Connect with us

MAKALAR YAU

Sakin Masu Garkuwa A Katsina: A ina Matsalar Ta Ke? (2)

Published

on

Kamar yadda na yi alkawari cewa zan cigaba da kawo abubuwan da Rijistara Kabir Shu’aibu ya bayyana a takardar manema labarai, yau cikon ikon Allah zan cigaba daga inda na tsaya a satin da ya gabata.

Kazalika ya gano cewa takardar belin ta na dauke da sanya hannun babban jami’in shari’a U.D Farouk mai aiki a jibiyar da ke bayar da lauyoyi ga mutanen da ake tuhuma da manya laifuka kuma basu da karfin daukar lauya.

Haka kuma an buga ma takardar sitam na kungiyar lauyoyi ta kasa, sannan lauyan da ke neman belin ya gabatar da wanda ya zai tsaya a bayar da belin, bayan da ya gabatar da takardar gabatarwa ta bogi da ke da sa hannun hakimin Kankara wanda wadanda a ke zargin sun fito daga yankin ne.

Wannan dabi’a da halayen da magatakardan tare da abokanan kullinsa su ka nuna sun zama yaudarar shari’a da laifuffukan da suka shafi gudanar da aiki a bangaren shari’a a a karkashin sashi na 124 da 125 da 141 da kuma 148 na kundin tsarin laifula da hukuncinsu na jihar Katsina.

Bisa ga haka ne babban Jojin na jiha ya tura kes din ga sashen tsaro na farin kaya  domin yin bincike da kuma fito da gaskiya yadda lamarin ya faru, domin daukar mataki na gaba.

Ya yi karin haske da cewa, wannan ba laifi bane kadai, cin amana ne da kuma yin zagon kasa ga sha’anin tsaro na kasa, da kuma sauran lamurrana da suka shafi shari’a.

Sashen tsaro na Farin kaya sun gudanar da kwarya-kwaryan bincike, inda suka gayyaci duk wani mai ruwa da tsaki game da laifin, wanda ya hada da hakimin Kankara, wanda takardar gabatarwa ta bogi ta fito daga ofishin sa. Babban jami’in da ke kula da gidan gyaran hali na jihar Katsina wanda ya sallami wadanda ake tuhumar ba tare da na gabatar da su gaban babbar kotun majistare ba domin tabbatar wa.

Haka kuma shi  U. D. Farouk yayi alkawari a rubuce gaban babban jojin jiha cewa zai  shirya yanda za a sake kama masu laifin da aka saki bisa yaudarar kotu, kuma hukumar DSS suka aminta da yin hakan , amma har sama da sati daya bai iya yin hakan ba. Saboda haka ne aka tsare shi, tare da gabatar da shi a gaban kotu.

Lokacin da aka gabatar da bukatar bada belin ma’aikatan shari’ar tare da shi lauyan,  da sauran wadanda ake tuhuma da laifin a gaban babbar kotun jiha ta 6 sai kotun taki amincewa da bada belin su.

Kungiyar lauyoyi ta kasa reshen jihar Katsina (NBA) ta san hanyar da ake daukaka kara, amma maimakon tayi hakan, sai ta zabi ta yayata abin ga jama’a, ta hanyar kiran taron manema labarai da  ikirarin cewa U. D. Farouk bai aikata wani laifi ba zance ne kawai, domin kotu ce kawai take iya tabbatar da hakan.

Mai girma babban jojin jiha ya kafa kwamitni da zai binciki lamarin a cikin gida. kwamitin ya kunshi Joji daya, a matsayin shugaba , Babban sakatare a ma’aikatar shari’a, babban magatakardar babbar kotun jiha, wakilin kwamishinan ‘yan sanda, wakilin daraktan DSS na jihar Katsina, shugaban kungiyar lauyoyi ta jihar Katsina (NBA)  kuma duka mambobin kwamitin nan lauyoyi ne, kuma mambobin kungiyar NBA.

Ba a jima ba da kwamitin ya mika rohotonsa, kuma zuwa yanzu ana kan nazarinsa , domin daukar matakin da ya dace  na shari’a akan wannan badakala da ta afku a cikin sashein shari’a

Muna tabbatarwa da jama’ a cewar babu inda muka ce wai an yaudari babban jojin jiha ne ya saki wadannan hatsabiban masu garkuwa da mutane, kamar yanda ake yadawa a kafafen sadarwa na zamani .

A takaice wadannan sune kalaman kariya da baban rijistara Kabir Shu’aibu dangane da zargin da ake yi wa mai gidansa baban jojin jihar Katsina Mai Shari’a Musa Danladi Abubukar na yin sakaci da aikinsa wajan bada umarnin sakin wadancan mutane.

Idan muka duba yadda wannan bayanin ya gabata za mu ga cewa har aka ci a cinye ba a yarda cewa babban jojin ya yi kuskure wajan sakin wadannan ‘yan ta’ada ba, saboda haka dole ne Kabir Shu’aibu ya amshi gyara cewa lallai an yi kuskure baban sai dai maganar gyaran Allah.

sannan  idan muka yi nazarin sharudan da aka bayar da su beli wadanda suka hada da mutane guda biyu wadanda za su tsaya masu a gaban shari’a, sai kuma takarda daga hakimi wanda take nuna cewa yasan da magana kuma ya amince da bukatarsu, za mu ga cewa kamar haan ya yi kadan amatsayin sharuda da ka iya sawa a bada belin wanda ake zargi da laifi irin wannan.

Gaskiyar magana shi ne irin wannan al’amari ya ja hankalin masu fashin baki akan sha;anin shari’a shi ma abu ne da ya kamata a duba domin yin gyara saboda gaba

Haka kuma a adalci na jarida da kuma yan adamtaka akwai bukatar a ji daga bakin wadanda wannna lamari ya shafa domin jin na su bayanan wadannan bayanai da kume wadanda aka danganta su da shi wasu suke fada a madadin su, amma in da su samu ne, daga bakinsu ya kamatb a ji domin yin adalci akan wannna sha’ani

To sai dai kawai yiwuwar har a ci a cinye da wahala aji daga bakin wadannan mutane domin suna hannn hukumar tsaro ta farin kaya wato SSS saboda haka abu ne mai hawalar gaske su bari a iya ji daga bakin wadanda ake zargi.

Kazlaika hakan ba zai hana masu fafutukar ganin adalci ya yi aikinsa akan wannan batu su cigaba da kokarin da suke yi na ganin hakan ta faru kowa ya samu adalci wanda shi ya yi karanci a bangaran shari’ar kasar nan baki daya.

Dangane da batun tawagar hukumar shari’a ta kasa da na yi maganar zuwansu jihar Katsina domin yin bincike na musamman game da wannan batu, har zuwa lokacin da nake hada wannan rubutu ba mu samu tabbacin isowar su jihar Katsina ba.

Amma dai ina bada tabbacin cewa duk lokacin da wannan tawaga ta iso jihar Katsina to zan sake dawowa domin yin bayanin irin abinda suka yarda aka ji, kuma nasan akwai kungiyoyin kare hakkin dan Adam da suka zura idanu suna kallon yadda wannnan batu zai kare.

Sannan ana jiran jin abinda kwamitin da Babban Joji ya kafa akan wannan badakala tare da irin shawarwarin da ya bada kuma yadda za a kalli abin domin kaow gyara a wannna bangare mai matukar muhimmaci a rayuwar ‘yan Najeriya.

Muna fatan a wannan karon ya zamana ma’aikatar shari’a ya fito da cikakken bayanin aikin kwamitin domin fidda kanta da wannan kallo da ake yi mata, sannan muna sa ran cewa sakamakon binciken shi zai zama dan ba na dawowa da martabar wannan bangare a jihar Katsina.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: