Duba da irin biliyoyin basukan gida da na ketare da zababbun gwamnoni za su yi kwalli da su bayan rantsar da su kama aiki, wannan dalili ne zai sa a yi musu kallon suna tsaka mai wuya!
Da mutanen jihata da sauran jihohin wannan Kasa za su amshi ra’ayin wannan marubuci, da sai su koma gefe, zuwa wani lokaci, suna masu gabatar da kyawawan shawarwari ga wadanda suka sami nasarar lashe zabukan kujerun gwamnoni a jihohin nasu kawai, ba tare da nuna zalamar sai an sallame su yanzu yanzu ba.
Cikin zabukan gwamnoni da aka gabatar a jihohi 28 na wannan Kasa daga daukacin jihohi 36, za a ga cewa, 16 daga cikin wadancan zababbun gwamnoni, sune wadanda suka amshi mulki daga hannun gwamnonin da suka kammala wa’adin mulkinsu na zango biyu da Tsarin Mulki na Kasa ya sahale musu, cikinsu har da jihar Kano. Kujerar gwamna guda ce wanda bai kammala zangon mulki biyu ba, aka samu wata jam’iyyar adawa ta yi mahangur6a ta amshe.
Yanzu haka wadannan zababbun gwamnoni 17, akwai wasu nau’ikan basuka iri biyu (bashin gida da na ketare), wadanda ke zaman jiran su zo, su san yadda za su yi da su. Irin wannan tarko na tsoffin gwamnoni da sunan cin bashi, tamkar irinsa ne shugaba Buhari zai gadar wa da sabon shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. Zancen nan da ake, akwai zunzurutun bashi na gida kawai, har kimanin naira miliyan dubu sau dubu (naira tiriliyan guda) da kuma naira miliyan dubu daya (N 2.1 tn) da tsoffin gwamnonin suka bar wa sabbin jini kuma sabbin gwamnoni 17 masu jiran gado.
Ba ya ga irin wadancan madudan basuka na gida, har ila yau, akwai zunzurutun basuka na waje har kimanin dalar Amurka miliyan dubu daya, da dala miliyan dari tara ($ 1.9 bn), da tsoffin gwamnonin suka jibga wa sabbi.
A jihar Abia, inda Dr Aled Otti zai karbi ragamar mulki daga Dr Okezie Ikpeazu, ta tabbata cewa, zai gaji zunzurutun bashi na gida kawai, har kimanin naira miliyan dubu 104, da miliyan dari 573 da kuma naira dubu 334 ( N 104, 573, 334, 025. 73). Sannan, akwai ma tulin bashi daga ketare da zai gada har kimanin dalar Amurka dubu 95 da dubu dari 632 da dari 239 ($ 95, 632, 239. 04).
Bugu da kari, a dai waccan jiha ta Abia, sabon gwamna Otti, zai gaji nauyin rashin biyan albashi na watanni 10 zuwa 27 a tsakanin ma’aikatan lafiya da malaman makarantu. To shin, ta ina ne sabon gwamna Dr Aled Otti zai fara?. Ba lalle ne ba magoya baya su fuskanci bukatar a dagawa wadannan sabbin gwamnoni kafa zuwa nan da wani lokaci ba! Idan gagaga kawai sabbin gwamnonin ake so su farwa dukiyoyin jihohin nasu ba tare da cikakken tsari, nazari da ingantaccen shiri a kasa ba, bisa shawarwari daga masana, labudda, kwa6ar da za a sake lafkawa sai ta kere irin wadda aka gada.
Binciken wasu masana na yin nuni da cewa, irin wadancan gwamnoni sabbin jini, za su dandana kudarsu ne wajen fuskantar tarin ma’aikata wadanda gwamnonin da suka gada su ka yi biris da su tsawon lokaci, ba tare da sun ba su albashinsu na wata wata ba. Ga wani mummunan lodi ko a ce wani tarago makare da “yan fansho jigum jigum, hakkunansu sun yi 6atan dabo cikin aljihunan wasu tsoffin gwamnoni.
Daga lokacin kuma, kallo ya koma sama ne nan take! Ma’ana, lodi ya koma bisa doron wuyayen sabbin gwamnoni ne. Daga nan ma za a cigaba da jin muryoyi ko sautukan tarin kungiyoyin “yan fansho da ake da su a cikin sakuna da lungu na wannan Kasa, suna masu cigaba da gumurzun sai an ba su kudadensu.
Bugu da kari, za a iske cewa, irin wadannan kungiyoyi na tsoffin ma’aikata, tuni sun kulla yarjejeniyar bayan fage da da yawan wadannan sabbin gwamnoni, bisa sharadin za su biya su irin wadancan hakkoki nasu da suka nemi dulmiya daga ofisoshin tsoffin gwamnoni, karyar yau daban, ta gobe ma daban.
Sai masu zurfin tunani “yan kalilan daga kunshin tsoffin gwamnonin ne kan taka rawa wajen rage adadin irin wadannan “yan fansho, amma su wa’e kuwa, irin mummunar alakar da ke a tsakaninsu da “yan fanshon ko kare ba shi ci! Sau nawa ne mai karatu zai ji wani tsoho dan fansho ya yanke jiki a layin kar6ar kudin fansho ko wajen wata zanga zangar fansho ya ya ce ga garinku? Ko ka san wani dan fanshon akwai sama da rayuka 30 a karkashin ciyarwarsa?
Amma don rashin imani na wasu maketatan gwamnonin, sai a kusan shafe shekara dan fansho bai ji sautin alat ba! Dan alat din ma da suke ji daga lokaci zuwa lokaci sai an yi masa dungulmi, a na nufin fince!
A wasu jihohin ma kuwa, sabbin gwamnonin, za su daura damarar cin karo ne da ma’aikatan da tsoffin gwamnoni suka ki sahale musu mafi karancin albashin da tuni gwamnatin taraiya ta jima da tabbatarwa da ma’aikata a duk fadin kasa. Duk inda za a je a zo, sai a ga cewa, cikin duk wani batun kudade ne ake samun lam’a da wasu daga cikin irin wadancan gwamnoni masu barin gado.
Cin Bashin Gwamnoni: Ba Matsala Ba ne Kuma Matsala Ne!
Daga sabon shugaban kasa zuwa sabbin gwamnoni da aka zaba a wannan Shekarar Zabe ta 2023, kusan kowannensu zai dandana kudarsa ne ta fuskacin tarago tarago na basuka da suka gada daga magabatansu.
Shi bashi a kankin kansa ba matsala ba ne. Da wuya ne a yau cikin fadin Duniya a ce ga wata kasa daya tilo da ta fi karfin cin bashi a cikin gida ko a cikin mu’amalolinta na kasa da kasa. Inda gizo ke yin sakar shi ne, shin, me aka yi da irin wadancan madudan kudade da aka ciwo bashinsu?. Ran 30 ga Watan Satumbar Shekarar 2022, ofishin kula da hada hadar bashi ta kasa, ya yi wani tsokaci game da basukan gida da na ketare da ake bin wannan Kasa kamar haka;
1- Bashin gida, a na bin kasar zunzurutun kudi har kimanin naira tiriliyan 21, da miliyan dubu 551 da miliyan 924 da dubu 507 da naira 448 (N 21, 551, 924, 507, 448..). Sannan.
2- Bashin ketare kuwa, a na bin wannan kasa kimanin dalar Amurka biliyan 39 da miliyan 66 ($ 39,66b). Wannan fa wata kididdiga ce ta watanni 6 da suka gabata, yaya lissafin cin bashin yake a yau (March, 2023)?
Da fatan mai karatu na sane da cewa, shi fa bashin da gwamnati ka ciyo, ba wai kawai zuwa ake yi ne a gine kudin kacokan ne ba. Ma’ana, irin wadannan kudade, a na so ne a tsunduma su cikin wata sabgar da za ta rika haihuwa a hankali a hankali ta mayar da kudaden da aka ranto, har ma a ci riba daga bisani. Misali, sarrafa kudaden cikin sha’anin sufuri da makamantansu.
A na kaddara Kasar Amurka a matsayin wata kasa da ta yi wa kowace kasa cikin wannan Duniya fintinkau a fannin karfin tattalin arziki. To amma sau nawa ne za a ji masana tattalin arzikin na yin ishara da cewa Amurkan ta fi kowace kasa hadiyar bashi a duk fadin Duniya?.
Ba Amurka kadai ba, da daman kasashe a nahiyoyin Duniya, tattalin arzikinsu ya burinkasa ne ta hanyar ciwo bashi a gida da waje.
Akasin haka ne ake haduwa da shi cikin wannan Kasa tamu ta Najeriya, saboda ru6a66en shugabanci da Kasar ke fuskanta tsawon lokaci!!!. Hakan na daga manyan dalilan da ke aza ayar tambaya bisa makudan biliyoyin kudade da gwamnatocin jihohi da na taraiya ke kan ciyowa a gida da waje da sunan bashi.
Basukan da aka ciwo a jiharku, nawa ne adadinsu? Me yasa ba ka bin lissafin? Adadin aiyuka nawa ne aka yi da kudaden? Daga aiyukan, wadanne ne suka dauki hanyar biyawa kansu basukan?
A Jihar Akwa-Ibom.
An hakkake cewa a cikin jihar ta Akwa-Ibom, gwamna mai barin gado, Udom Emmanuel, zai gadarwa da sabon gwamna, Umo Eno, zunzurutun basuka da aka ciwo a gida da waje. A gida, gwamnatin Udom ta hadiyi bashin naira miliyan dubu 219 da miliyan 617 da dubu 660 da naira 991 da kwabbai (N 219, 617, 660, 991. 63). A ketare kuwa, gwamnatin ta lankwame bashin dalar Amurka miliyan 46 da dubu 569 da dari 647 da kwabbai ($ 46, 569, 647. 22).
A Jihar Benue
A cikin wannan jiha ta Benue, kafin kai wa ga madudan basuka na gida da na waje da sabon gwamna zai gada, za a samu cewa, akwai wani tarago na watanni 8 zuwa 15 da ba a biya mutane albashi ba. Ina batun wani romon dimukradiyya ga mutanen da aka kere shekara sukutun ba a yi musu duban rahama ta fuskacin biyansu hakkokinsu ba? Irin wadannan mutane na Benue, babu shakka sabon gwamna zai iske su ne cikin mawuyacin yanayi maras kyawo ne, duk wani yare da gwamna zai fuskance su da shi, muddin ba biyansu zai sa a yi ba, kwata kwata ba za su fahimce shi ba. A fili yake cewa, tsoffin gwamnonin sun bar cakwakiya makil a karkashin kasa ga wadanda za su gaje su.