Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home MANYAN LABARAI

Sam Nda-Isaiah 1962-2020: An Yi Alhinin Rashin Nda-Isaiah A Kano

by Muhammad
December 30, 2020
in MANYAN LABARAI
5 min read
Shugaba Sam
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
  • *NUJ, Sheikh Khalil, Getso, JIFATU, Sani Brothers Sun Nuna Sun Mika Ta’aziyyarsu

Daga Mustapha Ibrahim, 

Tun a daren 11 ga Disamba, 2020 da a ka wayi gari 12 ga Disamba, 2020 da shugaban rukunonin kamfanin Jaridun Leadership ya koma ga mahaliccinsa, mutane mahimmai da sauran alumma ke ta bayyana alhini da raayoyinsu kan rasuwar Shugaban LEADERSHIP, Mista Sam Nda-Isaiah, wanda duniya ba zaSam ta taba mantawa da shi ba dangane da irin gudunmawar da ya bayar a rayuwarsa ta shekara 58 a duniya ba, lamarin da ya sanya jiga-jigan mutane da bangarori a Jihar Kano su ka shiga jerin masu mika sakonnin ta’aziyyarsu.

samndaads

Shugaban Kungiyar ’Yan Jarida ta kasa Reshen Jihar Kano, Kwamred Abbas Ibrahim, bayan alhininsa da ya bayyana kan rashin shugaban rukunonin jaridun LEADERSHIP da iyalansa da ’yan uwansa da ma`aikatansa da jiharsa ta Neja da kasarsa da Afrika da ma duniya bakidaya, ya kuma ce, rayuwar Sam na cike da darussa mai tarin yawa da ya kamata a koya daga cikinta.NUJ

Ya ce, Mista Nda-Isaiah ba jarida ya karanta ba; harhada magunguna ya karanta, wato Pharmacy, amma sha’awa ta sa ya sadaukar da rayuwarsa wajen kokari da kuma kwarancewa a fannin jarida har ma ya fi wasu da su ka karanta jarida kwarewa a aikin.

Bugu da kari, ya ce, yadda Sam ya kafa jaridun LEADERSHIP, wannan wani abu ne mai mahimmancin gaske, domin ya zama kalubale ga ’yan jarida da su ka karanta jaridar kuma su ke aikin jarida, domin kafa rukunonin jaridun LEADERSHIP mai fitowa kullum ta Turanci (LEADERSHIP) da kuma mai fitowa kullum da Hausa, LEADERSHIP A YAU (wacce ita ce irinta ta farko a tarihi) da kuma NATIONAL ECONOMY, inda  jaridu 21 ke fitowa a mako guda, ya na mai cewa, wannan babban shafi ne da zai wuyar rufewa a tarihin aikin jarida na duniya, kuma wannan babban gudunmawa ce maras iyaka a aikin jarida.

Saboda haka yadda ya kafa ta, ya tsaya tsayin daka wajen tsayuwarta da tabbatar ta, to shi ma wani kalubale ne ga magadansa da ma`aikatansa da makusantansa. Don haka wajibi ne a dauki dukkanin matakai na ganin idan ba a fi shi bunkasa jaridun rukunonin LEADERSHIP ba, to ya zama dole a yi kamar shi. Ya ce, haka shi ne hakikanin nagarta, kishin kasa da kishin al’umma da Sam ya gudanar a rayuwarsa ta shekaru 58 a duniya.

Shi kuwa Shugaban Majalisar Malaman Arewacin Najeriya, Sheikh Ibrahim Khalil, taaziyyarsa ya isar ga iyalan Sam da maaikatansa da ma masu gidajen jaridu a ko’ina da ma daukacin ’yan jarida da al’ummar Najeriya, musamman shugabannin Najeriya, inda kuma ya yi jawabi ko sharhi a kan wannan rasuwa ta babban gwarzo kuma jarumi wanda ya bada gudunmawa wajen wayar da kan jama`a ta hanyar rubuce-rubuce da makamantansu a rayuwarsa wanda kuma ya nuna bai kamata Najeriya ta manta da irin wadannan mutane ba ta ko’ina.Sheikh Khalil

Shi kuwa Alhaji Halilu Ahmed Getso, fitaccen ma’aikacin rediyo nan, wanda ya yi aiki a Rediyon Tarayyar Najeriya Kaduna (FRCN) da wajen Najeriya, BBC, wanda ya taba fada a wata hira da ya yi da Wakilin LEADERSHIP HAUSA a gonarsa a 2016 cewa, shekararsa sama da 30 ya na aikin jarida, amma bai taba yin aikin jarida da wani harshe ba sai Hausa, ya ce, babu shakka duk wani Bahaushe da ke duniya ya ci gajiyar mawallafin jaridar LEADERSHIP a baya ko a yanzu ko a nan gaba, saboda kasancewarsa shi ne wanda ya fara kafa jaridar Hausa mai fitowa a kullum ta Allah, kuma shi ba Bahaushe ba, to ba shakka Sam ya yi aikin da Hausawan ma ba su yi ba kuma mu kanmu mun ci gajiyar rayuwar Sam da irin gudunmawar da ya bayar a rayuwarsa.Getso

“Addu’armu ita ce, Allah ya tabbatar da gudunmawarsa a doron kasa yadda za a cigaba da cin gajiyar abinda ya kafa,” a ta bakinsa cikin zantawarsa da wakilinmu a gidansa da ke garin Getso.

Shi ma Shugaban rukononin kamfanonin Kantin Jifatu na kasa, Alhaji Sabitu Yahaya Muhammad Jifatu, ya nuna matukar alhininsa kan rasuwar shugaban jaridun LEADERSHIP, ya na mai cewa, Najeriya na bukatar irin su Sam, wanda nagartarsu ta bayyana wajen kokarin hada kan alumma da kuma sama musu aikin yi ba tare da laakari da kabilar da ka fito ba, ko kuma addinin da ka ke bi ba matukar ka cancanta ko wani abu mai kama da haka kowa yasan cewa maaikatan jaridun LEADERSHIP sun fito ne daga kowanne bangare na kasar nan wanda suka sha bamban a harsunan su da addinin su amma shugaban Leadership ya zama kamar Gwamnati ta hanyar hada mabambanta kabilu da addini wuri daya, wannan abin koyi ne ga alummar Najeriya musamman shugabanni, Malamai, Masana da sauran al`umma na cewa kullum a fifita nagarta ba kabilanci ko Harshe ba, yin hakan zai sa Najeriya ta ci gaba matukar aka fifita Nagarta ba Harshe ko kabila ba.Jifatu

A nasa Bangaren, tsohon Shugaban Kungiyar Masu Motocin Sufuri na biyu a tarihin kungiyar a Najeriya, Dattijo Alhaji Sani Yunusa Sarina, wanda aka fi sani da Sani Brother, ya bayyana cewa, ya na alhini da jajenta wa iyalai da daukacin ma`aikata da masoyan shugaban rukunonin jaridar LEADERSHIP, Sam Nda-Isaiah, dangane da irin gagarumin rashin da aka yi na rashin sa a daidai lokacin da a ka fi bukatar sa, saboda kasancewar sa jajirtaccen marubuci, wanda ya na daya daga cikin wanda su ka taka rawa wajen tabbatar dimukradiyya da ake yi a Najeriya, musamman alkalamin sa na rubuce-rubuce wanda yayi wajen yakar yunkurin hawa mulki har sau uku da Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya yi yunkuri.Sani Brothers

Haka dai al’umma da dama ke jajantawa da alhini na rasuwar Sam a wannan lokaci, Alhaji Danjuma Minjibir, wani tsohon ma’aikacin Bankin Arewa ne (Bank of The North) ya ce, mawallafin jaridun LEADERSHIP rayuwarsa ta taimaki Arewa, ta fitar da Arewa kunya, musamman ta fuskar aikin jarida da sauransu.

“Don haka Arewa da Najeriya sun yi babban rashi. Mu na fatan magadansa ko wani daga Arewa ya cike wannan gurbi,” a cewar Danjuma Minjibir, ma`abocin karatun jaridun LEADERSHIP.

Abdullahi Haruna Yari Bori, wani masanin harshen Hausa da ya ya yi karatu a makarantar gaba da sakandire da ke Garin Azare ta Jihar Bauchi, ya ce, babu abinda ya burge shi da Sam ya yi kamar yadda ya nuna kishinshi da kirkiro jaridar Hausa tun ta na mako-mako har ta koma kullum.

“Mu na ganin mun yi rashin gwarzo, kuma garkuwar Harshen Hausa na hakika a Najeriya ko ma duniya bakidaya,” a cewar Abdullahi Bori, matashi mazaunin Kano kuma dan asalin Jihar Katsina.

Tuni dai a ka binne Marigayi Nda-Isaiah ranar Litinin da ta gabata daidai da tanadin addinin Kirista.

SendShareTweetShare
Previous Post

Da Dimi-Diminsa: Bam Ya Kashe ‘Yan Sintiri 7 A Borno

Next Post

Rundunar Sojin Sama Ta Yi Ruwan Bama-bamai A Dajin Sambisa

RelatedPosts

Bude Makarantu

Korona: Ba Ja Baya Ga Bude Makarantu – Gwamnatin Bauchi

by Muhammad
6 days ago
0

Daga Khalid Idris Doya, Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Bauchi ta...

Harshen Hausa

Taron ‘Waiwaye Adon Tafiya’: Masana Sun Damu Bisa Nakasta Harshen Hausa

by Muhammad
1 week ago
0

Akwai Damuwa Kan Yadda Zamani Ke Tafiya Da Al’adun Bahaushe...

'Yan Kwaya

Zaben Kananan Hukumomin Kano: Yadda Aka Tono ’Yan Kwaya A ’Yan Takara

by Muhammad
1 week ago
0

Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta...

Next Post
Rundunar Sojin Sama Ta Yi Ruwan Bama-bamai A Dajin Sambisa

Rundunar Sojin Sama Ta Yi Ruwan Bama-bamai A Dajin Sambisa

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version