Sabon Zango: Ya Wajaba Jam’iyyar APC Ta Taimaki Kanta

Kwanci tashi babu wuya a wajen Allah kuma yau da gobe mai sa dan mutum ya fara rarrafe, ya mike har ya yi tata-tata, sannan wataran ya ruga a guje. A ranar 29 ga Mayun 2019 ne wa’adin zangon mulkin Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya ke karewa, wanda hakan ke nuni da cewa, bakin alkami ya riga ya bushe; iyaka abinda gwamnatin ta yi kawo yanzu shi ne iyakar abinda ta yi ko kuma a ce shi ne iyaka abinza ta iya yi.

A cikin wannan lokaci na shekara hudu, idan abin alheri ta yi, to na alherin ta yi kenan; idan kuma abin tsiya ta aikata, to abin tsiyar ta yi kenan. Abin nufi a nan shi ne, babu wani abu da zai dawo ya goge abinda ta riga ta aikata a baya, domin aikin gama ya riga ya gama.

Ta yiwu a bangaren gwamnati da magoya bayanta su kalli zangon mulkin a matsayin an shuka alheri mafi rinjaye, musamman idan su ka yi la’akari da cewa, an sake zaben su a karo na biyu, domin sake yin wani zangon mulkin na shekara hudu. To, sai dai kuma abinda ya fi dacewa gwamnati ta yi la’akari da shi a irin wannan yanyi shi ne, zai iya yiwuwa ta zarce ne ba don tsantsar kwazonta ba, a’a, sai don wasu dalilai daban-daban, cikinsu kuwa watakila har da na dabarin siyasa da lissafinta.

A wasu lokutan, sau da yawa mutane su kan iya cin zabe, ba don sun yi abin arziki ko abin a zo a gani ba, illa sai don wasu dalilai da su ka tilasta wa mutane sake zaben su. Misali a nan shi ne, kamar bangaranci ko wani kuskure na abokin takara, kamar yadda mu ka gani a wasu yankunan kasar nan da ma kasar bakidayanta kan wasu abubuwan. A nan za a iya bada misali da cewa, a fili ta ke cewa, bangaranci ya yi tasiri a zaben da ya gabata, domin yankunan Arewa da na Kudu maso Gabas sun fi bayar da karfi ga jam’iyyar gwamnati mai ci, wato APC, yayin da yankunan Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas su ka fi muhimmintar da babbar jam’iyyar adawa ta kasa, wato PDP.

Bugu da wari, za a iya cewa, ikirarin dan takarar ita babbar jam’iyyar adawa ta kasa, PDP, wato Alhaji Atiku Abubakar, na zai sayar da kamfanin NNPC idan lashe zabe, ya yi tasiri sosai a zukatan yawancin talakawan da a ka haramta wa samun ingantaccen ilimi, inda su ka kasa fahimtar abinda ya ke nufi da hakan, kuma jam’iyya mai ci ta yi ma sa farfaganda kan hakan. Tabbas lamarin za a iya cewa ya kara ma sa bakin jinin da ya rage ma sa yawan kuri’a. Wadannan wasu kananan misalai ne.

Abinda hakan kawai ya ke nunawa shi ne, wani lokacin ba kokarin jam’iyya ke sanya wa ta lashe zabe ba, illa dai wasu dalilai na daban. Tabbas ya zama wajibi ga gwamnatin APC ta yi la’akari da irin hakan, domin an jima a na yiwa PDP irin wannan takarar karatun shekaru da dama kafin ta fadi zaben 2015 har ita APC ta samu damar darewar kan karagar mulkin Najeriya.

Da yawa na ganin cewa, da a ce PDP ta kula da yawancin jan kunnen da a ka rika yi ma ta a baya, to za ta iya shekara 60 din da ta so yi a kan mulkin kasar ba tare da tsinkewa ba, musamman idan a ka dubi tsakanin hakuri da rashin wayewar da a ka dora wa mafi yawan talakawan Najeriya kan batun cigaban tattalin arzikin kasa a zamanance.

Dom haka kada jam’iyyar APC ta dauka cewa, sake lashe zabe a karo na biyu ruwa ta sha kenan, domin saurin zuwa ne da ita. Wannan shekara hudun da a ka fara daga ranar 29 ga Mayu, 2019, tamkar yau ne za a wayi gari a ga wani zaben na 2023 ya zo kuma abin zai zo ne kamar kiftawa da bisimillah.

Saboda haka wajibi ne APC ta zama jam’iyya mai kunnen sauraron jama’a. dukkan guraren da ta yi kurakurai, amma ta yi sa’a a sake zaben ta a haka, to ta yi iyakar bakin kokarinta wajen ganin ta gyara su a aikata kuma a tabbance. Lokacin bayar da uzuri ya riga ya wuce. Idan har ba ta iya aiwatar da abubuwan da su ka kamata ba a wannan sabon zango, to duk wani karfin gwiwa da talaka ya ke da shi a kanta, zai gushe ne, kuma ba za ta gane illar hakan a gare ta ba, sai lokaci ya riga ya kure ma ta.

Dole kowacce jam’iyyar mai mulki ta daina daukar masu tunatar da ita a matsayin makiya. Har gara ma ta dauke su a matsayin ’yan adawar siyasa kawai, domin hakan zai iya taimaka wa jam’iyyar ta gano kurenta, don ta gyara.

Wajibi ne APC ta fahimci cewa, za a zo zaben 2023 ne ba tare da ta na da farin jinin dan takararta na 2019 ba, wato Shugaba Buhari. Wajibi ne ta gane cewa, za ta so ta tsayar da dan takara daga Kudu ne, wato yankin da ba shi ne ya ke da mafi yawan al’ummar kasar ba. Wajibi ne ta gane cewa, shekaru hudunta na farko ’yan Arewa su na kallon su a matsayin ba su ne ke juya akalar gwamnatin ba. Don haka za su so su sake zaben gwamnatin da za ta yi da su matukar a zangon APC na biyu ba ta waiwaye su yadda su ke tsammani ba.

Wajibi ne APC ta fahimci cewa, a lokacin da PDP ta amshi mulkin Najeriya a 1999 ita ma jam’iyya ce wacce a ke kallon ta a matsayin mai ceton al’umma daga hannun mulkin kama-karya na sojoji. Don haka na amshi PDP a Najeriya ne cikin shauki tare da fata da kwarin gwiwar cewa ita ce mafita.

To, amma da PDP ba ta yi abinda dan kasa ya ke kallo a matsayin hanyar da za a bi wajen ceto shi ba, sai ta zama abar tsinuwa da la’anta a wajensa. Ita ma APC ta zo ne a 2015 bisa tsammanin cewa, za ta ceto talaka daga masifar mulkin PDP na shekara 16, amma abin mamaki shi ne ita APC a cikin shekara hudu kacal korafi ya fara yawa. To, kada ta bari ta yi wa kanta kasassabar da ba za ta yi karkon da PDP ta yi ba.

A yanzu ta na da damar da za ta gyara komai na matsalolinta cikin wanna shekara hudun sabuwar fil. Kin yin hakan ba kowa zai yi wa illa ba a siyasance tamkar ita kanta APC din. Shi talaka ba siyasa ce ta dame shi ba; abinda ya fi damun sa shi ne, rayuwarsa ta inganta, ya fita daga halin kaka-ni-ka-yi.

APC ta na da zabi kan hakan; ko dai ta taimaki talaka a sabon zangon nan, ita kuma ya saka ma ta ta hanyar ta yi karko a siyasance, ko kuma ta ki taimakon sa, sai mutuncinta ya zube warwas!

Exit mobile version