Bisa dalilai na zahiri, da matakai daban daban da mahukuntan kasar Sin ke aiwatarwa na zamanintar da kasa, muna iya cewa baya ga ci gaban da Sin ta cimma a wannan fage, su ma kawayenta, kuma abokan tafiya na kasashe masu tasowa musamman nahiyar Afirka, na iya koyon manyan darussa daga salon zamanintarwa na kasar. Cikin ginshikan cimma nasara da ake lura da su a wannan fage akwai batun yaki da fatara, da gina ababen more rayuwa, da bunkasar sashen kirkire-kirkiren fasahohi wadanda ka iya zamewa kasashen nahiyar Afirka kyawawan darussa a kan turbarsu ta bunkasa kai.
Alal hakika, kasar Sin ta yi aiki tukuru, inda ta tashi daga matsayin babbar kasar manoma zuwa cibiyar kere-kere da hada-hadar tattalin arziki ta duniya. Gwamnatin Sin ta yi aiki tukuru wajen tsame miliyoyin ’yan kasar daga kangin fatara, tare da himmatuwa wajen rage gibin dake akwai tsakanin mawadata da talakawa, da ma birane da yankunan karkara. Wannan na nuni ga muhimmancin daidaita tafiya tsakanin bukatun raya tattalin arzikin al’umma da na bunkasa zamantakewarsu.
Ko shakka babu kasashen Afirka ma na da matukar bukatar raya fannonin zamanintar da kai, musamman fannonin raya noma, da ayyukan gina layin dogo da hanyoyin mota, ta yadda hakan zai bayar da damar samarwa, da sarrafawa da safarar hajoji, da hidimomi, da zirga-zirga tsakanin al’ummu. Kana yayin da ake kokarin cimma wadannan burika, akwai babban misali da kasar Sin ta samar a wannan fage, wato samar da ci gaba ba tare da gurbata yanayi ko muhalli ba. A nan ya zama wajibi, yayin da kasashen Afirka ke kokarin samun ci gaba, su kuma kiyaye muhimmancin yaki da sauyin yanayi, da samar da isasshen makamashi mai tsafa, kamar dai yadda Sin ta wuce gaba wajen cin gajiyar makamashi mai tsafta da wanda ake iya sabuntawa, irin wadanda ake samarwa ta hasken rana da iska da sauransu, wadanda suka yi matukar dacewa da yanayin bukatu da albarkatun akasarin kasashen nahiyar ta Afirka.
Tabbas fannonin zamanintar da kai na Sin na iya zama babbar taswira da kasashen Afirka ka iya bi, wajen kaiwa ga bunkasa yankuna, da kyautata zamantakewar al’ummunsu, da samar da isassun damammaki na gudanar da kyakkyawar rayuwa mai cike da walwala ga al’ummun nahiyar.(Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp