Idan aka zo batun “salon zamanantarwa irin na kasar Sin”, za ku so ku ji shin: Takamaime wace irin hanya ce wannan? Me ya bambanta ta da zamanantarwa irin ta sauran kasashe a duniya? A gaskiya dai, fahimtar salon zamanantarwa irin na Sin babu sarkakiya a ciki. Tana nan lullube a cikin harkokin yau da kullum na jama’ar kasar Sin, da ma alakar da ke tsakanin wannan kasar da sassan duniya.
Salon zamanantarwa irin na kasar Sin wani tsarin zamanantarwa ne na dimbin jama’a, da zamanantar da samun wadata ta bai-daya domin daukacin al’umma, da zamanantar da tsarin dunkulewar kayayyaki da ruhin wayewar kai, da zamanantar da zaman lumana tsakanin mutum da dabi’ar halitta, da kuma zamanantar da bin hanyar samun ci gaba cikin zaman lafiya.
Salon zamanantarwa irin na kasar Sin shi ne wanda ya bude kofofinsa ga duniya. Musamman ga dimbin kasashe masu tasowa. Salon zamanantarwa irin na kasar Sin yana gabatar da kyakkyawar gogewa don yin tunani ko nazari kan cewa: bai kamata mutum ya sadaukar da muhalli don neman “gaggauta zamanantarwa” ba, sannan kada ya yi watsi da rayuwar jama’a don samun jari, kuma wajibi ne mutane kar su kuskura su sauya tsare-tsarensu da al’adunsu don biyan bukatun yammacin duniya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp