Kimanin mutane 666 daga cikin wadanda suka fada tarkon masu safarar bil ‘adama ne aka ajiye a cibiyar OIM mai kula da ‘yan cirani dake Zinder daga shekarar 2017 zuwa 2021 a cewar rahoton hukumar ta IOM wanne ya kara da cewa kashi 69 daga cikinsu mata ne da ‘yan mata.
Wani rahoton hukumar Majalisar Dinkin Duniya (MDD) mai kula da hijirar jama’a wato IOM ya gano cewa galibin mutanen da ke shiga hannun masu safarar mutane a kan hanyoyin dake ratsa Jamhuriyar Nijer zuwa kasashen Larabawa da na yammacin duniya mata ne da ‘yan mata suke shiga tashin hankali.
Wadanan mutane an yi masu rajista ne a Zinder da Agadez da Arlit da Dirkou da birnin Yamai abin da ke nunin yadda fataucin mutane ke neman zama ruwan dare a wannan kasa duk da matakan da mahukunta ke dauka.
Daliba a wata makarantar ilimin kimiyar Kwamfuta, Shamsiya Sabo na mai alakanta wannan al’amari da wasu tarin dalilai.
Rahoton ya ambato wakiliyar hukumar OIM a Nijer Barbara Rijks ta na cewa kyakkyawar fahimtar da ake samu a ayyukan hadin guiwar dake tsakaninsu da hukumomin kasar ta taimaka sosai wajen gudanar da wannan bincike da zai ba da damar tallafa wa wadanan mutane. Shugabar Kungiyar Kare Hakkin Mata ta APAISE Hadjia Rabi Djibo Magaji na da irin wannan ra’ayi.
Haka kuma an gano cewa kashi 56 daga cikin 100 na wadanan mutane ‘yan Nijeriya ne dake neman ratsa Nijer don zuwa kasashen Yammaci yayin da kashi 23 daga cikinsu ‘yan Nijer ne sannan sauran kan fitowa ne daga kasashen yankin Kudu da sahara.
Wani mai rajin kare hakkin jama’a Dambaji Son Allah mamba ne a kwamitin hadin gwiwar hukumomi da kungiyoyi masu zaman kansu CNLTP mai yaki da fataucin mutane.
Kashi 38 daga cikin 100 na wadanda da aka ajiye a cibiyoyin kula da bakin haure mutane ne da aka saka cikin harkar kasruwanci ko kuma ake kokarin shigar da su cikin wannan harka yayin da kashi 21 daga cikinsu ana ci da guminsu ta hanyar aikatau da wasu sauran ayyukan karfi sai kashi 23 na rukunin wadanda aka tilastawa shiga sana’ar bara a cewar hukumar OIM.