Daga Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
Ɗaruruwan mabiya aƙidar Kwankwasiyya a Jihar Sakkwato sun fito ƙwai da gije suka gudanar da saukar Ƙur’ani Mai Tsalki da Addu’o’in Musamman domin tunawa da ranar zagoyowar haifuwar Jagoran Kwankwasiyya na Ƙasa.
Kwankwasawan na Sakkwato a ɗaukacin Ƙananan Hukumomi 23 sun gudanar da addu’o’in musamman ne a ranar Asabar a gidan Jagoran Kwankwasiyya na Jihar Sakkwato, Honarabul Malami Muhammad Galadanci wanda aka fi sani da Bajare.
Bayan saukar Ƙur’ani malamai ɗaya bayan ɗaya sun gabatar da addu’o’in ƙarin yawaitar shekaru masu albarka, ingantacciyar lafiya da ƙarin ɗaukaka da nasara a dukkanin lamurran da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya sanya a gaba.
A zantawarsa da manema labarai, Jagoran Kwankwasiyya na Sakkwato Honarabul Malami Bajare ya bayyana cewar ranar muhimmiyar rana ce ta musamman da suke murnar tunawa da ayyukan alhairin da Sanata Kwankwaso ya aiwatar a karan zubin siyasar sa.
Ɗan Majalisar na Jihar Sakkwato daga mazabar Sakkwato ta Arewa ta (1) ya bayyana cewar “Kwankwaso jagora ne nagari, ya aiwatar da muhimman ayyukan raya jiha da ci-gaban al’umma a kowane fanni, ya gina Kano da Kanawa, ya samu nasarar zama na biyu a zaɓen fitar da gwani na takarar shugabancin ƙasa a jam’iyyar APC.”
Ya ce “Yadda Sakkwatawa suka fito domin taya murna ga Sanata Kwankwaso ya nuna cewar lallai tsohon Gwamnan na Kano, cikakken ɗan siyasa ne wanda ya samu gagarumar karɓuwa a faɗin ƙasa bakiɗaya.”
Wasu daga cikin mahalarta taron, Muktar Mu’azu ‘Yarsakke da Shehu Muhammad Danchadi sun bayyana cewar mulkin gaskiya da adalci da Kwankwaso ya gudanar a Kano ne dalillin da yasa suka bi jirgin siyasar sa. “Muna tare da tafiyar Kwankwasiyya 100 bisa 100 a matakin jiha da ƙasa bakidaya.” Inji su.
Fitaccen matashin ɗan kasuwa kuma ɗaya daga cikin masu tallafawa tafiyar Kwankwasiyya, Alhaji Abdulrazak Rabi’u Razi na daga cikin dimbin jama’ar da suka hakarci taron irinsa na farko a Sakkwato.