Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home ILIMI

Sai Da Hadin Gwiwa Ilimin Mata Zai Bunkasa A Kasar Nan —Dakta Fatima

by Tayo Adelaja
August 1, 2017
in ILIMI
6 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Muhammad Maitela, Damaturu

Dakta Fatima S. Mohammed (Phd) hazikar mace mai fadi-tashin ganin ilimin ’ya’ya mata ya bunkasa, kallabi tsakanin rawunna, kwararriyar masaniyar ilimin kimiyyar harhada magunguna (Biochemistry), Malama, kuma Shugabar tsangayar Biochemistry a Kwalejin kimiyya da fasaha ta gwamnatin tarayya da ke Damaturu a jihar Yobe, kuma babbar Malamar jeka-ka-dawo a Jami’ar gwamnatin tarayya da ke Gashuwa, Yobe da Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, da Jami’ar Dutsimma da ke Katsina.

samndaads

An haifi Dukta Fatima S. Mohammed a garin Potiskum, cibiyar Karamar Hukumar mulki ta Potiskum da ke jihar Yobe a 1970, ta bayyana takaicinta dangane da yadda ilimin ’ya’ya mata yake fuskantar koma-baya a Arewacin kasar nan, tare da bayyana cewa al’adu da yanayin matsin tattalin arzikin mazauna wannan yanki na Arewa ke ciki a matsayin ginshikin tabarbarewarsa. Sannan ta bada shawarar cewa dole sai an hada hannu da karfe tsakanin gwamnati da al’umma, hadi da kungiyoyi masu zaman kansu kafin a shawo kan matsalar.

Dukta Fatima ta yi wadannan kalaman ne a cikin wata tattaunawar musamman da wakilinmu na jihar Yobe, Muhammad Maitela ya yi da ita a gidan ta da ke Damaturu, kan batutuwan yadda ci gaban ilimin ’ya’ya mata yake a jihar da ma yankin Arewa baki daya ko akasin hakan. Sannan da matakan da ya kamata a bi don shawo kan wasu daga cikin matsalolin.

Dukta Fatima S. Mohammed ta fara da fayyace matakan da ta bi tiryan-tiryan har ta kai matsayin da take yanzu, baya ga tuba-tuban da ta sha karo da su a fagen neman ilimin zamani a matsayinta na ‘ya mace. Tare da ankarar da cewar ba abu ne mai sauki ba, a irin wannan muhalli, a gurin ’ya mace ta tsallake irin wannan siratsin ba.

Inda ta ce al’ummar yankin Arewa, musamman Arewa maso Gabas, an al’adanci fifita ’ya’ya maza kan mata, kuma hatta mu’amalar yau da kullum ta kunshi hakan, yayin da har abin ya yi tasiri a jini, kan cewa kowane lokaci mata su ne a baya, maza su ne kan gaba. Kuma wannan ya sanya tsoro da fargaba a zukatan ’ya’ya mata wajen yanke tsammanin yin karatun boko mai zurfi, musamman a fanin kimiyya da fasaha.

“Daya daga cikin kalubalen da na yi ta cin karo da su, tun muna Firamare; kamar yadda yake a al’adun mu, wani lokaci za ka rinka jin ana cewa ai ilimin ’ya mace ba shi da wani amfani, ko tasiri. Saboda yadda yake a shekarun baya, an saba bisa al’ada ka iske ’ya mace komai kokari da son karatunta, ba kasafai take wuce matakin Sakandare ba, to balle a ce ilimin kimiyya da fasaha. Amma ni sai ya kasance na samu goyon bayan mahaifin mu ta dalilin tsayin-daka kan sai na yi karatu mai zurfi, tare da karya lagon wancan tunani”. Ta bayyana.

Ta ci gaba da bayyana cewa, “saboda haka bisa ga hakikanin gaskiya iyaye ne suka ba ni cikakken goyon baya wajen cimma burina na samun nasarori a rayuwa ta, a fannin karatuna na boko mai zurfi. Haka kuma, ba wai wata makarantar kudi ko gata aka kai mu ba, ko daya, makarantu ne na gwamnati wadanda kowa da kowa zai iya zuwa. Makarantar farko da na yi ita ce Kara Primary da makarantar ’yan mata ta GGSS, duk a cikin garin Potiskum.”

Dk Fatima S. Mohammed, ta ce bisa ga yadda ta kuduri aniyar cimma wannan buri nata, shi ne sai ta yunkura zuwa Jami’ar Maiduguri da ke jihar Borno, inda ta yi Diploma a fannin ilimin kimiyya, inda wannan ya ba ta zarafin zarcewa karatun Digirinta na farko a Jami’ar, a sashen ilimin kimiyyar harhada magunguna (Biochemistry). Daga bisani ta karanci Digirinta na biyu a fannin tsarin kiwon lafiya da gudanar da shi, wato Health Planning and Management, duk dai a Jami’ar ta Maiduguri. Har walayau kuma, ba ta tsaya nan ba, ta nausa kasar Burtaniya inda ta yi Digirin-digirgir (PhD) a Jami’ar Cranfield a fannin ilimin kimiyyar muhalli (Enbironmental Biochemistry).

Da ta ke zayyana wuraren da ta yi aiki kuwa, Malamar ta bayyana cewa, “da farko na fara aiki da Hukumar sashen koyarwa ta ma’aikatar ilimi a jihar Yobe(TSB), kuma Malama mai koyar da darussan Chemistry, Biology, da lissafi da sauran su. Sannan mai bibiyar lamurran da suka shafi yanayin ilimin ’ya’ya mata. Daga bisani na koma aikin malanta da Kwalejin kimiyya ta Federal Polytechnic, Damaturu a1996). Kuma zan iya cewa ni ce farkon Malama kuma shugabar tsangayar Biochemistry a Kwalejin. Bayan da na bar gurin a can baya, yanzu haka sun sake nemo ni domin ci gaba da kulawa da gurin ganin akwai karancin kwararru a wajen.”

“Haka zalika, na gudanar da bincike-bincike da dama dangane da abin da ya shafi yanayin muhalli-a numfashi, ruwa da kasa, shi ne gudanar da gwaje-gwaje kan hadurra da kalubalen da ke tunkarar lafiyar bil adama. Kuma ban tsaya nan ba; kamar yadda na shaida maka a baya, ina mai sa ido wajen ganin bunkasa rayuwar mata da ilimin su a wannan yanki namu,” ta ce.

Har wala yau, kwararriyar Malamar jami’a ta sake nuna cewa, irin wadannan tunanin sun bude kofa hatta iyaye suna kallon ilimin ’y’ya mata baida wani amfani, ko tsoron kashe kudi ma wani na kallonsa a matsayin aikin banza, ko tunanin ilimin kimiyya da fasaha ga ‘ya mace, ba abu ba ne mai yiwuwa ba. Sai ta ce, “wannan kuskure ne babba, kuma bai kamata mu rinka jin ba za mu iya ba, ko fargabar daukar nauyin ’ya’yanmu ba, kada mu manta Allah ya ce ‘tashi in taimake ka,’ kuma kada mu manta kan cewa duk wanda ya ilmantar da mace ya ilmantar da al’umma ne, sabanin wanda ya ilmantar da namiji ya ilmantar da mutum daya ne. Lokaci ya yi da za mu farka daga dogon barcin da muke yi.”

Duk da wannan, Malamar ba ta tsaya nan ba ta sake shaida da cewa, halin da ake ciki yanzu, kusan duk fadin jihar Yobe babu wata makarantar mata ta a zo a gani, ko wani ingantaccen tsarin da ake bisa kansa wajen bunkasar ilimin mata. Inda ta ce, “idan ka ziyarci makarantun mu na Firamare ko na Sakandare abin babu kyaun gani, sai ka tarar da yara sama da 100 a aji guda, sannan wasu yankuna da dama a wannan jihar ba su da babbar makarantar Sakandare ta ’yan mata ko daya, saboda haka uba ba ka da zabi, ko dai ka kai diyarka makarantar kudi ko ka hakura da karatunta, alhalin su ma makarantun kudin ba tabbas ne da su ba wajen samar da ingantaccen ilimi da tarbiyyar yarka.”

Ta ce, “kuma idan mun kalli wadannan matsaloli, wadanda suka yi wa sha’anin ilimin ’ya’ya mata katutu, gwamnati ita kadai ba za ta iya magance su ba, dole sai an hada hannu wuri guda tsakanin ita gwamnati da kungiyoyin da ba na gwamnati ba, tare da sauran kananan kungiyoyi da dai daikun al’umma. Wannan ita ce kadai mafitar matsalar koma-bayan sha’anin tabarbarewar ilimin mata. Sannan kuma, wannan matsala ta shafi hatta zamantakewar iyalinmu a Arewa.”

“Yanzu kamata ya yi a farfado da tsarin koyar da sana’o’in hannu na dogaro da kai ga mata, wanda idan yarinya ta kammala karatun, a kalla an koya mata sana’ar dinki ko saka, yin man shafawa ko sabulu da makamantansu, wanda ko da aure aka yi mata wannan sana’a za ta tallafa mata wajen dogaro da kanta, ko da mijin nata bai ba ta ba, kuma wannan zai ba ta kwarin gwiwar zuwa karo ilimi a duk lokacin da ta samu zarafi. Sabanin yanzu haka da yanayi ke hana da dama zuwa makarantar gaba,” in ji Malama Fatima.

Hajiya Fatima S. Mohammed ta bayyana cewa, “yanzu haka mun tsayu haikan wajen wayar da kan iyaye da ’ya’ya mata inda wani lokaci ma mukan kai ziyarori daban-daban a wasu makarantu a nan jihar Yobe, tare da karfafa gwiwar iyaye da dalibai da ba su karsashin cewa su bar yanke tsammanin ci gaba ko jin tsoron karanta kimiyya, ina mai ba su misali da kaina, sannan ya haska masu yadda na faro da inda muke yanzu.”

“Wannan ya ba ni damar canja tunanin yara da iyaye da dama dangane da yadda ya kamata su yi domin cimma muradu a rayuwa. Sannan yanzu haka muna kokarin samar da wata kakkarfar kungiyar da za mu rika magana da murya daya don tunkarar wannan matsala a nan jihar Yobe da ma a Arewacin kasar nan, kuma in sha Allahu sai abin da ya ture wa Buzu nadi a kan wannan manufa tamu.” Dk Fatima ta dauki alwashi.

SendShareTweetShare
Previous Post

Mun Kammala Shirye Shiryen Dawowar Buhari – Fadar Shugaban Kasa

Next Post

Wata Sabuwa: Masu Mata Sama Da Daya Sun Fi Dadewa A Duniya?

RelatedPosts

Me Yasa Ake Dakile Ilimin Mata A Arewa (1)?

by Sulaiman Ibrahim
6 months ago
0

SHIMFIDA. Lokacin da aka sace daliban makarantar Chibok a jihar...

Hana Barace-barace Shi Ne Mafi Alheri Ga Al’umma – Pantami

Zuwa Ga Shugaba Buhari!

by Daurawa Daurawa
9 months ago
0

Barka da shan ruwa, da kuma fatar Allah ya amshi...

Mafita Kan Yadda Aka Yi Watsi Da Ilimi A Arewa

Mafita Kan Yadda Aka Yi Watsi Da Ilimi A Arewa

by Sulaiman Ibrahim
9 months ago
0

Ilimi haske ne da shiriya, kamar yadda jahilci duhu ne...

Next Post

Wata Sabuwa: Masu Mata Sama Da Daya Sun Fi Dadewa A Duniya?

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version