Mahdi M Muhammad">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

Sam Nda-Isaiah (1962-2020):IBB, Abdulsalami, Etsu Nupe Za Su Albarkaci Jana’izarsa

by Mahdi M Muhammad
December 21, 2020
in LABARAI
2 min read
Ta’aziyar Rasuwar Sam Nda Isaiah
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
  • Laraba Mai Zuwa Za A Yi Jawabai Na Musamman
  • Lahadi A Gudanar Da Wakoki
  • Litini Taron Biznewa

A halin da ake ciki, iyalan Shugaban kamfanin Rukunin LEADERSHIP, Sam Nda-Isaiah, sun fitar da jadawalin yadda jana’izarsa za ta gudana, a inda suka bayyana cewa, tsofaffi shugabannin Nijeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida da Janar Abdulsalami Abubakar, za su albarkaci jana’izar marigayin, inda a ranar Laraba mai zuwa za a fara gudanar da ayyukan jana’izar, wacce ranar ce da za a gabatar da wani taro na musamman, don sauraron jawabai daga makusanta da ’yan uwan Marigayin.

A wata sanarwar da dan uwan marigayin, Mista Abraham Nda-Isaiah, ya fitar, ya bayyana manyan mutanen da ake sa ran za su halarci wannan babban taro, wanda zai fara daga karfe 12 na ranar Laraba mai zuwa, tare da nuna girmamawa ta musamman, ciki har da tsofaffin shugabannin kasa, kamar Janar Ibrahim Babangida da Janar Abdulsalami Abubakar.

samndaads

Sanarwar ta kara da bayyana cewa, ana kuma sa ran Babban Basaraken gargajiya na jihar Neja, Etsu Nupe, Dakta Yahaya Abubakar zai halarci taron. Nda-Isaiah ya rike sarautar Kakaki Nupe, wato mai magana da yawun al’ummar Nupe, tare da wasu mukamai na gargajiya da dama.

Haka zalika, akwai alamu masu karfi da ke nuna cewa a ranar Lahadin, fadar Shugaban kasa da ta gwamnatin Jihar Neja, (inda Marigayin ya fito), za su tura manyan wakilai zuwa wajen taron.

Abraham ya ci gaba da cewa, “za a gudanar da taron bizne Marigayin ne a ranar Litinin 28 ga Disamba, 2020, a makabartar Gudu da ke Abuja, da misalin karfe 10 na safe, wanda zai zama taro ne na wadanda aka gayyata kawai.”

Sam Nda-Isaiah, wanda ya kasance masanin harhada magunguna, dan kasuwa, mashuhuri a harkar yada labarai, kuma hazikin dan siyasa. Mutuwar sa ta girgiza mutane a duk fadin kasar nan da ma kasashen waje.

Wata sanarwar da ta fito daga iyalansa a yayin da su ke sanar da mutuwar tasa a ranar Juma’a, sun bayyana cewa, “Sam Nda-Isaiah mutum ne mai kula da gidansa, dan kasuwa ne mai hangen nesa, kuma mutum ne mai matukar sha’awar siyasa, kuma sama da komai, mutum ne mai imani.”

Duk da yake mutum ne wanda ya sami horo a fannin sarrafa magunguna, Sam yana fada da farin ciki cewa, ya dauki aikin jarida a matsayin sana’arsa, kuma ya samu nasarori tun bayan da ya kafa tsayayyar Kamfanin Jaridun LEADERSHIP, ‘National Economy’ da LEDERSHIP A YAU, wacce ta kasance jaridar Hausa ta farko mai fitowa kullum a duniya.

Ya kuma kasance wadanda suka kafa jam’iyyar ‘All Progressibes Congress’ APC, a inda ya yi takarar tikitin shugaban kasa a shekarar 2014.

Nda-Isaiah, mai shekaru 58 a duniya, ya rasu ne a ranar Juma’a 11 ga Disamba, bayan ya yi rashin lafiya na dan gajeren lokaci. Ya bar Mahaifiyarsa, matarsa, ’ya’ya da ‘yan uwa.

SendShareTweetShare
Previous Post

Sam Ndah-Isaiah: Tun Farkon Haduwa Da Shi Na San Mutumin Kirki Ne

Next Post

‘Okay’ Din Ciyaman, Sam Nda-Isaiah (2)

RelatedPosts

Gwamnan Bauchi Ya Amince Da Murabus Din Sakatarenshi

Gwamnan Bauchi Ya Amince Da Murabus Din Sakatarenshi

by Mahdi M Muhammad
2 hours ago
0

Daga Khalid Idris Doya, Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad...

Fitaccen Dan Jarida A Duniya, Larry King, Ya Rasu

Fitaccen Dan Jarida A Duniya, Larry King, Ya Rasu

by Mahdi M Muhammad
7 hours ago
0

Fitaccen mai watsa shirye-shiryen talabijin da rediyo, Larry King, wanda...

EFCC Ta Cafke ‘Yan Damfarar Intanet 11 A Osogbo

EFCC Ta Cafke ‘Yan Damfarar Intanet 11 A Osogbo

by Mahdi M Muhammad
9 hours ago
0

EFCC ta cafke wasu mutane 11 da ake zargi da...

Next Post
Shigo-shigo Ba Zurfi, Tinubu!

‘Okay’ Din Ciyaman, Sam Nda-Isaiah (2)

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version