Tsokacin yau zai yi duba ne game da yadda ake gudanar da zance wato zuwa hira wajen budurwa.
Idan aka yi duba da lokutan baya ko da a ce ba zamanin iyaye da kakanni ba, a iya wannan zamanin cikin shekaru kalilan da suka wuce, yanayin yadda ake gudanar da zance a yanzu ya sha bamban da lokutan baya.
A yanzu wasu matan da kansu suke zuwa wajen saurayi zance sabanin saurayi ya je wajen budurwa, sai dai kuma yin hakan akan rasa gane wa masu zuwa zance wajen samari, shin wayewa ce irin ta zamani da kullum take zuwa da sabon salo na rayuwa ko tabarbarewar tarbiyya ce ko kuma akasin hakan ne?
Haka kuma a sauyin da aka samu na zuwa zance lokutan baya kadan wanda ba a kai su da nisa ba, idan mace za ta yi zance za ta yi ne da rana ko da a ce za ta yi da dare ba za ta yi shi ya wuce karfe taran dare ko goma ba, sai dai a yanzu zancen ya zo da sabon salon da babu kyan kalla, domin da yawan wasu suna zance ne bayan daukewar kafar kowa, wani ma sai wajen tara ko goma na dare zai je wajen budurwar, har a kai ga za a rufe gidan su yarinyar, wanda wasu iyayen su suke cewa yarinyar idan ta gama zancen ta rufe gidan, sabida rashin kula.
Baya ga haka a lokutan baya kadan cikin wannan zamanin idan za a yi zance akan ba da tazara tsakanin Macen da Namiji yayin gudanar da zancen, sai dai a yanzu yin hakan ya zamo tamkar rashin wayewa da duhun kai, an maida haduwa da juna waje guda, a dadduma guda ko a dandamali guda, ko da kuma a tsaye waje guda gab da juna matsayin wayewa da kuma zamani wanda wasu suke kallon sa a haka.
A yanzu yin zance ga wasu ba shi da amfani ko kadan domin sukan fahimci junansu ne kafin su shiga gidajen aurensu ta wani fannin daban, wanda in aka yi rashin sa’a sai ya zamo saurayin ba shi zai zama mijin ba kuma ta riga da ta ba shi kanta.
Wannan dalilin ke sawa wasu mutanen ke yi wa ‘Yan mata kudin goro; gani suke dukka halin tamkar daya ne, sabida ya gwada a kan mafi yawan ‘Yan Mata, ya ga yadda suka bashi kansu dan haka kowacce ma hakan take a wajensa, wanda kuma sam! ba dukka aka taru aka zama daya ba, sai dai akan rasa gane tagari kamar yadda su ma mazan akan rasa gane na gari tun da ba tukunya ba ne bare a kwankwasa in ji masu iya magana, wannan a takaice kenan.
Dalilin hakan ya sa shafin Taskira ya ji ta baki wasu daga cikin mabiyansa, Ko Mene ne amfanin zuwa zance, ya tasirinsa yake?, Ya bambancinsa yake tsakanin lokutan baya kadan da na yanzu? Ya ake gudanar da zance? Iinda suka fayyace nasu ra’ayoyin kamar haka:
Rahmat A. Abba Jada (Matar Mamman) daga Bauchi:
Amfanin zuwa zance dan a fahimci juna a san da wa za a zauna, kuma hakan zai sa a fuskan ci ko wane irin mutum ma’ana halayyar sa da dcabi’unsa. Eh! gaskiya zance na lokacin baya dana yanzu akwai bambanci sosai ada ana zance cikin tsari na al’adar bahaushe wato kunya sai ka ga saurayi na can ita kuma budurwa na can rakube a gefe, sabanin na yanzu da mafi akasari za a yi ta cikin wayewa irin ta nasara za ki ga wani lokaci har ana runguma da sauran su.
Zance wani abu ne da saurayi da budurwa za su hadu ayi hira irin ta fahimtar juna. Saurayi zai zo kofar gidanmu karfe 4:00 na yamma ya yi sallama sai in fito biyar da rabi na yi zamu yi sallama ya koma.
Shawarar da zan ba matasa shi ne su tsare mutuncinsu da kimar su sa’annan in an je zance a ringa sassauta kalamai.
Hussy Saniey daga Jihar Katsina:
Zuwa zance yana da matukar amfani game da taka muhimmiyar rawa wurin fahimtar wa za ka aura ko da wa za ka yi soyayya.
Zancen da yana da bambanci dana yanzu tamkar nisan dake tsakanin bindin rakumi da kasa, domin yanzu zance yana zuwa da wani sabon salo mai girma, wanda a yanzu saurayi zai iya daukar budurwa su je yawon zaga gari daga nan har a yi mata siyayyar kayan makulashe da wasu abubuwan kuma daga ita sai ji ba tare da sun nemi dan rakiya ba. Zancen da kuwa da a kofar gida ma sai ta fita tare da yaro bare ma har a yi tunanin zuwa wani wuri. Saurayi ne zai zo gidansu yarinya, sai ya samu yaro ya aika a kira mishi ita ko ya kirata a waya, bayan ta fito za su gaisa daga nan sai su tattauna wasu abubuwan da suka shafesu.
Eh! ana zuwar min. Ina gudanar da zance ne a cikin gidanmu. Shawarata anan ita ce su tsarkake zukatansu kar su bari rudin zamani ya rudesu.
Comrade Muhammad Kabir Kamji daga Batsari Jihar Katsina:
Zance yana da matukar tasiri a fannin soyayya. Zance yana da tasiri sosai, domin zuwa zance kamar in ce wata hanya ce wadda take kara wa masoya shakuwa da juna, kara son juna. Zuwa zance yana taimaka wa namiji wajen gano idan macen tana sonsa, ta hanyar tarbar da ake masa, da kuma kalar kwalliyar da ake masa. Zance a soyayya ya fi komai amfani. Zancen lokutan baya kuwa ya sha bamban dana yanzun.
Zancen da aka yi a lokutan baya ya fi sosai. Zancen wannan lokacin kuwa babu abin da ke cikinsa sai fitsara da rashin kunya, zancen lokutan baya kuwa babu wannan a tattare da shi. Yadda ake gudanar da zance shi ne; saurayi zai iske budurwa har gida domin su gana da juna, muradin masoya shi ne su zauna a tare su yi firarsu ta farin ciki gami da annashuwa.
Eh ina zuwa zance sosai ma, yadda nake gudanar da shi kuwa hanyoyi ne masu dumbin yawa, wani ‘time’ din idan na je babu abin da muke yi sai zolayar juna, wani lokacin kuma labarin yadda auren mu zai kasance muke yi, wani lokacin kuma labarin duniya muke.
Shawara ga matasa akan zuwa zance ita ce, a matsayinka na matashi idan za ka je zance wajen masoyiyarka, kayi kwalliya, ka fesa dan turarenka kuma ka tsara duk abin da za ka fada ma ta wanda kasan zai yi tasiri a zuciyar ta, domin ita Mace soyayya na shigar tane ta kunnuwanta, ka kasance mai iya lafazi da kurara ta. Mace na son hakan sosai.
Ibrahim Danmulky daga Jihar Kano Karamar Hukumar Nassarawa, Unguwar Brigade Gama:
Alhamdulillah zuwa zance yana da matukar fa’ida sosai ga rayuwar masoya, soyayya ta gaskiya kuma tsarinsa yana tafiya ne da al’adun Hausa da kuma dokokin addinin musulunci ba kamar yadda wasu abubuwa suka bata tsarin ba yanzu. Da awai bambanci sosai ma ba kadan ba, tsarin ya canza zamani ma haka. Yadda ake gudanar da zance ba wani abu ne mai wahala ba, Saurayine zai je gidansu budurwar da yake so ya gana da ita domin tattaunawa tare da izinin iyayen budurwa. Gaskiya ni ban taba zuwa zance ba balle na fadi yadda nake yi sai dai ko nan gaba in sha Allah. Ni dai shawarar da zan bawa matasa masu zuwa zance ita ce su ji tsoron Allah, kuma su rike al’adarsu ta Hausa da kyau, su daina aro ko shigo da al’adun wasu cikin tsarin gudanar da zance awannan zamanin, yin haka ba karamar matsala yake haifarwa ba.
Lubabatu Auta Ingawa daga Jihar Katsina:
Ni a ra’ayina ma gaskiya gaba daya zance baya birge ni, musamman wanda za a yi ta zuwa kullum ko duk bayan kwana 2, irin wannan gaskiya gani nake kamar za a iya kosawa ko gajiyawa da juna, amma mafi birge wa da alfanu shi ne saurayi ya rinka ziyartar budurwa duk bayan sati 1 idan suna gari daya, duk bayan wata 1 idan suna gari mafi kusa, duk bayan wata 2 ko 3 har zuwa 4 idan an yi nisa da gari, hakan zai sa a rinka mararin juna da son ganin juna a marmarce, amma idan kullum ne ai an saba wata rana idan tayi kwalliya ta fito wata rana daga gona za ka wuce wurin ta fito kila ma daga ‘kitchen’ take ba wanka bare kwalliyar. Amma idan abin ya kasance cikin tsari to fa akwai tanadi na abin kyautata da za ta yi maka kuma kai ma za ka yi ma ta. Wannan shi ne ra’ayi na a takaice.
Binta Dalha daga Jihar Kano:
Zuwa zance yanada matukar amfani saboda anan za ku fuskanci juna, kowa ya san abin da dayansa yake so da abin da baya so kafin aure. Zance lokacin ‘da’ dana yanzu akwai bambanci sosai, zancen baya idan budurwa za ta fito daga gida akan hadota da yarinya tayi mata rakiya kuma yawanci za a ga da yamma zuwa magriba an gama zance, kuma sai ranar alhamis da juma’a sakamakon makarantar dare, shi kuwa zancen yanzu wasu a cikin mota suke yi ko kuma akai har 11 ana zance wata ma a dauketa a tafi yawo su je can su je can ba tare da iyayenta sun sani ba kuma babu dan rakiya. Ana gudanar da zance bisa al’ada, saurayi zai zo gidansu yarinya ya tura yaro ya ce ana sallama da wance ita kuma idan iyayenta sun ba ta dama sai ta fito. Eh! ana zuwa gurina zance kuma ina yinsa a shagon gidanmu da yamma. Ina ba da shawara akan zance aji tsoron Allah a tsarkake zuciya kuma ban da yaudara idan ka yaudari ‘yar wani kai ma watarana za ka haifi taka duk abin da kayi sai an yi ma ta.
Sunana Zahra’u Abubakar (Dr. Zara), Karamar hukumar Nassarawa Jihar Kano:
Amfanin zuwa zance ko hira wajen budurwa yana da tasiri sosai, Kuma hakan na da matukar amfani saboda anan ne za a fahimci juna fiye da ace a waya ake hirar ko kuma da makamancin hakan. Akwai bambanci sosai saboda zencen da ana tafiya tare da kanwa ko kani sabanin yanzu kuma da saurayi na gefe ita ma tana gefe, ban da yanzu da ake zama darduma daya ko benci da dai sauran su. Yadda ake gudanar da zance saurayi zai yi sallama gidan iyayen budurwar sai ya kira ta a waya ko kuma ya aika yara su kira ta to idan ta fito zatai musu shimfidar abun zama ko kuma ta kawo musu kujerun zama da dan abun sha haka ko ruwa ne idan da hali to daga nan za su gaisa sai kuma a fara tatauna abin da ya shafe su na game da soyyayar su. Ana zuwan mun zance, kuma yadda nake gudanar da zancen shi ne dama ranakun a tsare suke so in yazo zai kira ni ya ce ya karaso to daga nan zan shirya in dauki kujerun zama guda 2 in kai mana baranda wataran da dan ‘drinks’ wataran kuma babu to zamu gaisa sai kuma mu yi hirar data shafe mu da kuma yadda al’amura za su ci gaba da tafiya idan Allah ya cika mana burin mu. Shawarar da zan bawa matasa masu zuwa zance ita ce da a rike gaskiya da rukon amana in har ka san ba auren zaka yi ba to bai kamata ma ka fara zuwa zancen ba, kana bata ma ta lokaci ba, sannan kuma in an je hirar ta kasance wadda ta shafe ku ne ba wai ai ta dauko zancen wasu ba, sannan kuma ya kamata a kula da lokaci idan zancen na dare ne, sannan kuma a rinka saka sutura ta mutunci yayin gudanar da wannan zancen.
Engr. Isma’il Muhammad Garin Borno:
Yana kara shakuwa tsakanin saurayi da budurwa. A da budurwa ba ta fitowa zance wurin saurayi sai tare da yaro ko yarinya, ba kamar yanzu ba da aka barin saurayi da budurwa su kadai su kebe suna fira. Saurayi ne zai je kofar gidan su budurwa ya aika a kirawota ta fito kofar gida ko zaure ta shimfidawa saurayin tabarma ko darduma domin su kara samun fahimtar juna ta hanyar zantawa. Ina zuwa amma da yamma nake zuwa domin mu fahimci juna da yarinyar. Shawara ga matasa masu zuwa zance shi ne; duk saurayin da ya san ba da gaske yake son yarinya ba ka da ya soma ya je kofar gidan su yarinya zance ba.