Daga Khalid Idris Doya
Gwamnan Jihar Ribas Nyesom Wike, ya bukaci shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari, da cewa ya kalli batutuwan da ake akwai kan sake fasalta kasar nan gami da batun korafi kan tattalin arziki da wasu ke kallon ana kwararsu, ya na mai cewa muddin aka gaza shawo kan matsaloli kasar nan a halin yanzu, to lallai ana fuskantar barazana mai hatsari.
Gwamnan ya ce, dole ne fa Buhari ya hanzarta magance matsalolin da
suke addabar Nijeriya a yanzu.
A jawabin da Wike ya gabatar yayin wata shirin a wata gidan talabijin
kamar yadda Kakakinsa Kelbin Ebiri, ya nakalto a ranar Alhamis, yana
mai cewa yanzu ne lokacin gyara da shawo kan lamura.
Wike ya yi wannan bayani ne a matsayin martani ga bukatun gwamnonin
Kudu maso Kudancin kasar, lokacin da suka hadu da wakilcin shugabancin
kasar da Ibrahim Gambari shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasar ya
jagoranta, zaman da aka yi kwana-kwanan nan kan wannan batun a
Fatakawal wanda aka roki Buharin ya gaggauta biyan bukatun da suke
akwai.
Ya ce, yanzu ne lokacin da ya dace Buharin ya farka domin yin ababen
da suka dace tun kafin lokacin da lamura za su wargaje fiye da halin
da ake ciki a yau.
Gwamnonin da suke da damuwa a ransun sun nemi a bar jihohi su rika iko
da albarkacinsu sama da gwamnatin tarayya, domin tabbatar da ci gaban
mutanensu.
“Ba wai ba ni da kwarin gwiwa ba ne, ban yarda da cewa ba don baka yi
abin da aka cimma matsaya da kai ba a jiya, baya nufin ba za ka yi
abin da aka cimma da kai ba a yau,” in ji Wike.
“Mutane sun yi korafin tattaunawa ba za ta haifar da komai ba. Ni ban
yarda da su ba. Na yi imanin idan shugaban kasa bai yi hakan ba, wato
bayar da dama, zai jefa Nijeriya cikin tashin hankali.
“Bai zama dole ya iya yin komai da ya yi alkawari ba, amma mutane na
son su ga wata shaida a kasa karkashin shugabancin Buhari, ko ba komai
ya yi abu daya biyu uku hudu na bukatun mutane”.
Ya nemi Buharin da ya farka ya nemi hanyoyin da za su kai wajen ganin
an shawo kan batutuwan ta yadda kowani yanki ba zai ji ana kwararsa
ba.