Ana so a jirkinta yin sahur zuwa karshen dare. Akwai hadisai da suka nuna haka.Â
An karÉ“o hadisi daga Sahlu dan Sa’ad Allah ya kara yarda a gare su, ya ce: “Na kasance ina yin sahur tare da iyalaina, sai na yi gaggawa (zuwa masallaci) domin na riski sallar asuba tare Manzon Allah Sallallahu alaihi wa alihi wa sallam” Bukhari (#577, da #1920)
An wani hadisi daga Anas dan Malik daga Zaidu dan Sabit, Allah ya kara yarda a gare su, ya ce: “Mun yi sahur tare da Annabi Sallallahu alaihi wa alihi wa sallam, sa’an nan ya tashi ya tafi salla. Sai na ce: Mene ne tazarar da take tsakanin yin sahur da kiran salla? Sai ya ce: gwargwadon a karanta aya hamsin (matsakaita)” Bukhari (#576, da #1921) da Muslim (#1097)]
A cikin wannan hadisi akwai halaccin mutum ya fita da dare domin wata bukata, domin Zaidu dan Sabit ba tare da Annabi suke kwana ba, kuma akwai halarcin a taru domin a yi sahur. Domin ganin haka duba Fathul Bãri (4/495)
Amma mai azumi ya kula matuka wajen kirdadon karshen dare. Sannan mutum ya yawaita addu’a da tuba da istigfari da neman gafara, domin lokaci ne na karbar addu’a.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp