Assalamu alaikum wa rahmtullahi ta’ala wa barkatuh. Masu karatu da ke biya da mu barkan mu da sake saduwa a wannan makon cikin shafinmu na Dausayin Musulunci.
Yau karatunmu zai juya akala ne zuwa ambaton wasu daga cikin Sadaukantaka da karfin rai (Taimako) na Manzon Allah (SAW), sadaukantaka ita ce karfin rinjaye amma hankalin jarimin ya fi rinjaye a kan sadaukantar. Ya zo daga Hadisin Annabi (SAW) yana cewa “Sadauki shi ne wanda yake mallakar zuciyarsa yayin da ya yi fushi ba wanda ke bubbuge mutane ba yayin da ya yi fushi.”
- Xi Ya Yi Jawabi Ga Taron COP14 Kan Kiyaye Filaye Masu Dausayi
- LEADERSHIP Ta Jinjina Wa Shehu Isma’ila Mai Diwani Kan Shafin Dausayin Musulunci
Ma’anar karfin rai kuwa, ita ce taimako yayin da wanda za a taimakan, mai taimakon zai iya rasa ransa a wurin taimakon.
Manzon Allah (SAW) ya tsaya wurin da babu wanda zai jahilci sadaukantakarsa. Ya halarci yakoki da yawa wanda a cikinsu sadaukai suke guduwa su bar shi a filin yakin, ba ya gushewa a filin yaki ballantana ya ja da baya sai dai a ce “…illa mutaharrifan likitalin au mutahayyizan ila fi’atin – Ma’ana wanda ya sauya wurin yaki ya koma cikin tawagarsu ko kuma ya juya don sauya fasalin yaki, wannan ba guduwa ba ne daga filin yaki”. Babu wani sadauki face ya bar tarihin guduwa a yaki wata rana amma Annabi (SAW) ba a taba kirga masa guduwa a filin yaki ba.
An ruwato hadisi daga Sahabin Annabi (SAW), Barra’u ana tambayarsa cewa “Da gaske kun gudu kun bar Annabi (SAW) a ranar yakin Hunaini? Sai Barra’u ya ce, amma dai shi Annabi (SAW) bai gudu ba, sannan ya ce hakika na ga Annabi (SAW) akan alfadararsa Fara da Abu Sufyan bin Haris bin Abdulmuzallib (zan’uwan Annabi SAW ne) yana rike da wurin sa kafa a shimfizar alfadarin sannan kuma Ammun Nabiyy Abbas bin Muzzalibi yana rike da linzamin alfadarin, shi kuma Annabi (SAW) yana cewa “Ni ne Annabin nan, ba karya ba” a wata ruwaya kuma “ Ni ne zan Abdul Muzallibi” Ana cewa ba a taba ganin Annabi (SAW) ya yi yaki sama da na wannan rana ba.
Annabi (SAW) yana da Alfadarai Bakwai, akwai wazanda ya rike har ya rasu suna wurinsa akwai kuma wazanda ya bai wa wasu daga cikin sahabbansa. Wacce ya je yakin Hunaini da ita, wani sarkin Larabawa (zan makafatul kinani) ne ya bashi, akwai wacce sarkin Ailatu ya bashi akwai ta sarkin Limatul Jandali, akwai ta Sarki Najjashi, akwai ta sarkin Kisra, akwai ta sarkin Mukaukisu akwai Jindilu. Jindilu itace mashhuriya wacce Annabi ya rasu ya bar ta Sayyidina Aliyu ya ci gaba da hawanta, duk yakukuwan Sayyidina Ali, mafi yawancinsu a kanta ya yi, ranar yakin Wak’atu Jamal, Sayyada A’isha (RA) ta ganshi a kanta, sai ta ce “ya yi kama da zan’uwansa” sai mai rike da akalar rakuminta ya jefar ya koma cikin rundunar Sayyadina Ali ya ce masa, Sayyada tace “ka yi kama da zan’uwanka (Sayyadina Rasulallah).
Imam Muslim ya ruwaito Hadisi daga Abbas yana cewa “yayin da tawagar Musulmai da Kafirai suka hazu, sai Musulmai suka gudu suka juya baya, sai Manzon Allah shi kuma ya kasance yana jan alfadarinsa inda Kafiran suke, ni kuma ina rike da linzamin alfadarinsa ina jan linzamin baya shi kuma Abu Sufyan zan Haris zan Abdulmuzallib yana rike da wurin sanya kafafuwa na shimfizar alfadarin, sannan Annabi (SAW) ya yi kira ga Musulmai suka dawo.” A wata ruwaya kuma, Annabi (SAW), Baffansa Abbas ya sa ya kira Musulmai.
Annabi (SAW) ya kasance idan ya yi fushi (shi kuma ba ya fushi sai in an taba Allah), to wani abu bai iya tare shi, ko Sahabi ko tsoro ko wata razana.
Abdullahi zan Umar ya ce, “ban taba ganin wani abu mafi sadaukantaka ko karfin zuciya ko kyauta mafi yarda wanda ya fi Annabi (SAW) ba.”
Sayyadina Ali yana cewa “Mun kasance in yaki ya yi zafi, ya yi tsanani idanuwa suka sauya kala suka yi ja, sai mu dinga kare kanmu da Annabi (SAW), babu wani da yake kusantar makiya sai shi, sannan mu biyo bayansa.
An karbo Hadisi daga Anas yana cewa “Manzon Allah (SAW) ya kasance mafi kyawun Mutane, mafi kyautar mutane, mafi sadaukantakar mutane.”
Wata rana da dare mutanen Madina sun razana sabida kara mai karfi da aka ji ta taso a daren, Sahabbai suka fara bi gida-gida suna taso abokansu a je a duba sabida a san me ke faruwa. Kawai sai suka hazu da Manzon Allah (SAW) yana dawowa, ya riga su zuwa wurin, sabida sauri a dokin Abi Dalhata ya je kuma babu shimfiza a kan dokin, yana rataye da takobi yana cewa Sahabbai “kar ku tsorata, na je na gani babu komai.”
A wannan lokaci Madina ta kasance kullum ana tsoron wani daga cikin Sarakunan makiya zai kawo hari.
Imran bin Hussaini yake cewa, Manzon Allah (SAW) bai taba hazuwa da wata runduna ba sai ya kasance na farko wanda zai fara kai musu hari.
Yayin da Ubayyu bin Khalaf ya ga Annabi (SAW) a ranar yakin Uhudu, Ubayyu ya fito yana cewa, Ina Muhammadu yau sai zaya ya mutu a cikinmu, ko ni ko shi. Ubayyu yana daga cikin wazanda suka fanshi kansu a ranar yakin Badr, bayan ya fanshi kanshi sai ya ce wa Annabi (SAW), yana da doki da ya kulle kullum yana bashi masaki na dawa, a kansa zan kashe ka, sai Manzon Allah (SAW) ya ce masa, Insha Allah, ni ne zan kashe ka a kanshi. A ranar yakin Uhudu da Ubayyu ya ga Annabi (SAW), sai ya sukwano dokinshi zuwa ga Annabi (SAW), Mazaje sadaukai suka yi kanshi sai (SAW) ya ce musu “ku kyale shi haka nake so”. Sai Manzon Allah (SAW) ya karbi wani mashi a hannun wani sahabi sannan ya soke shi a wuya daga kan dokinshi, sai ya koma yana ce wa kuraishawa, Muhammadu ya kashe ni, an ruwaito cewa, Ubayyu ya Mutu a hanyar dawowarsa daga Uhudu zuwa Makkah.
Kunya Da Kawar Da Kai Na Manzon Allah (SAW)
Wannan kazan kenan daga cikin sadaukantaka irin ta Annabi (SAW), yanzun kuma za mu juya akalar karatunmu zuwa ambaton wasu daga cikin halayen Kunya da kawar da kai na Manzon Allah (SAW).
Abin da ake nufi da kunya shi ne taushin zuciya da yake bijirowa a fuskar zan Adam yayin da mutum ya aikata wani aiki ko ya faza wata magana da ake kin ji ko gani, ko kuma mutum ya aika ta abin da rashin aikata shi ya fi, sai zan Adam ya ce “ina ma na bari ban aikata ba.”
Shi kuma runtse ido ko kawar da kai, yana nufin rafkana da abin da mutum ba ya so a aikata masa (ba ya so a aikata masa wani abu, ga kuma wani ya nace sai ya aikata abin da ba a son) shi kuma sai ya kawar da kai ya nuna bai san ma ana yi ba.
Manzon Allah (SAW) ya fi kowa Kunya sabida Hadisin “Alhaya’u minal Iman… – Kunya tana daga cikin Imani”.
Manzon Allah (SAW) yana cewa, “wanda bai da kunya, ya aikata abin da ya ga dama, Allah ba ruwanshi da shi”. Annabi (SAW) shi ne mafi kawar da kai ga Al’aurar Mutane.
Ubangiji tabaraka wata’ala ya faza cikin kur’ani “Ya ayyuhallazina amanu la tadkhulu buyutan nabiyya illa an yu’uzana lakum ila za’amin gaira nazirina inahu…”