Muhammad Auwal" />

Sama Da Limaman Juma’a 500 Suka Halarci Gangamin Wayar Da Kai Kan Zaman Lafiya Da Hadin Kai A Neja

An bayyana cewar gwamnatin Neja bisa jagorancin Alhaji Abubakar Sani Bello ta samar da walwalar gudanar da al’amurra a cikin jama’a da kuma tsaro a tsakanin al’ummar jihar, wanda yana daya daga cikin nasarorin da gwamnatin ta samar bancin biyan albashin ma’aikata kan kari wanda yana da cikin abubuwan da aka shaidi gwamnatin da su, shugaban kungiyar Limaman juma’a a jihar, Sheikh Isah Fari limamin babban masallacin juma’a na garin Minna ne ya bayyana a lokacin bude taron karawa juna sani kan gudunmawar Limamai dan tsaftar siyasa kasar da kungiyar ta shirya wa limaman na kwana biyu daga asabar zuwa lahadin makon nan da ya gabata.
Sheikh Isah Fari ya jawo hankalin limaman da cewar lallai suna da gudunmawar bayarwa dan ganin an gudanar tsaftataccen zabuka a babban zaben kasar nan mai zuwa, wajibi ne malamai da malamai su tashi tsaye wajen fadakar da kawunan mabiya muhimmancin zaman lafiya da zabin shugabanni na gari.
Tunda farko da yake jawabi, dan majalisar dokokin jiha, Hon. Muhammad Danlami Bako, wanda ya wakilci shugaban majalisar dokokin, Hon. Ahmed Marafa Guni, ya nemi malaman da su taimakawa gwamnati ta fuskar ilimi ta yadda za a rika yin wa’azozin da zasu hada kawunan jama’a bisa fahimta ta cigaba, da kyawawan kalamai masu anfani da su kawo cigaba da zaman lafiya mai dorewa a cikin jama’a.
Shugaban majalisar yace malamai iyayen al’umma ne domin su ne fitilar da za ta rika haska hanyar da ta dace a bi, don haka a halin da kasar nan ke ciki akwai bukatar limamai su zage damtse a masallatai da wajajen wa’azi musamman dan fadakarwa kan zaman lafiya da kira ga iyaye kan kula da tarbiyar matasa masu tasowa akan illar shaye-shaye da bangar siyasa, mu a gwamnatance malamai na da muhimmanci kuma muna ganin suna ne kan gaba wajen tarbiyatar da al’umma ta fuskar addini.
Gwamnan jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello da ya samu wakilcin mataimakin sa, Hon. Ahmed Muhammed Ketso, ya yaba da majalisar malamai da ta samar da wannan kungiyar da hada kawunan limamai da hadin guiwar hukumar kula da harkokin addinai ta yadda za a hada limamai waje daya dan tattauna matsalolin da ke taso wa da kuma hanyoyin da za a magance su a addinan ce.
Gwamnan yace taken bitar taron na bana “ Hanyar da za a samar da zaman lafiya, hadin kai, cigaban kasa dan samar da ingantacciyar gwamnati” ya zo daidai da inda ake fuskanta a yanzu na zaben 2019, ina kyautata zaton wannan taron zan baiwa limamai da malaman mu damar sahihiyar hanyar fadakar da mutanen anfanin zaman lafiya da yin zabe na gari. Dan haka ya kamata ku fadakar da alfanun zaman lafiya, domin duk hakki ne da ya rataya a wuyar mu wanda sai mun yi bayani a gaban mahalicci.
Da ‘yan siyasa da malaman addini ya kamata mu ji tsoron Allah, mu hada hannu wajen samar da gwamnati mai amana da za ta iya kare rayuka da jinainan mutane, domin in ba zaman lafiya ba yadda al’umma za ta iya cin ribar mulkin dimukuradiyya.
Kowani malamin addini ko limami ya tabbatar yana tafiya akan hikimar karantarwa ban zagi ko sukar wani wanda a karshen hakan kan janyo rarrabuwan kawunan al’umma, dole kowani malami ya zama yana cancantar koyarwa ta ilimin shiri’ar addini. Dan a wannan taron na kwana biyu a tabo batutuwan da zasu anfanar kuma wadanda suka da ce da yanayin da muke ciki.
Da yake karin haske ga manema labarai, sakataren kungiyar limaman juma’a kuma babban daraktan hukumar kula da harkokin addinai ta jihar Neja, Dakta Umar Faruk Abdullahi, yace ba a taba samun gwamnati da ta karfafa malamai a cikin ta ba a jihar nan ba, kamar wannan gwamnatin ta Alhaji Abubakar Sani Bello ba, domin muhimmantar da limamai aka damka alhakin kula da harkokin addinai a hannu limaman addini.
Sheikh Abdallahi yace aikin wannan hukumar ya shafi kusan dukkanin bangarorin addini da gwamnati ta amince da su da suka shafi addinin musulunci da na kiristanci. Dan haka duk wani aikin da gwamnatin Neja ta yiwa musulmi a lokuttan azumi da sallah kamar ciyarwa lokacin watan Ramadan da na sallah, haka ake yinsa a karkashin wannan hukumar ga mabiya addinin kirista a lokuttan bukukuwan kiristami, da ziyarce-ziyarcen wuraren Ibadah na aikin Umrah, Hajji da ziyarar kasar Isra’ila, don haka ba a bar kowa a baya ba.
A karshe dai ranar lahadin nan dai kungiyar ta karrama gwamnan jihar, Alhaji Abubakar Sani Bello kan jajircewa wajen ganin an samar da tsaro da kuma janyo limamai a jiki dan sanin muhimmancinsu a gwamnatance.
Kungiyar ta sha alwashin tashi tsaye haikan wajen fadakar da kan jama’a muhimmancin mallakar katin zabe da kuma zabin shugabanni na gari da muhimmancin zaman lafiya da alheran da yake kawo wa a kasa.

Exit mobile version