakanin juna babu kama hannun yaro.
Tsakanin Oha da Daraktocin Ma’aikatar Babban Birnin Tarayya suna aiki ne da fahimtar juna. Kaunar ma’aikata da ba su uzuri a kodayaushe ya janyo mishi kauna a zukatansu.
Sa Oha ya kasance mutum mai cikakkiyar biyayya ga na gaba da shi. Falsafarsa ita ce, abin da son rai ba zai iya samarwa ba, aiki tare na iyawa. Haka nan kuma ya yi imanin cewa komi dadewar karya tana nan a matsayinta na karya, ita kuwa gaskiya ba za ta taba sauya sun aba.
Ohaa y fito ne daga gidan Cif Ohaa Owo, an haife shi a ranar 4 ga watan Fabrairun 1961 a Obuoffia da ke Karamar Hukumar Nkanu ta yamma ta Jihar Inugu. Ya yi aure inda Ubangiji ya albarkace shi da ‘ya’ya. Oha yana da satifiket din karatu kamar haka: GCE-1979, WASC -1980, Babbar Difloma a fannin Kimiyyar Kudi -1985, PGD, Kan fanin Kimiyyar kudi -1990, MBA, fannin kimiyyar kudi-1992.
Oha ya kasance memba a ‘National Accountant of Nigeria (FCNA)-2010’ haka kuma memba ne na Kungiyar ‘Chartered Institute of Tadation of Nigeria (CITN)-2012’ da dai sauransu.
Sa Oha yana da dadadden tarihin aikin gwamnati da ma’aikatu masu zaman kansu. Domin kuwa ya fara samun kwarewa ne a ‘Co-operatibe & Commerce Bank of Nigeria Ltd’ inda ya yi hidimar kasa daga shekarar 1985 zuwa 1986). Bayan ya kammala hidimtawa kasa sai ya fara aiki a matsayin mai kula da harkokin kudi a Cibiyar Ilimi ta Jihar Inugu (daga shekarar 1986 zuwa 1989), ya zama akawun kamfanin ‘banguard Industries LTD’ da ke Jihar Inugu (daga shekarar 1989 zuwa 1992).
Oha ya zama mai bada shawara ga kwamishinan kudi na Jihar Inugu (daga shekarar 1992 zuwa 1993), mataimakin ma’aji a ofishin Babban Akawun Jihar Inugu (daga shekarar 1993 zuwa 1996), Mataimakin Ma’aji a kan harkar filaye na ofishin Babban Akawun Jihar Inugu (daga shekarar 1996 zuwa 1999).
Daga shekarar 1999 zuwa 2006 ne kuma ya rike mukamin Babban Akawun Jihar Inugu, daga nan ya zama Kwamishinan Noma (dga shekarar 2006 zuwa 2007). Daga nan ne ya nemi sauyin aiki daga matakin jiha zuwa matakin tarayya, inda aka ba shi mukamin mataimakin Darakta a Ma’aikatar Kwadago (daga shekarar 2007 zuwa 2009).
A shekarar 2009 ne ya zama shugaban sashen bin diddigi na Ma’aikatar Tsro, mukamin da ya rike har zuwa shekarar 2012. Inda daga can aka mayar da shi Ma’aikatar Sufuri a matsayin Daraktan Kudi (daga shekarar 2012 zuwa 2013), daga bisani ya koma Ma’aikatar Ma’adinan Ruwa, a matsyain Daraktan Kudi. A shekarar 2015 ne kuma aka yi mishi Babban Sakatare na Ma’aikatar Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Ohaa yana da kwarewa da ilimi a fannoni mabambanta, domin ya halarci kwasa-kwasai har a kasashen waje irinsu Landan, Amurka, Dubai da sauransu
An Shaidi Oha da son ganin rayuwar matasa ta bunkasa. Haka nan mutum ne mai son ganin an raya karkara da hanyoyin ci gaba mabambanta. Ya kasance jigo kuma abin kauna a wurin al’umma, ga shi mutum mai riko da addini. Ya rike mukamai mabambanta na hidima ga al’umma da addini, Shi ne Shugaban Kungiyar Awkunanaw, Shugaban iklisiyyar Methodist d dai sauransu.
Kishin Kasa da yin aiki a bayyane sun bayyana wane ne Sa Oha. Wannan ne ma ya janyo aka nada shi Babban Sakataren Ma’aikatar Birnin Tarayya.
– Ibrahim Shi ne Daraktan Sadarwa Da Tsare-tsare na Kwamitin Tallafawa Shugaban Kasa ‘Presidential Support Committee’ (PSC).
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: