Rahotonnin da su ka zo ma na a jiya na bayyana yadda wasu matasa su ka sake fitowa zanga-zangar #EndSARS a jihohin Legas, Osun da kuma Ibadan, inda su ke bayyana bukatunsu mabambanta.
Wasu matasa a ranar Litinin da su ke da alaka da kungiyar #EndSARS Moverment sun sake fitowa kan titi domin gudanar da zanga-zangar zargin rashin kyakkyawar shugabanci a Osogbo babban birnin jihar Osun.
Masu zanga-zangar da suka fara haduwa a kan layin Ogo-Oluwa daga baya sun yi jerin gwano zuwa majalisar dokokin jihar Osun da ke kusa da sakatariyar jihar a Abere.
Matasan, wadanda suka samu jagorancin Emmanuel Adebisi, su na masu bukatar kyakkyawar shugabanci, bukatar neman a sake wadanda aka kama yayin zanga-zangar EndSARS da aka gudanar a kwanakin baya wanda ya juya zuwa tashin-tashi.
Kakakin majalisar dokokin jihar Osun, Hon. Timothy Owoeye ya shaida wa masu zanga-zangar da su kasance masu hakuri su kara wa gwamnati uzuri domin ta samu damar sauraron dukkanin bukatunsu.
Matasan wadanda suka dace kan cewa sun fito ne domin neman kyakkyawar shugabanci, sun sha alwashin cewa ba zanga-zanga ce ta tashin hankali ba, sun fito ne cikin lumana domin neman a biya musu bukatunsu, kana sun nuni da cewa basu da alaka da siyasa.
Har-ila-yau, dukka a jiyan, masu zanga-zangar EndSARS sun sun kuma fito kan tituna a jihar Legas da Ibadan babban birnin jihar Oyo.
Masu zanga-zangar wadanda suka koma kan gadar Lekki Toll Plaza inda aka zargi sojoji da bude wa masu zanga-zangar wuta a kwanakin baya.
Jami’an ‘yan sanda da soji sun kasance a yayin zanga-zangar domin tabbatar da masu yinta basu karya doka da oda ba.
Sai dai a bangaren jami’an tsaro, ‘yan sanda sun yi gargadin cewa dukkanin dukkanin wani da ya kara fitowa zanga-zangar nan duk abun da ya sameshi shine ya jawo wa kansa.