Sabon rikici ya kunno kai a jam’iyyar APC mai mulki bayan mutum biyu daga cikin kwamitin gudanarwar jam’iyyar ya bukaci sauran mambobin kwamitin su bijirewa shugabancin Sanata Abdullahi Adamu.
BBC ta ce, wata sanarwa da suka fitar jiya Talata, mataimakin shugaban kwamitin shiyyar arewa maso yamma, Salihu Muhammad Lukman da takwaransa na kudu maso yamma, Isaac Kekemeke sun gargadi Sanata Adamu kan yanke hukuncin bai-daya da sunan shugaba kasa, Muhammadu Buhari.
- Ana Bincike Kan Kisan Mutum 3 A Zaben Fidda Gwani Na APC, An Bukaci Soke Zaben Kano
- Zaben Atiku: Muna Jan Kunnen Buhari Da APC Kan Matsalolin NDDC – Samarin APC A Neja-Delta
Jaridun Nijeriya na rawaito cewa an dage taron kwamitin har sau biyu ba tare da bayyana dalili ba ana tsaka da danbarwar siyasa.
Wadannan kananan rigingimun cikin gida na zuwa ne adaidai lokacin da ake dakon mutumin da zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar zai tabbatar a matsayin ɗan takarar shugaban kasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp