Shugaba Bola Tinubu ya taya al’ummar Musulmi murnar sallah babba, inda ya bayyana muhimmancin sadaukarwa da hadin kai a tsakanin al’ummr kasar nan.Â
Ya yi fatan Allah Ya karbi addu’o’in da Musulmi suka yi a ranar Hajji.
- Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Gaza Tana Kasa Tana Dabo
- Ɗan Shekara 13 Ya Kashe Kansa Bayan Jami’an Tsaro Sun Azabtar Da shi
Shugaba Tinubu ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su yi la’akari da muhimmancin sadaukarwa da aiki wajen gina kasa.
Shugaban ya kuma amince da irin sadaukarwar da ‘yan Nijeriya suka yi a shekarar da ta gabata.
Ya bayar da tabbacin cewa hakurin da al’umma suka yi zai haifar da sakamako mai kyau, tare da bunkasa tattalin arzikin kasar nan.
A karshe, shugaba Tinubu ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa ta samar da tsaro, gyara zamantakewa, da tattalin arzikin dukkanin ‘yan Nijeriya.
Ya bukaci al’ummar kasar nan da su ci gaba da yin addu’o’in samun zaman lafiya da kwanciyar hankali domin samun ci gaban da ake muradi.