Hukumar Ilimin bai daya ta jihar Kaduna, KADSUBEB, ta raba Naira Dubu 183,000 ga makarantu 2,121, domin gudanar da kananan gyare-gyare, daga cikin Naira miliyan 400 da hukumar ilmin bai daya ta UBEC ta baiwa gwamnatin jihar.
Da yake jawabi a wajen bikin, inda aka raba kudaden ga makarantun da su ka amfana, Shugaban Hukumar KADSUBEB, Malam Tijjani Abdullahi, ya ce shirin ya samar da kudaden ne Daga asusun shirin samar da ingantaccen ilimi ga kowa da kowa (BESDA).
Shugaban hukumar wanda ya shawarci kwamitocin kula da makarantu (SBMCs) da su yi amfani da kudaden ta yarda ya dace, ya bayyana cewa ma’aikatar ilimi ta tarayya da UBEC ne suka zabi makarantun da suka amfana bayan gudanar da bincike a shekarar 2021.