‘Sama Da ‘Yan Nijeriya Miliyan 60 Ba Su Iya Rubutu Da Karatu Ba’

Hukumar kula da ilimantar da ‘yan kasa a Nijeriya ta ce fiye da ’yan Nijeriya miliyan 60 ne ba sa iya rubutu da karatu cikin kowane yare.

Babban sakataren wannan hukumar, Farfesa Abba Abubakar Haladu wanda ya bayyana haka a wani taro a birnin tarayyar kasar Abuja, ya ce kasar na fuskantar kalubalen da ta kai ga dimbim manya da matasa ba sa iya hada harrufa su bada ma’ana.

Ya ce wannan ne ma ummul’aba’san rashin ci gaba a kasar, duba da yawan manya da matasa da wannan al’amari ya shafa.

Ya ce idan har ana bukatar kasar ta bunkasa a fannoni da dama, dole ne dukkan mutanen kasar su iya rubutu da karatu da kuma lissafi a ko ina suke, kuma ko mene ne jinsin su.

Ministan ilimi na kasar, Malam Adamu Adamu ya ce wajibi ne a dauki matakan gaggawa don kawo sauyi ganin yadda yawan yaran dake barin makaranta ke karuwa.

Exit mobile version