• English
  • Business News
Friday, May 16, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sabuwar Hanyar Kwacen Shafin Facebook (I)

by Ibrahim Sabo
2 years ago
in Kimiyya Da Fasahar Sadarwa
0
Sabuwar Hanyar Kwacen Shafin Facebook (I)
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Labarai Masu Nasaba

Wayar Da Kai Kan Barazanar Intanet A Rayuwar Al’umma (CYBER AWARENESS)

Kariya Daga Soyayyar ‘Online’ Da Shagalta A Intanet

A kwanan nan kwacen shafin sada zumunta na Facebook wanda a turance ake kira ‘Hacking’ ya zama ruwan dare, mafi yawan mutane sun rasa ta yaya hakan yake faruwa. To yanzu za mu dan yi bayanin yadda mutum zai kare kansa daga fada wa tarkon wadannan masu kutsen.

Sabuwar hanyar da a yanzu suke amfani da ita shi ne yaudara. Da zarar sun yi nasarar kwace Facebook account na wani, to sai su bi abokansa na Facebook din ta messenger, sai su yi ta tura sako, suna cewa a ka tura musu lambar wayarka, za su baka kyautar data na browsing mai yawan gaske. Wasu 250 GB wasu kuma 500 GB. To da zarar ka ga haka, to wannan mai Facebook account din hackers sun kwace masa Facebook. Idan kuwa ka tura musu, za su ce an turo maka wani code, ka turo mana shi. Kana tura musu, shikenan baka da iko da Facebook account dinka, sun kwace maka shi. Kar ka yadda wani yace ka tura masa lambar wayarka ko email, ka tura masa.

  • Xi Ya Jaddada Bude Wani Sabon Babi Na Ci Gaban Heilongjiang Mai Inganci
  • Shugaban Kasar Zambia Zai Kawo Ziyarar Aiki A Kasar Sin

Mafi yawan mutane idan sun bude shafin Facebook ba sa la’akari da seta wasu abubuwan, musamman wadanda suka shafi layin tsaro kamar boye wasu muhimman sirruka game da mutum kansa.

wasu daga cikin mutane idan sun bude shafin Facebook, sukan yi amfani da makullan sirri mafi sauki ta yadda ba za su taba mantawa ba, mafi rinjaye daga cikin su, suna amfani da lambobin wayarsu lambar kuma wanda suka riga suka yi rijista wajen bude shafin Facebook din da shi.

Shin laifi ne amfani da lambar waya a matsayin makullin sirri ‘password’?  A’a ba laifi ba ne amma akwai bukatar boye lambar wayar daga masu bude ko bincika shafin ‘profile’ din mutane don ganin sirrukansu ko samun lambobin su.

Yana da matukar muhimmanci mu san cewa masu kutse cikin shafin mutane na Facebook, mafi yawa daga cikin su ta hanya mafi sauki suke iya shiga, shi ne rashin tsaro da kuma rashin ba da muhimmancin da muke yi wa shafin na Facebook. Daga mun fara amfani da shafin muna ‘chatting’ shikenan bamu damu da kulawa ba.

Abubuwan da ya kamata mu kiyaye sun hada da boye sirrukan mu masu muhimmanci irin su lambar waya, Email, shekarun haihuwa (Date of Birth) da sauransu, kuma muke yawan kara saka masa tsaro musamman akwai abubuwan da ake kira code generator, two factors authentication da sauransu.

Ya kamata kuma kasan ‘where you’re logged in’ ko da za ka sayar da wayar ka to ka tabbatar ka sauke shafinka na Facebook daga cikin wayar. Wato za ka yi ‘log out’ kenan. Sannan yana da kyau idan za ka canza waya ka goge dukkan abin da ke kan wayar ta hanyar shiga setting na kan wayar, sai ka shiga ‘factory data reset’.

Mutane da dama suna yawan kuka da yadda ake kwace musu shafinsu na Facebook, alhali shafin yana da muhimmanci a wurin su, wasu na da abokai makusanta da wadanda ke nesa, kamar kasashen waje, kuma ta wannan sahar Facebook din ce kadai suke haduwa, wasu kuwa sun shahara da shafinsu na Facebook din, ma’ana suna da mabiya da yawa wanda lalacewar shafin kan iya haifar musu da matsala ta rashin dawo da wasu cikin mabiyan nasu, ko wani al’amari na siyasa ko kasuwanci da suke tallata wa ta shafin nasu na Facebook.

Sau da yawan lokuta mutane sukan bude shafin Facebook  haka kawai ba tare da bin matakai na Facebook din ba, daga sun bude shafin Facebook din, sukan fara amfani da shi ne kai tsaye ba tare da tunanin seta wasu abubuwa da zai saukaka musu amfani da Facebook din ba, ko kuma kakaba wa shafin tsaro mai yawa domin kiyaye lafiyar shafin Facebook din daga baragurbin mafarauta (Hackers).

Daga lokacin da mutum ya bar shafinsa na Facebook haka kawai ba tare da tsaro ba, ta hanya mai sauki za a iya kutsawa a bata masa shafin na sa, ko a maka kwacen shafin Facebook gabadaya, sai dai ka ga ana saka abubuwa a shafin na ka kai kuma baka sani ba, ko kuma ka ga an tura sakon rokon kudi a wajen jama’a har da wadanda kake jin kunya da ganin girmansu.

Lokacin da aka kwace wa mutum shafinsa na Facebook, abu na farko da suke yi shi ne canza wa mutum makullin sirri ‘password’ sannan su shiga su canza duk wata hanya ko kafar da za a iya bi don dawo da shafin, bayan nan sai su goge duk wani rubutu ko hoto da ke cikin shafin Facebook din (amma idan sun ga dama, domin ba kowane a cikinsu ke yin hakan ba), canza wa mutum hoton dake a kan ‘Profile’ dinsa shi ne abu na karshe da suke bayan sun canza wa mutum suna.

Idan har sun goge lambar wayarka da email, to hakan yakan ba da wahala sosai wajen dawo da shafin Facebook din, domin kuwa sun toshe saukakan hanyoyin da za a bi don a kwato Facebook account din. Ko da an yi nasarar kwato shafin na ka, to wasu abubuwan ma basa dawowa, sai dai daga karshe ka ji mutum yana cewa ba ya  jin dadin shafin na sa na Facebook din.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Shirin Tinubu Na Samar Da Tabarau Miliyan Biyar Ga Masu Fama Da Ciwon Ido

Next Post

Yadda Bullar Cutar Gansakuka Ta Sa Manoman Citta Tafka Mummunar Asara A Kaduna

Related

Wayar Da Kai Kan Barazanar Intanet A Rayuwar Al’umma (CYBER AWARENESS)
Kimiyya Da Fasahar Sadarwa

Wayar Da Kai Kan Barazanar Intanet A Rayuwar Al’umma (CYBER AWARENESS)

4 weeks ago
Kariya Daga Soyayyar ‘Online’ Da Shagalta A Intanet
Kimiyya Da Fasahar Sadarwa

Kariya Daga Soyayyar ‘Online’ Da Shagalta A Intanet

2 months ago
Hanyoyin Kare Kanka Daga Damfara Ta Intanet
Kimiyya Da Fasahar Sadarwa

Hanyoyin Kare Kanka Daga Damfara Ta Intanet

3 months ago
Yadda Za A Kare Yara Daga Barazanar Intanet
Kimiyya Da Fasahar Sadarwa

Yadda Za A Kare Yara Daga Barazanar Intanet

3 months ago
Mantuwa Na Matukar Taimakon Rayuwar Mutane – Masani
Kimiyya Da Fasahar Sadarwa

Mantuwa Na Matukar Taimakon Rayuwar Mutane – Masani

7 months ago
Yadda Na Kirkiro ‘Brain-chip’ Da Ke Dawo Wa Wadanda Aka Haifa Da Makanta Ganinsu – Elon Musk
Kimiyya Da Fasahar Sadarwa

Yadda Na Kirkiro ‘Brain-chip’ Da Ke Dawo Wa Wadanda Aka Haifa Da Makanta Ganinsu – Elon Musk

7 months ago
Next Post
Kalubalen Da Manoman Shinkafa Ke Fuskanta A Kano

Yadda Bullar Cutar Gansakuka Ta Sa Manoman Citta Tafka Mummunar Asara A Kaduna

LABARAI MASU NASABA

Masu Garkuwa Sun Nemi Miliyan ₦30 Don Sako Shugaban APC A Ondo

Masu Garkuwa Sun Nemi Miliyan ₦30 Don Sako Shugaban APC A Ondo

May 16, 2025
Dalilin Tsame Daya Cikin Uku Na Ma’aikatan Ƙasar Nan A Tsarin Sauye-sauyen Biyan Haraji – Czar

Dalilin Tsame Daya Cikin Uku Na Ma’aikatan Ƙasar Nan A Tsarin Sauye-sauyen Biyan Haraji – Czar

May 16, 2025
Abubuwan Da Aka Haramta Wa Mahajjaci

Abubuwan Da Aka Haramta Wa Mahajjaci

May 16, 2025
Tinubu Ya Kira Taron Manyan Kafafen Yada Labarai Kan Samar Da Wadataccen Abinci

Tinubu Ya Kira Taron Manyan Kafafen Yada Labarai Kan Samar Da Wadataccen Abinci

May 16, 2025
Abin  Da Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (1)

Abin  Da Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (1)

May 16, 2025
Rashin Tsaro Da Raba Wa Manoma Kayan Aiki Kan Lokaci Na Baraza Ga Wadata Kasa Da Abinci

Rashin Tsaro Da Raba Wa Manoma Kayan Aiki Kan Lokaci Na Baraza Ga Wadata Kasa Da Abinci

May 16, 2025
Kasar Sin Ta Yanke Shawarar Hana Taiwan Halartar Babban Taron WHO Na Bana

Kasar Sin Ta Yanke Shawarar Hana Taiwan Halartar Babban Taron WHO Na Bana

May 15, 2025
Faɗuwar Farashi: Masu Ɓoye Abinci Don Ya Yi Tsada, Asara Kawai Suke Ƙirgawa , In Ji BUA

Faɗuwar Farashi: Masu Ɓoye Abinci Don Ya Yi Tsada, Asara Kawai Suke Ƙirgawa , In Ji BUA

May 15, 2025
Sin Ta Bukaci Amurka Ta Dakatar Da Harajin Sashe Na 232

Sin Ta Bukaci Amurka Ta Dakatar Da Harajin Sashe Na 232

May 15, 2025
Xi Ya Taya Shugaban Togo Murnar Karbar Ragamar Shugabanci

Xi Ya Taya Shugaban Togo Murnar Karbar Ragamar Shugabanci

May 15, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.