Yayin da bahaushe ya ce don lada ake sallah daya daga cikin manyan masu daukar nauyi a masana’antar Kannywood, Abdulrahman Muhammad wanda akafi sani da Abdul Amart ko kuma Abdul Mai Kwashewa ya ce dangane da shiri mai dogon zango da yake daukar nauyi a halin yanzu na Manyan Mata, ya na yi ne kawai saboda akwai wani sako da yake son isarwa ba wai don dan abinda zai samu ba.
Andul yayin da yake hira da gidan talabijin na Rfi Hausa ya ce babban abin da ya janyo hankalin shi wajen shirya wannan fim shi ne domin ya isar da wani sako ta wannan hanya da Allah ya hore masa sani akai, a matsayinmu na masu fadakarwa ga al’umma to dole ne mu tabbatar da cewar mun tsayu a kan wannan hanya ba wai mu canza manufarmu zuwa wani abin ba in ji shi.
- Tun Kafin A Samu Masana’antar Kannywood Nake Harkar Fim – Lilisco
- Ana Yi Wa ‘Yan Fim Kallon Malamai A Zamanin Baya -Ali Rabi’u Ali
Saboda haka sai na zauna ma duba minene yake damuwar wannan yanki namu na Arewacin Nijeriya, hakan ya sa na zauna da manyan marubuta da sauran masu ruwa da tsaki wajen hada karfi da karfe domin aiwatar da wannan shiri ya ci gaba da cewa.
Da yake amsa tambaya a kan ko akwai wani banbanci da aka samu a yanzu a wannan harka ta shirin fim duba da cewar yanzu komai ya koma a yanar gizo ba kamar a wancan lokacin da ake shirya fim a fitar da fayafayen ce akai kasuwa ba, Abdul ya ce duk da cewar yanzu da sulen bature ake samun kudi amma ko alama ba za a hada samun yanzu da na lokacin baya ba.
A lokacin baya da muke saka fina finanmu a faifan cd tun kafin ka kammala shirinka wani dan kasuwa zai zo maka da kudi a jaka ku yi ciniki ka siyar masa ka samu ribarka, amma yanzu sai ka dage da tallata fina finanka sannan ka dora a shafukan yanar gizo kafin ka samu ka fita da fitarka ba kamar a wancan lokacin da idan ka fitar da faya fayen CD na shirinka matukar ya na da kyau cikin lokaci za ka mayar da kudinka har ka lissfa riba ba.
Dangane da yadda a yanzu suke kalubalantar gwamnatin da a wancan lokacin su ne suka tallata ta, Abdul yace matukar ka na da hankali kuma kai dan kasa nagari ne dole ne ka nunawa gwamnati kuskurenta ko da kuwa a cikinta kake, idan ka lura a yanzu duk wani wanda yake cikin wannan masana’antar ta Kannywood kuma muka tallata wannan gwamnatin tare da shi ba yada kwarin gwiwar da yake da shi a baya.
Saboda idan ka yi wani posting a kan yan siyasa a yanzu wadanda za su zage ka sun fi wadanda za su yaba maka yawa, saboda haka ni a halin yanzu bani da wata jam’iyar siyasa da nike a cikinta kawai dai ni dan kasa ne kuma har gobe ni dan siyasa ne domin kuwa na taso na iske ana yin siyasa a gidanmu kuma a siyasa na samu kudin da na fara daukar nauyin shirin fim a masana’antar Kannywood.