Al’ummar Nijeriya na cike da damuwa da kuma tunanin yadda al’amurra za su kasance daga ranar 1 ga watan Janairi ta sabuwar shekarar 2026 da ake sa ran gwamtanin shugaba Bola Ahmed Tinubu za ta fara aiwatar da sabuwar tsarin haraji a sassan ƙasar nan. An ta yawo da raɗe-raɗi kala-kala na yadda zai shafi al’umma musamman masu mu’amala da bankuna da kuma ƴan kasuwa, a kan haka ne kamfanin jaridar LEADERSHIP ta baƙaci Mr Taiwo Adedeji, shugabanbn kwamitin shugaban ƙasa a kan lamarin harajin ya warware mana zare da abawa.
A ranar 3 ga wata Oktoba 2024, Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya miƙa wa majalisar ƙasa wasu sauye-sauye da yake fatan gani an yi a ɓangaren harkokin karɓa da bayar da haraji a ƙasar nan. Sabbin tsarin sun haɗa da ‘Nigerian Taɗ Bill’ da ‘Nigeria Taɗ Administration Bill’ da ‘Joint Reɓenue Board Bill’ da kuma ‘Nigeria Reɓenue Serɓice Bill’. Wannan kwaskwarimar da neman gudanarwa sun zama dole ne musamman ganin wasu daga cikin dokokin harajin da muke amfani da su a sassan ƙasar suna nan ne tun fiye da shekaru 100 da suke wuce kuma ana nan ana amfani dasu har yanzu hakan kuma yana cutar da al’umam da kuma gwamnati.
- Sin Za Ta Gyara Matakan Haraji Kan Kayayyakin Da Ake Shigowa Da Su Daga Amurka
- Dillalan Man Fetur Sun Yi Maraba Da Dakatar Da Harajin Kashi 15 Na Shigo Da Man Cikin Nijeriya
Mista Taiwo Oyedele Shugaban kwamitin kula da sauye-sauye da garambawul a kan tsarin harajin ƙasar ya bayyana cewa, babban ginshiƙin wannan kwaskwarimar ya ta’alaƙa ne domin maganin yadda ake karɓar haraji daga ƴan kasuwa da ma’aikata ba tare da ƙa’ida ba “bayan mutum ya bayar da haraji a kan wasu harkokin da ya gudanar a ƙaramar hukuma, jami’an gwamnatin jihar suna nan suna jiransa haka kuma ma’aikatan gwamatin tarayya suma suna nan suna jiran karɓar nasu. Haka zai tsawwala tsadar kayayyakin da ake magana a kai abin kuma da za a ɗora wa talaka mai amfani da kayan daga ƙarshe. Haka kuma wannan tsarin zai faɗaɗa fagen karɓar harajin musamman daga manyan masu kamfanoni da masu kuɗi waɗanda kafin yanzu sune suka fi kauce wa biyan haraji a cikin ƴan ƙasa.
Mr Taiwo Oyedele, ya yi waɗanna bayanan ne a taron da hukumar gudanarwar jaridar LEADERSHIP ta shirya wa manyan editoci da wasu manyan ma’aikata a sashin kuɗi don ƙara ma’aikatan fahimtar dasu yadda al’amarin sabon tsarin harajin yake, musamman ganin yadda ake yawo da raɗe-raɗi da yaɗa labarai na ƙazon kurege. Ya ce, ba kamar yadda ake raɗe-raɗin cewa, daga ranar 1 ga wata za a rufe wa duk wanda bashi da mamban nan ta TIN ba za a rufe masa asusun banki da kuma cewa, za a ninkawa masu gudanar da harkokin kasuwanci haraji, ya ce maimakon haka masu ƙananan harkokin kasuwanci ne za su samu sauƙin harajijn da gwamnati ke karɓa a wurinsu matuƙar sun yi ragistar harkokin kasuwancin su.
Ya ƙara da cewa, sabon dokar harajin ya tsame ƙananan kamfanoni masu samun ƙasa da Naira miliyan 50 a shekara daga biyan duk wani na’uin haraji.
Bayanin ya kuma nuna cewa, ma’aikatan da ke karɓar albashin da ya gaza naira dubu 800, ba za su biya kowanne nau’in haraji ba, bincike ya nuna cewa kashi 10 ne na ƴan Nijeriya ke samun kuɗin shiga da ya wuce naira dubu 100 a shekara wanda hakan ke nuna cewa, mafi yawan ƴan Nijeriya za su samu sauƙin dakon haraji a sabuwar shekarar da za mu shiga sakamakon sabon tsarin harajin da Bola Tinubnu ya fitar da shi.
Mr Mista Taiwo Oyedele ya kuma bayyana cewa, sabon tsrain harajin zai sauwwaƙewa wasu kayayaki da harkokin da suka shafi masu ƙaramin ƙarfi harajin ƁAT, harkokin sun haɗa da magunguna da kiwon lafiya, kuɗin haya, kayan abinci, ilimi, sufuri, gass, da sauransu wanda hakan zai samarwa masu ƙaramin ƙarfi waɗanda ke kashe fiye da kashi 100 na kuɗaɗen shigansu a kan waɗannan abubuwan domin tafiyar da rayuwarsu.
Taron da ya gudana a Otel din Continetal da ke Abuja ya samu halartar babban mataimakin Shugaban Kamfanin LEADERSHIP Mr Azu Ishiekwene da Babban Daraktan Kamfanin Mr Mu’azu Elezah da sauran manyan ma’aikata. Inda Mr Oyedele ya ƙara haske a kan yadda lamarin zai kasance game da kuɗin haraji da za a ci gaba da cire wa ma’aikata a cikin sabuwar shekara, ya ce, ƙananan ma’aikata za su lura da raguwar kuɗaɗen haraji da za a ringa cire musu a cikin sabon shekara yayin da manyan ma’aikata kuma nasu zai ɗan ƙaru. Hikimar kamar yadda ya bayyana shi ne a rage wa mafiya yawan ƴan Nijjeriya nauyin da ke kan su musamman ganin sune suka yi yawa a cikin al’umma.
Ya kuma yi zargin cewa, da yawa daga cikin masu sukar sabon tsarin harajin basu san cikakken yadda lamarin ba yake ba, ma’ana sun jahilci abin da ke ƙunshe a cikin kundin. Kuma maimakon su natsu domin fahimtar yadda aka tsara sai siyasa da son rai ya rufe musu ido suna suka ba tare la’akari da matsalar da sukar tasu zai haifar ba.
Ya ce, a sabon tsarin kamfanoni za su iya karɓo wasu kaso daga cikin harajin ƁAT da sukiam karɓa haka wani abune da ba a taɓa yi ba a baya. Wannan matakin zai ƙara bunƙasa tattalin arziƙin kamfanoni a Nijeriya. Haka kuma zai ƙarfafa guwiwar masu zuba jari daga ƙasashen waje.
Daga ƙarshe Mr. Taiwo Oyedele ya tabbatar wa da al’umma cewa, sabon tsarin harajin da zai fara aiki a watan Janairu ba wani abin tsoro ba ne, abu ne da zai kare al’ummar mu tare da bunƙasa tattalihn arziƙinsu.














