Ga dukkan alamu sabon rikicin cikin gidan da ya kunno kai a babbar jam’iyyar adawa ta PDP sanadin zabo Gwamna Okowa a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa a zaben 2023 na barazanar mayar da hannun agogo baya a jam’iyyar.
Dama dai ana ganin tun da aka tsayar da Alhaji Atiku Abubakar a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ta PDP a babban zaben 2023, tsuguno ba ta kare ba a cikin jam’iyyar, musamman ganin cewa yankin kudancin Nijeriya ya so a ba shi takara amma hakan bai yiwu ba.
Wasu na ganin kamar ma jam’iyyar za ta iya samun koma-baya ganin yadda wasu jiga-jigan jam’iyyar ciki har da gwamnoni suke yunkurin sauya sheka.
Hakan bai kara fitowa fili ba sai bayan da Atiku Abubakar ya tsayar da Ifeanyi Okowa a matsayin wanda zai tsaya mataimakinsa.
Hakan ya ta da kura tare da haifar da sabani tsakanin manyan jiga-jigan jam’iyyar, yayin da wasu suka fara kiraye-kirayen a tunbuke shugaban PDP na kasa, Dakta Iyorchia Ayu.
Batun gaskiya sabon rikicin na neman mai da hannun agogo baya a jam’iyyar PDP, inda shi kansa Atiku ya ce PDP ba za ta tarwatse ba, za su dauki matakin shawo kan duk wadanda ke ganin an yi musu ba daidai ba.
Alamu sun nuna ba abin da ke tafiya daidai a jam’iyyar, domin kuwa gwamnoni biyu rak cikin 13 ne suka halarci wurin da kwamitin gudanarwa na jam’iyyar ya kaddamar da tawagar yakin neman zaben gwamnan Jihar Osun.
Akwai rade-radin da ke yawo cewa Atiku na shan maganganu daga gwamnoni na ya ajiye Okowa tare da musanya shi da Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike.
Haka zalika, magoya bayan Wike su ma suna ci gaba da nuna bukatar a sanya Wike idan dai ana son zaman lafiya a cikin jam’iyyar.
Ko a cikin makon nan ma Kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP, ya ce zai je gaban gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike ya roke shi domin ya ci gaba da zama a jam’iyyar, saboda ana tunanin zai bar jam’iyyar.
Shugaban kwamitin Walid Jibrin ne ya bayyana haka, kwanaki uku bayan da Wike ya watsa wa wata tawagar da aka tura masa kasa a ido, ranar Alhamis a Turkiyya.
Wannan rikici dai ya kawo wata babbar baraka ga PDP da kuma Atiku daidai lokacin da ake kokarin fara shirin yakin neman zaben 2023.
Rikicin ya kara muni a ranar Laraba, yayin da manyan makusantan Wike biyu, Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benuwe da tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose suka fito suka ce ba za su goyi bayan takarar Atiku ba.
Yayin da Ortom ya ce har yanzu zuciyarsa ba ta kwanta da goyon bayan Atiku Abubakar ba, Fayose kuwa cewa ya yi Wike ba zai goyi bayan Atiku ba.
An dai tura masa tsohon ministan harkokin ‘yan sanda, Adamu Waziri domin ya gana da shi, amma ya ki yarda ya gan shi.
Duk da yake ‘yan kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP sun rabu dangane da aniyar kwamitin na ziyartar Wike don rarrashinsa, wanda shugaban kwamitin ya ce idan ta kama su durkusa masa ne za su yi. Alhaji Adamu Maina Waziri dan kwamitin amintattun ne, wanda ya ce ba ya goyon bayan haka.
Wasu rahotanni da dama suna bayyana cewa shirun da Wike yake yi tun bayan zaben fitar da gwani, ya damalmala abubuwa ne a jam’iyyar PDP. Rashin jituwar Gwamna Wike da Atiku yana barka PDP a kudancin Nijeriya. Bugu da kari, Wike ya ki bari ya zauna da mutanen Atiku.
Bayanai na nuna cewa Atiku da Okowa na fuskantar barazana a jihohin irinsu Delta, Edo, Akwa Ibom, Bayelsa, Legas, Ogun, Ondo, Anambra da kuma Imo.
Amma a jihohin Ribas, Kuros Riba, Inugu, Abiya, Oyo da Ekiti, ‘ya ‘yan PDP ba su gamsu da Okowa ba. Masana suna ganin hakan zai iya kawo wa PDP cikas.
Amma akwai wata sanarwa daga Kungiyar Matasa ta Ohaneaze (OYC) sun ce Atiku ya ajiye Okowa a kan bukatar kanshi. Sanarwar mai dauke da sa hannun Shugaban, Mazi Nnabuike da Sakatare Kwamared Obinna Achionye sun ce duk wani yunkuri na canja Okowa zai janyo wasu abubuwa.
Kungiyar Inyamurai ta ce yankin kudu maso gabas ba zai taba yarda ya fadi gaba daya ba, tun da ya rasa haifar da dan takarar shugaban kasa a PDP ko a APC.
“Babu Bukatar sauya abin da muka yi tunanin PDP da APC za su kai tikitin takarar shugaban kasa ga yankin kudu maso gabas, amma hakan bai samu ba.
“Duk da wannan an riga an wuce da shi, abin da kadai ya rage mana shi ne zabin Gwamna Ifeanyi Okowa a matsayin abokin takarar Alhaji Atiku Abubakar, ta la’akari da cewa Okowa Inyamuri ne cikakke.
Idan kuwa aka koma cikin jam’iyyar PDP da mukaman da ke cikin jam’iyyar za a ga cewa ‘yan arewa ne suka mamaye manyan mukamai a cikinta. Zaben Atiku matsayin dan takara ya sa a yanzu PDP ta koma hannun ‘yan Arewa.
Atiku dai shi ne dan takarar shugaban kasa daga arewa maso gabas. Shugaban PDP, Iyorchia Ayu dan Arewa ta tsakiya ne. Shugaban dattawa na jam’iyyar, Walid Jibrin dan arewa maso gabas ne.
Mataimakin shugaban, Umar Damagum dan arewa ne, wanda shi ke bayan da umarni idan Ayu ba ya nan.
Yayin da Atiku ya kai wa Wike ziyara bayan kammala zaben fid da gwani, Wike ya tunatar da shi yarjejeniyar da ta ce idan dan arewa ne ya yi nasarar a zaben fid da gwani, to Iyorchia Ayu zai sauka daga shugabancin PDP.
Atiku ya shawarci Wike da cewa su bar wannan batun tukunna a tsakaninsu, ka da su fitar da shi har sai ya shawarci Ayu.
Idan dai ba a manta ba, irin wannan rikicin cikin gida na daga cikin musabbabin faduwar jam’iyyar PDP zabe a 2015.
Yanzu dai ya rage wa shugabannin jam’iyyar da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar su zauna su lalubo hanyar sulhunta ‘ya’yanta don kai wa ga gaci, idan ba haka kuwa suna ji suna gani zaben 2023 ya sake kucce masu a matakin kasa.