Wani dan kasuwa, kuma dan takarar Shugaban kasa a shekarar 2019, Mista Gbenga Olawepo Hashim ya bayyana cewa lokaci ya yi da dukkan bangarorin da ke jayayya da juna su daidai ta a game da mahawarar sake fasalin Nijeriya, domin hakan ya dace a yi shi ne don hadin kan kasa, zaman lafiya, tsaro da ci gaba baki daya.
A cikin wata takardar da aka raba wa manema labarai a ranar Litinin, Olawepo Hashim bayani ya yi da cewa tun da dai Gwamnatin tarayya ba za ta ci gaba da yin wani abu ba a game da batun rabon iko a kan wasu al’amura, kuma za a iya samun abin da ake bukata domin abu ne mai yuwuwa, shi kuma bangaren masu daga murya a bangare daya, ba wai komai da suke magana a kansa ba ne zai yuwu a cikin jadawalin bukatunsu kafin lokacin zabe mai zuwa, hakika ya dace a samu matsaya tsakanin bangarorin.
Kamar yadda babban dan kasuwar ya ce, tsarin daidaitawa daga wajen majalisar zartaswa ta fuskar yi wa kundin tsarin mulki gyaran fuska a kan wani bangare da ke magana a game da batutuwan yau da kullum da kuma na bangaren masu yin dokoki, hakika duk za su yiwu, musamman a bangarorin da suka kasance daman akwai batutuwa a bayyane da aka cimma yarjejeniya.
Ya bayyana cewa, “lokaci ya yi mu amince a kan batutuwan da za a iya amincewa da su, sai kuma mu ci gaba da tattaunawa a game da wadanda ba a fayyace su ba, amma za su iya zama cimma nasara a nan gaba. Samun cimma daidaito ba alama ce ta rauni ba, amma dai alama ce da ke nuna cewa ana bukatar ci gaba da kuma taimakon kasa”.
Ya ci gaba da cewa, “gyaran da zai ba kananan Hukumomi damar samun mallakar dukkan ma’adanan kasa, musamman ga wadanda suke a kan doron kasa. Samar da gyare-gyaren a game da samar da wutar lantarki, wato a ba Gwamnatin tarayya da Jihohi ikon samar da wutar lantarki, sarrafata da kuma rarrabawa da kuma gyaran fuska a bangaren dokar zabe da suka hada da samar da sakamakon zabe ta hanyar zamani da na’ura a dukkan matakan da ake tattara sakamakon zabe”.
Mista Olawepo Hashim ya ce, daga cikin wannan tsarin samar da gyaran tsarin mulki a cikin sauki zai samu gagarumin goyon baya daga Gwamnonin jihohi 36 a Nijeriya, da kuma shugabannin majalisun dokokin jihohi.
Ya ce, “abin da ake bukata na samun kashi 2 cilin uku na goyon baya daga majalisun jihohi a fadin kasar nan za a iya samunsa domin samun abin da ake bukata a kundin tsarin mulki in an gudanar da gyaran”.
“Dole ne Nijeriya ta ci gaba da zama a cikin zaman lafiya da kyautatuwar al’amura, gina kasa ba zai taba zama ya samu a kwana daya ba ko a lokaci kankani ba. Ai da akwai rayuwa bayan shekarar 2023, kuma ina da tabbacin cewa Nijeriya za ta rayu kuma sauran wadansu batutuwan za a iya duba su bayan zaben 2023 da ikon Allah,” in ji shi.
Ya kara da cewa, tsarin amincewa alama ce ta samun kwarin gwiwa ba rauni ba. “Inda kawai na ga ba batun amincewa shi ne abin da masu tsattsauran ra’ayi suke ta matsawa sai sun raba Nijeriya. Don haka daga cikin mutane irina da muke son Nijeriya da kuma wadanda suka sadaukar da kai ko kuma suka sha wahala domin samar da Dimokuradiyya a kasar nan.”