Liverpool ta cire sunan Mohamed Salah daga cikin yan wasanta da za su fafata a gasar zakarun Turai da Inter Milan a ranar Talata, hakan na zuwa ne bayan wata hira da Salah ya yi inda ya zargi Liverpool da rashin yi masa Adalci duk da kokarin da ya yi mata tsawon lokaci kuma ya bayyana rashin jituwa tsakaninsa da babban kocin kungiyar, Arne Slot.
An yanke shawarar cire sunan Salah da cikakken goyon bayan Slot kuma ana ganin hakan ya faru ne sakamakon kalaman Salah a bainar jama’a a ranar Asabar, zuwa yanzu ba a yanke shawarar daukar matakin ladabtarwa ba akan Salah, amma dan wasan mai shekaru 33 zai shafe dan wani lokaci kafin ya dawo cikin wadanda za su bugawa Liverpool wasa.
An shirya cewa Salah zai tafi gasar cin kofin kasashen Afirka (AFCON) ranar Litinin mai zuwa kuma ana sa ran zai rasa wasan Firimiya da Liverpool za ta buga da Brighton ranar Asabar, dan wasan gaban Masar ya yi magantu bayan an ajiye shi a benci a wasan da Liverpool ta buga canjaras da ci 3-3 da Leeds United, wanda shi ne wasa na uku a jere da aka fara wasa yana kan benci.
Kwallonsa ta karshe a cikin yan wasa 11 na farko shi ne wasan da suka sha kashi a hannun PSV Eindhoven a gasar zakarun Turai a farkon Nuwamba, inda ya ci kwallonsa ta karshe a ranar 1 ga watan Nuwamba a wasansu da Aston Villa, Salah, wanda ya koma Liverpool daga Roma a shekarar 2017 ya saka hannu kan tsawaita kwantiragin shekaru biyu a watan Afrilun da ya gabata, ya zura kwallaye biyar a wasanni 18 da ya buga a gasar Firimiya da gasar zakarun Turai a wannan kakar.














