Sai Gwamnati Ta Bayar Da Kaso A Cikin Naira Biliyan 823 Kafin Mu Dakatar Da Yajin Aiki -ASUP

ASUP

Kungiyar malaman kwalejin kimiyya da fasahar ta kasa (ASUP) ta ci gaba da gudanar da yajin aiki wanda ya tsaida harkokin karatu a dukkan kwalejen kasar nan, inda ta dage sai gwamnatin tarayya ta biya mata bukatocinta kafin ta koma bakin aiki.

Ta bayyana cewa, a yanzu haka suna bukatar gwamnatin ta ba su naira biliyan 19, wato kashi 2.23na naira biliyan 823 wanda gwamnatin tarayya ta amince za ta bai wa kungiyar da za a kashe su wajen gyara kwalejin kimiyya da ke fadin kasar nan tun a shekarar 2018. A cewar kungiyar, a cikin naira biliyan 19 da gwamnatin za ta ba su, za su yi amfani da naira biliyan 15 wajen gyara kwalejin kimiyya da ke fadin kasar na, sauran biliyan hudu kuma za ta yi amfani da su wajen biyan hakkokin malaman na mafi karancin albashi.

Shugaban kungiyar ASUP, Dakta Anderson Ezeibe shi ya bayyana wannan mataki lokacin da yake zantawa da manema labarai. A cewarsa, kungiyar ASUP ba ta yi tsammanin yajin aikin ya kawo har zuwa wannan lokaci ba, amma gwamnatin tarayya ne take jan kafa a kan lamarin wanda ya sa har ya kawo wannan lokaci. Ya ci gaba da bayyana cewa, kungiyar ASUP ba ta bukaci sabon wani abu ba, amma tana bukatar gwamnatin tarayya ta cika tsohon yarjejeniyar da ta kulla da ita.

“Mu fa ba sabon abu muke bukata ba. Muna bukatar gwamnatin tarayya ta gaggauta kashe wa vangaren ilimin kwalejin kimiyya da fasahar naira biliyan 19 ba tare da wani vata lokaci ba. Zai inganta harkokin ilimi a vangaren kwalejin kimiyya da fasaha da kuma inganta tattalin arzikin kasar nan.

“Kamar yadda nake magana a halin yanzu haka, sadar farashin kayayyakin zai lakume yawan kudaden. Darajar naira biliyan 19 a shekarar da ta gabata ba zai zama daya da na wannan shekarar ba, domin a kowacce rana darajar kudaden na kara yin kasa.

“Domin haka, ya kamata gwamnatin tarayya ta gaggauta sakin wadannan kudade a kan lokaci ba tare da wani jinkiri ba.

“Mun ji cewa ma’aikatan ilimi ta tarayya ta rubuta wa shugaban kasa wasikar a kan bayar da kudaden, ba za mu dogara da wasikar bayar da kudaden ba har sai mun tabbatar da bayar da su.”

Shugaban kungiyar ASUP ya kara da cewa, kwalejin kimiyya da fasahar tana bunkasa sana’oin da suke kara inganta tattalin arzikin. Ya kuma roki dalibai da iyayen da sauran masoya ci gaban ilimi da su dauki wannan yajin aiki a matsayin sadaukarwa domin samun ci gaba mai daurewa. Ya ce, domin haka, mambobin kungiyar ASUP su ci gaba da zama a gida har sai an cika musu bukatocinsu.

Exit mobile version