Sabbin Ministocin Da Osinbajo Ya Rantsar Za Su Kama Aiki

Mukaddashin shugaban Nijeriya, Yemi Osinbajo, ya mika wa sabbin ministocin da aka rantsar dasu sati uku da suka wuce ma’aikatu.

An rantsar da Sulaiman Hassan da Stephen Ocheni tun a watan Mayu, bayan yan majalisar dattawa sun tattance su.

Mista Ocheni shine zai maye gurbin da marigayi James Ocholi ya bari sanadiyar mutuwarsa a hadarin mota bara, dukkansu yan jihar Kogi ne, zai kama aiki a matsayin karamin minista a ma’aikatar kwadago

Sulaiman hassan shi kuma zai cike gurbin jihar Gombe ne a matsayin karamin ministan, wuta, ayyuka da gidaje.

Exit mobile version