Connect with us

WASANNI

Sadio Mane: Daga Malamin Makaranta Zuwa Dan Kwallo

Published

on

Saido Mane bai dauki lambar yabo ba a shekarar 2015, amma lokacin da dan wasan mai buga wasa a Liberpool a yanzu ya ci kwallaye uku a cikin dakika 176 a lokacin da yana Southampton a  karawar da suka doke Aston Billa 6-1 a cikin watan Afirilun shekara ta 2015 ya sa ya kafa tarihi a gasar firimiya da za a dade ba’a manta da shi ba.

Tarihin da ya karya na cin kwallaye uku a karancin lokaci an kafa shi ne a shekarar 1994 kuma tsohon dan wasan tawagar Ingila da Liberpool ne ya kafa shi.

Kuma kwallaye ukun da ya ci ya sa hankulan masoya kwallon kafa na duniya ya karkata wajensa, wanda hakan ya sa ake ta jinjina wa dan kwallon kafar Senegal, wanda ya zama daya daga cikin ‘yan wasan firimiya da suke da hadari a wasanni.

Dan kwallon mai shekaru 26, ya je gasar firimiya ne da tagomashinsa bayan da ya isa filin wasa na St Mary kan kudi da ya kai $12m a watan Satumbar 2014 daga Red Bull Salzburg kungiyar da ya lashe gasar kasar Australia sau biyu kafin daga baya kuma Liberpool ta siyeshi akan kudi fam miliyan 35.

Koda yake gasar Australia ba ta kai ta daraja da wahala ba, saboda haka ana kila wakala kan kwarewarsa a fagen kwallo har said a ya nunawa duniya cewa zai iya abinda ake zato.

Yayin da kwallaye ukun da ya ci a karanci lokaci ta jawo hankulan ‘yan jaridu a labaransu, ya kuma haskaka a karawar da suka yi da Chelsea a cikin watan Oktoba na shekara ta 2015 a inda ya ci kwallo ya kuma bayar da wacce aka zura a raga a wasan da suka ci 3-1 a firimiya ya kara haskaka kwazon dan wasan.

Mane wanda zai iya buga gurbin mai cin kwallo da kuma iya wasa a dukkan inda aka saka shi a gaba, shi ne dan kwallon da a halin yanzu kasar Senegal take alfahari dashi bama kasarsa ta haihuwa ba har nahiyar Africa

Hakan kuma nasara ce ga dan wasan duba da yadda yanzu duniya take kallonsa a matsayin wani dan wasa wanda babu kamarsa a kungiyar Liberpool idan aka cire Muhammad Salah wanda shima dan Africa ne.

Jumulla kwallaye 23 da ya ci ya taimakawa Liberpool  samun gurbin buga gasar cin kofin zakarun Turai wato Eufa Champions League bayan da suka buga wasan karshe kuma sukasha kashi a hannun Real Madrid daci 3-1 a watan Mayun daya gabata.

Ya kware wajen taka kwallo da iya tafiya da ita a kafarsa da tunkarar dan wasan baya kai tsaye wanda hakan ne ya sa Manchester United ta yi zawarcinsa duk da cewar Liberpool ce tasamu nasarra daukarsa.

Wasannin da ya taka a kungiyarsa ya bai wa dan kwallon tabbacin shiga cikin ‘yan takarar kyautar dan kwallon kafa na Afirka da BBC za ta karrama a karon farko, wanda ba za a manta rawar da ya taka a gasar kofin duniya a shekarar nan ba.

Duk da cewa kasar Senegal batayi kokari ba domin bata samu damar fitowa daga cikin rukuni ba amma kuma dan wasan ya buga abin azo agani kuma ya buga abinda daman akayi tunanin zai buga tunda daman yayi kokari a Liberpool tunda har wasan karshe nacin kofin zakarun turai yaje kuma ya zura kwallo a wasan duk da cewa sune sukayi rashin nasara.

Bai zama abin mamaki ba da Liberpool  tayi sha’awar daukar Sadio Mane bisa kwarewa da yake da ita Ba wai gudu da  iya tafiya da kwallo ne makaminsa a fili ba har da sarrafa kwallo da kuma dabara kala-kala, wanda kocin Liberpool yace bai taba aiki da dan wasan Africa daya iya kwallo ba kamar Mane.

Mafarkin kociya bai wuce yadda dan kwallon ke iya buga gurbin mai cin kwallo da kuma dabarar zura kwallaye a raga da kuma taimakawa a ci da kuma raba kwallaye ga abokan wasansa.

Tsawon dan wasan bai wuce kafa biyar da inci takwas ba kuma bashi da nauyi, amma ya zama dan wasan firimiya da ake fargabar a hadu dashi a wasa kuma yana taimakawa matasan ‘yan wasan Liberpool.

Dan kwallon ya yi kaurin suna wajen saka ‘yan kallon Liberpool  su mikewa daga kujerar da suke zaune suna sowa dama tsohon dan kwallon firimiya Matt Kenny Delglish da wajen da attajirai ke zama da hakan ya dace ya zama gwarzon dan wasan Afirka da BBC za ta karrama a bana

 

  • Iyayensa Sun So Ya Zama Malamin Makaranta

Lokacin da Mane yafara buga kwallon kafa a kauyensu mai suna Seidio dake kudancin kasar Senegal a ranar 10 ga watan Aprilun shekara ta 1992 sannan yafara buga kwallo a karamar kungiyar dake kauyensu.

Bayan dan wasan ya girma ne sai soyayyar kwallon kafa ta shiga zuciyarsa kuma yaga zai iya bugawa hakan yasa ya daina zuwa makaranta da kowanne waje kuma ya mayar da hankali wajen ganin yasamu daukaka a kwallon kafa.

Sai dai iyayen Mane basu yarda da kwallon dayake yi ba a wannan lokaci inda suka gwammace yayi irin abinda ragowar mutanen kauyen sukeyi wato yayi karatu domin yazama malamin makaranta.

Hakan yasa dan wasan ya bazama babban birnin kasar kuma daga baya iyayensa sukaji labara sukaje suka sake dawo dashi kauyen domin a cewarsu yana bata lokacinsa ne kawai domin bazai iya zama dan kwallo ba.

“Na girma a kauyen da babu wanda ya taba zama babban dan kwallo ya bugawa wata babar kungiya a duniya hakan yasa kowa yake cewa abinda nakeyi bamai dorewa bane gwanda in koma inyi karatu domin zama malamin makaranta” in ji Mane

Ya ci gaba da cewa “Sai dai naci gaba da gayamusu cewa kwallon kafa itace hanya daya tilo da zan iya taimaka musu sai dai basu yarda ba saboda basuga wanda yataba zama babban dan kwallo ba gaba daya kauyenmu har sai da sukaga na samu kungiyar, sannan kuma tsakanin garinmu da babban birni da nisa sosai”

Mane, wanda a yanzu haka yake daya daga cikin ‘yan wasan da babu kamarsu a kasar Ingila ko kuma a duniya ma gaba daya idan har ana maganar ‘yan wasan gaba ya ce sai da ya kulla yarjejeniya da babbar kungiya sannan iyayensa suka amince cewa zai iya buga kwallo.

 

  • Yadda Ya Fara Taimaka Wa Mutanen Kauyensu

A kwanakin  baya Sadio Mane ya bada miliyoyin kudi da suka kai kusan miliyan 200 ga dagacin kauyensu domin a gina makaranta da asibiti da kuma masallaci sakamakon kauyen nasu babu wadatattun abubun da aka lissafo.

Wannan taimako yaja hankalin gwamnatin kasar da mutane kasar gaba daya kuma yana yawan taimakawa mutanen garin da kudi idan har yasamu damar zuwa kasar sannan kuma yanada kungiyar ko kuma gidauniya wadda yasa aka kafata domin tallafawa marasa gata a kauyen nasu.

Har yanzu babu wani dan wasa mai girmansa a kauyen nasu kuma shine dan wasa na farko daya taba wakiltar kasar a kauyensu hakan yasa matasan kauyen sun sake dagewa wajen buga kwallon kafa domin dai suka suma sun zama ko kuma sunyi abinda yafi na Mane.

Har ila yau Mane ya bude kungiyar kwallon kafa a kauyen nasu kuma yana taimaka mata da kudi da duk wani kayan wasa domin ganin matasan kauyen suma sun fito sun nuna kansu a duniya sannan kuma yana yawan yiwa kungiyar fatan alheri idan yana hira da manema labarai.

 

  • Shin Da Gaske Sadio Mane Musulmi Ne?

A lokuta da dama ana ganin Mane yana addu’a idan har kungiyarsa ta Liberpool zata buga wasa ko kuma zai bugawa kasar Senegal wasa sannan kuma yana yawan zuwa masallaci a birnin Liberpool dashi da Muhammad Salah.

Kasancewa Mane da Muhammad Salah yasa abokantar ‘yan wasan ta kara karfi sosai sakamakon shima Muhammad Salah musulmi ne sannan kuma yana yawan tallafawa musulmi a garin Liberpool din a wasu lokutan idan bukatar hakan ta taso.

Sai dai har yanzu ana cewa ba’a taba ganinsa a kasar Saudiyya ba domin yin ibadah duk da cewa anga ‘yan wasa irinsu Muhammad Salah da N’Golo Kante na Chelsea da Paul Pogba na Manchester United.

Amma kuma hakan baya nufin cewa shi ba musulmi bane saboda ana yawan  ganinsa yana addu’a a masallaci sannan kuma babban abokin Muhammad Salah ne kuma yana taimakon addini.

Har ila yau bincike ya nuna cewa mutanen kauyensu kashi 90 cikin dari musulmi ne kuma gaba daya mutanen gidansu da abokansa na gida duk musulmi ne sannan kuma babu wani daya tabayi wanda yake nuna cewa shi ba musulmi bane.

Kawo yanzu dai Mane yana daya daga cikin manyen ‘yan wasan Africa da ake ji dasu kuma sunansa ya fito acikin sunayen wadanda ake ganin za’a bawa gwarzon dan kwallon Africa wanda hukumar kwallon kafa ta nahiyar Africa take bayarwa
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: