Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Mohammed Matawalle, ya ƙaddamar da rabon buhun shinkafa 7,000 da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya bai wa ’yan jam’iyyar APC a Zamfara domin bikin ƙaramar salla.
Sakataren Yaɗa Labarai na jam’iyyar APC a Zamfara, Yusif Idris ne, ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a Gusau.
- Gwamnati Ta Jaddada ƙudirin Kare ‘Yancin Faɗin Albarkacin Baki Da ‘Yancin ‘Yan Jarida
- Gwamnoni Na Kamun Kafa A Wurin Tinubu Don Hana Bai Wa Kananan Hukumomi ‘Yanci
Da yake miƙa kayan ga shugabannin jam’iyyar a Gusau, Minista Matawalle, wanda ya samu wakilcin Shugaban APC na jihar, Hon. Tukur Umar Danfulani, ya ce wannan tallafi na Shugaban Ƙasa alama ce ta kulawa da ’yan jam’iyyar.
Ya kuma buƙaci su ci gaba da yin addu’a domin samun zaman lafiya a jihar da kuma kawo ƙarshen matsalar ’yan bindiga da ke addabar yankin Arewa maso Yamma.
Matawalle ya gode da ƙoƙarin da shugabannin jam’iyyar a Zamfara ke yi wajen sadaukar da kansu da riƙon amana, wanda ke ƙara wa APC ƙarfi da haɗin kai.
Ya kuma buƙaci mambobin jam’iyyar da su ci gaba da haƙuri da fahimtar juna domin haɗa kai tare da tabbatar da goyon baya ga jam’iyyar.
A nasa ɓangaren, Sakataren APC na Zamfara, Hon. Ibrahim Umar Dangaladima, ya gode wa Shugaban Ƙasa Tinubu da Minista Matawalle bisa wannan tallafi.
Ya ce shinkafar ta zo a daidai lokacin da jama’a ke fuskantar wahalar rayuwa, kuma ya yi alƙawarin cewa ’yan jam’iyyar za su ci gaba da haɗa kai da kaunar juna.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp