Masu karatu assalamu alaikum. Kafin mu shiga sabon darasinmu na yau, kamar yadda muka yi bayani a makon da ya gabata, Manzon Allah (SAW) ya kasance yana son Turare da kamshi mai dadi, kuma yana amfani da duk wani abu mai kamshi, yana kwadaitarwa a kan Turare, yana cewa “a cikin duniyar nan taku, an soyar min da Mata in aure su don halas dina ne sai kuma Turare, an sanya sanyin idanuna kuma a cikin Sallah, ba na nutsuwa sai na tayar da Sallah”.
Yana daga mutuntakarsa (SAW), haninsa da cewa, “Kar a busa abinci sabida kar mutum ya ce an zuba masa Miyau a ciki” da kuma cewa, “kowa ya ci gabansa” amma Malamai sun ce “in abincin duka iri daya ne”, Manzon Allah (SAW) ya yi umurni da yin Asiwaki – wanke baki, don haka, ya hana shiga cikin Masallacinsa in Mutum ya ci Tafarnuwa sai dai in ya dafa ta (ma’ana, Mutum ya kashe warinta).
Manzon Allah (SAW) ya yi horo da wanke gabobi yayin wanka da cuccuda kwarin gabobin hannu, ya yi umurnin aikata dabi’u na halitta wanda haka Allah ya halicci Dan’adam da su, su ne: Kaciya da aske Gashin gaba da Gyaran gashin baki da aske Farata – Kumba da Tsige Gashin hammata da girmama Gashi – ga Mace ko Namiji mai gashi da yawa da barin Furfura amma ba laifi ya mata kunshi ja, da amfani da Turare na ruwa da na Wuta.
Wannan Fasali zai yi magana kan Tsantseni da Gudun Duniya na Annabi (SAW).
Duk da Allah ya yassare wa Manzon Allah (SAW) Duniya amma sai ya nuna babu ruwanshi da ita. Wannan shine gudun Duniya amma ba ka da Dukiya ko abun Duniya amma ka ce ba ka son duniya, wannan ba shi ne gudun Duniya ba.
Malaman Fik’hu na cewa, idan aka rasa gaba to hukuncinta ya fadi. Mutum yana da dukiya amma yana bin Allah yana ayyukan alheri, wannan shi ne gudun Duniya.
Gudun Duniyar Annabi (SAW) ya gabata a karatuttukanmu na baya amma za mu zurfafa cikin karatu sosai yanzun kan gudun Duniyarsa. Ya ishe ka cewa, yadda ya haramta wa kansa abubuwa kuma ya kauda kai a kansu a kan adon Duniya. Allah ya ba shi Duniya baki dayanta, dukka kasashen Larabawa a zamaninsa sai da Allah ya bude masa, Sarakuna duk suka tsorata da shi suka turo masa da dukiya da kudi da Riguna irin na kyautar sarakuna don neman amincewarsa ko kuma don tsoronsa, ya samu Ganima a yake-yaken bude garuruwa amma rigar yakinsa tana can ya bayar da jinginarta wurin Bayahude don neman abincin iyalinsa.
Abin da zai kara nuna maka gudun Duniyar Annabi (SAW) shi ne, addu’arsa inda yake cewa “Allah ka sanya Arzikin ‘ya’yan gidan Annabi Muhammad (SAW) na yanzu ne” Malamai suka yi bayanin Hadisin da cewa, ‘ya’yan gidan Annabi Muhammad (SAW) yana nufin shi kanshi Annabi Muhammad (SAW), sabida Hadisin da ya zo cewa “yana ba wa kowacce daga cikin iyalansa abincin shekara.”
An karbo Hadisi daga Sayyada A’isha ta ce “Manzon Allah (SAW) bai taba Koshi kwanaki Uku a jere ba har ya koma ga Ubangijinsa”. Malamai masu Sharhin Hadisi suka ce, wannan Hadisi Ma’anarshi “Ba kowane lokaci ba”.
A wata ruwaya kuma “Dabino bai ishe mu (Iyalan gidan Annabi) ba har sai da aka yi Fat’hu Khaibara.”
Sayyada A’isha ta ce “Annabi (SAW) ya rasu bai bar Dinari ko guda daya ba, ko a kuya ko rakumi.”
A cikin Hadisin Amiri bin Harisu “Manzon Allah (SAW) bai bar komai ba sai makaminshi da Alfadarinshi da wata gonarsa.”
Daga cikin masu sharhi, akwai wani Daktan Malami da ya yi Littafi mai suna “Manzon Allah (SAW) Miloniya ne sai dai ba ya son dukiyar”, daga cikin littafin ya rubuta cewa, Allah ya bude wa Annabi (SAW) garuruwa, kuma duk Harajin wadannan garuruwa da aka bude ba tare da yaki ba nashi ne da iyalan gidansa da talakawa.
Allah ya ba shi gonakai ban da kanana, yana da guda bakwai wanda Mukairiku ya ba shi, sannan ya bude masa kasar Khaibara da Tadakku. Sayyada Khadijah (RA) ta ce, Allah ba zai tozartaka ba sabida kana zumunci, kana daukar nauyin wanda ba shi da shi kana garar baki, kana taimakon mutum a bisa wani bala’i na gaskiya da ya faru da Mutum. Mai littafi ya ce, wanda ba shi da kudi, ta kaka zai yi wannan abun. Ya kuma kawo cewa, Annabi (SAW) tun yana dan karaminsa ba kasalalle ba ne, yana zuwa kiwon Tumaki a biya shi, kuma ya yi kasuwancin Sayyada Khadijah, kuma ya gaji Rakuma biyar da Baiwa (Ummu Aimana) da Bawa (Shadrana da Dansa), da Takobi a wurin Mahafinsa. Ya gaji gida a wurin mahaifiyarsa. Ya samu gado mai yawa daga matarsa (Sayyada Khadijah). Ya gaji Khumusin Ganima, dukiyar Banun Nazir da dukiyar Tadakku da dukiyar Khaibara duka na Annabi (SAW) ne.
Mukairiku wani Malamin Yahudawa ne a garin Madina, yayin da ya ji labarin yakin Uhud ya karye wa Annabi (SAW), sai ya tattaro Yahudawa ya fada musu gaskiyar cewa, wannan shi ne Annabin Gaskiya da muke jira, in muka bari aka kashe shi ba mu taimake shi ba, Allah ba zai kyale mu ba, Yahudawa suka ki bin gaskiyarshi shi, shi kuma ya tafi ya bar wasiyya, in bai dawo ba, duk dukiyarshi ya ba wa Annabi (SAW).
Annabi (SAW) ya rasu ya bar Takobba 9, rigar yaki guda 7, Kibiyoyi 6, Gidan kwari daya, Garkuwar Mashi 3, Mashi 6, Hular kwano 2, Tamfol daya, Sanda 3, Akushi na shan ruwa/na cin abinci 7, Jakar da yake sanya matajin gashi daya, da Kwalli da Asiwaki da Kwanon awo da Katifa da Gado da Shimfida da Zobe 2 da Alkyabba 2, Rawani 3, da Tutoci 2, Doki 20, Alfadari 5, Jaki 3, Rakumi na hawa 3, Rakuma ta tatsar Nono 45, Akuya 100, Kwarkwarori 7, Bayi 17 ko 43 in ji ibn Jauzi.
Annabi (SAW) ya kasance yana ba wa kowacce daga cikin Iyalinsa abincin shekara, ya yi Hadaya da Rakuma 100 a Hajjin Bankwana, ya yi kyautar Tumakai ba adadi, ya yi kyautar Rakuma 1000, akwai masu kudi daga cikin Sahabbansa da ke ba shi kyauta. Don haka, maganar Annabi ba shi da kudi wani abu ne kuma daban.
Sayyada A’isha tana cewa, “Annabi (SAW) ya rasu amma babu wani abu da Mutum zai ci a cikin dakina, sai dai rabin buhu na Alkama a cikin Rumbuna.” Malamai suka ce, kila Sayyada ta yi magana ne a kan yadda dakinta yake tun da Annabi (SAW) kowacce daga cikin Matansa yana ba ta abincinta ne.
Sayyada A’isha ta ce, Annabi ya fada mata, “Allah ya nemi idan ina so kwarin garin Makkah duka ya zama Zinari, sai na ce, a’a, ni dai ina so wata rana in koshi wata rana in ji Yunwa, amma ina so a ranar da zan ji Yunwa, in yi kankan da kai a gare ka kuma in roke ka, ranar da na koshi kuma, in yi godiya da yabo a gare ka.”
A wani Hadisi kuma, Mala’ikah Jibrilu ya sauka ga Annabi (SAW) sai ya ce masa, “Ubangiji tabaraka wata’ala yana gaisuwa a gare ka sannan yana tambaya, kana so ya sanya wadannan duwarwatsu su zama Zinari su zama tare da kai a duk inda kake, sai Annabi (SAW) ya sunkuyar da kai na dan wani lokaci, sai ya ce, Ya Jibrilu, gidan Duniya, gidan wanda ba shi da gida da dukiya ne a Lahira (in bai nemi Lahira da ita ba). Jibrilu ya ce, Allah ya tabbatar da kai a haka da gaskiyar zance.
Sayyada A’isha ta ce, mu da muke Iyalan gidan Manzon Allah (SAW) amma mukan zama wata daya ba mu kunna wutar girki ba sai dai Dabino da Ruwa.